Waiwaye: Kasafin 2025 da biyan kuɗin fansa tiriliyan biyu a Najeriya
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi na naira tiriliyan 47.9

Asalin hoton, @FMINONigeria
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar na 2025 ga majalisun dokokin ƙasar.
Kasafin dai wanda ya kai yawan naira tiriliyan 47.9, shi ne irinsa na biyu da shugaban ke yi tun kama aikinsa a shekarar 2023.
Tinubu ya bayyana kasafin kuɗin da kasafin da aka yi domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar.
"Batun raya ƙasa da samar da kayan more rayuwa su ne ƙashin bayan wannan kasafin na shekarar 2025." In ji Tinubu.
A ranar Litinin ne dai majalisar zartarwar kasar ta zartar da kasafin kuɗin na 2025.
Majalisun guda biyu wato na dattawa da wakilai dai za su yi duba na tsanaki domin yin gyara ga kasafin kafin ya zamo doka.
Zargin da Nijar ta yi wa Najeriya

A wannan makon ne Nijar ta zargi Najeriya da cewa tana haɗa kai da wasu manyan ƙasashen duniya da jami'an tsohuwar gwamnatin Bazoum da ke zaman mafaka a Najerya domin kitsa yadda za a jefa ƙasar cikin hargitsi.
Wannan zargi na zuwa ne duk da wani taro da aka yi watannin baya tsakanin hafsoshin sojan Nijar da na Najeriya, inda Najeriya ta bayar da tabbacin ba za ta yarda a cuci makwabciyarta.
Yayin wata hira da sashen Hausa na BBC a watannin baya, Firaministan Nijar din Lamine Zain, ya yi zargin cewa mahukuntan Najeriya da jami'an tsohuwar gwamnatin na tsara yadda za a cutar da kasar daga Abuja, zargin da Najeriyar ta musanta.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai ta ɓalɓalce ne tun bayan da sojoji suka karɓe ragamar mulki a Nijar suka kuma fice daga Ecowas.
Mutuwar yara 35 a Oyo

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rundunar ƴansanda jihar Oyo ta ce an samu gawar ƙananan yara 35 sannan guda shida suna cikin mawuyacin hali a asibitoci daban-daban.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis, rundunar ta ce ta kuma kama mutum takwas masu alaƙa da shirya taron da ya janyo turmutsutsun ranar Laraba, ciki har da tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Agunwusi.
Tun bayan mummunan turmutsutsu da aka samu a wata makarantar Islamiyya a birnin na Badun ake ta nuna yatsa ga tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Silekunola Ogunwusi da mai gidan rediyon Agidigbo FM, Oriyomi Hamzat waɗanda su ne ake yi wa kallon haddasa al'amarin.
Tsohuwar mai ɗaƙin Sarki Ooni na Ife, Naomi Silekunola Ogunwusi ce dai ke shirya wannan bikin na al'ada a duk shekara inda jama'a musamman yara ke haɗuwa lokacin hutu su yi wasanni da yi wa ubangiji godiya ta an shekara lafiya.
Bayanai sun nuna cewa wani gidan rediyo mai suna Agidigbo FM ne ya taka babbar rawa wajen tallata taron Misis Naomi na shekara-shekarar.
Rahotanni sun ce har lokacin da ake cikin turmutsutsun a wurin taron, gidan rediyon bai daina watsa shirye-shirye a kan taron ba wani abu da ake ganin ya ƙara sanya jama'a yin tururuwa zuwa wajen.
An biya kuɗin fansa sama da tiriliyan biyu - NBS
Wani rahoto da hukumar tattara alƙaluman Najeriya, NBS ta fitar ranar Litinin ya nuna irin girman matsalar tsaro a Najeriya musamman abin da ya shafi garkuwa da mutane.
Rahoton mai taken Laifukan da aka fuskanta da kuma jin ra'ayin mutanen kan sha'anin tsaro na 2024, ya ce tsakanin watan Mayun 2023 da Afrilun 2024, an kashe ƴan Najeriya 614,937 sannan an yi garkuwa da mutum miliyan 2,235,954.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an biya masu garkuwa da mutane kuɗin fansar da suka kai yawan naira tiriliyan 2.2, kuma hakan na nufin akan biyu naira miliyan 2.7 ga kowane mutum.
Cecekuce kan sansanin sojin Faransa a Najeriya

Asalin hoton, @DefenceInfoNG
Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce babu gaskiya a labaran da ake yaɗawa cewa dakarun Faransa na shirin kafa sansaninsu a Najeriya.
Wata sanarwar da daraktan yaɗa labaran Hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar a yau Litinin ta ce labaran jita-jita ce, kuma basu da tushe.
Ya ce, "An ankarar da hedikwatar tsaron Najeriya a kan rahotannin da ake yaɗawa a shafuka sada zumunta da ke zargin cewa zangon farko na dakarun Faransa ya isoa Maiduguri a shirye-shirye kafa sansanin su a yanki Arewa maso gabashin Najeriya.
"Rundunar sojin Najeriya na tabbatar da cewa wannan rahoto na ƙarya ne kuma bashi da makama. Idan za a iya tunawa babban hafsan Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi bayani game da wannan batu, kuma ya jaddada cewa jita-jita ne kawai aka kitsa a wannan labari.''
Hedikwatar tsaron ta buƙaci jama'a su yi watsi da rahotannin ƙaryar, waɗanda ta ce har yanzu akwai masu ci gaba da yaɗa su domin cimma muradun su na son rai.
Ademola Lookman ya zama gwarzon Afrika

Asalin hoton, @PBATMediaCentre
Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na tawagar Super Eagles ta Najeriya da ƙungiyar Atalanta ta Italiya, Ademola Lookman ya lashe kyautar ɗan ƙwallon ƙafa na Afirka.
Ɗan wasan ya doke fitattun zaratan ƴan wasa irin Achraf Hakimi na Morocco da Simon Adingra na tawagar Ivory Coast da ƙungiyar Brighton & Hove Albion ta Ingila da Ruto Williams na Afirka ta Kudu da Serhou Guirassy na ƙasar Guinea da ƙungiyar Dortmund ta Jamus domin lashe kyautar.
An gudanar da bikin karrama gwarazan ƴanwasan na Afrika ne a a birnin Marrakech na ƙasar Morocco
Lashe kyautar a wannan karon ya sa ƴan wasan Najeriya biyu sun lashe kyautar sau biyu a jere bayan Victor Osimhen da ya lashe kyautar a bara.











