Real ta yi amfani da dama a kan Atletico a Champions League
Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta yi nasara a kan Atletico Madrid da cin 2-1 a wasan farko zaggayen ƴan 16 a Champions League ranar Talata.
Real ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Rodrygo minti huɗu da fara wasan daga baya Julian Alvarez ya farke tun kan hutu.
Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne Real ta kara na biyu ta hannun Brahim Díaz.
Wannan shi ne karo na uku da suka kece raini tsakanin Real da Atletico a bana, bayan wasa biyu a gasar La Liga.
Champions League Talata 4 ga watan Maris ɗin 2025
- Real Madrid 2 - 1 Atletico Madrid
Spanish Liga ranar Asabar 8 ga watan Fabariarun 2025
- Real Madrid 1 - 1 Atletico Madrid
Spanish Primera Liga ranar Lahadi 29 ga watan Satumbar 2024
- Atletico Madrid 1 - 1 Real Madrid
Wannan shi ne karo na takwas da suka fafata a gasar zakarun Turai, inda Real ta yi nasara ta huɗu da canjaras biyu, Atletico ta ci karawa biyu.
Jude Bellingham bai buga wa Real wasan ba, sakamakon katin gargaɗi na uku da ya karɓa a wasa da Manchester City.
Yanzu ɗan wasan tawagar Ingila zai buga zagaye na biyu ranar Laraba 12 ga watan Maris a gidan Atletico.
Kafin nan Real za ta kara da Real Vallecano a gasar La Liga ranar Lahadi.
Atletico ce ta biyu a teburin La Liga da maki 56 da tazarar maki ɗaya tsakani da Barcelona mai jan ragama kawo yanzu.
Real Madrid ta yi ƙasa zuwa mataki na uku a teburin La Liga da maki 54, bayan cin karawa 16 da canjaras shida aka doke ta wasa huɗu, bayan wasannin mako na 26.
Babban Labari
Labarai na musamman
Labaran da suka fi shahara
Babu karin bayanai