Mutanen da jikinsu ya tsani mu'amala da sauran mutane

Hoton wata mace

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Christine Ro
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • Lokacin karatu: Minti 4

Maura ta yi imanin cewa kwaroron roba ne ya tseratar da rayuwarta.

'Yar shekara 43 a yanzu da ke zaune a jihar Ohio ta Amurka, Maura ta ce ta fara fuskantar matsalar ne tun tana shekara 20 da wani abu.

"Na lura gabana na zafi duk lokacin da na yi jima'i ba tare da kariya ba," a cewarta.

Maura da muka ɓoye sunanta, ta ce ta ji fargabar faɗa wa abokin zamanta. Saboda haka, sai ta jira ya fita kafin ta wanke jikinta da kyau.

Ta sauya abin da take wanka da shi daga dunƙulen sabulu zuwa na ruwa. Amma mastalar sai ma ƙaruwa ta yi, inda wurin ya kumbura kuma ya yi ja, kuma hakan ya faru ne bayan maniyyi ya taɓa ta a karon farko.

Daga baya ta rabu da shi kuma ta fara hulɗa da wani wanda ba shi ƙyamatar amfani da kwaroron roba na kariya.

"Babu wata matsala, har sai wata rana da muna kwance bayan mun yi jima'i, kawai sai harshena ya fara kumbura," kamar yadda ta bayar da labari. "Nan take ya lura da abin da yake faruwa, ya saka kuruwa, kuma ya jawo min na'urata ta nimfashi, ya kafa min a ba ki har sai da na fara shaƙarta.

Maura tana da matsalar nimfashi ta asthma da kuma wasu abubuwa da jikinta ba ya so. Ta ce tana tunanin kwaroron ne ya ɓule. kafin abin ya faru da ita, ba ta taɓa tunanin abu ne mai yiwuwa ba a ce jikin wani mutum ba ya son mu'amala da maniyyi.

Duk da cewa babu su da yawa, akwai mutanen da ke fama da matsananciyar ƙiyayya ta yin mu'amala da jikin sauran mutane.

Amma har yanzu ba a san abin da ke faruwa ba da kuma abin da ke haddasa matsalar.

Daga fata

Akasari ƙin son mu'amala da jikin wani na faruwa ne saboda abin da ake shafawa ko kuma yake taɓa fatar mutum.

ba kodayaushe ne ake iya gane abin da ke haddasa ƙan-jiki ba (wani abu da jikin mutum ba ya so). Wata mace 'yar Amurka da ke da larurar da ke hana ƙwayoyin halittar garkuwar jiinta yin aiki, ta kamu da larurar allergy ta yadda jikinta ya daina son turaren mijinta.

Wata a asibitin Jami'ar Kepler da ke Austria mai suna Sabine Altrichter, ta ce duk da cewa babu hujja amma masu larurar kan ce jikinsu yana ƙyamatar warin jikin mutum ne ko kuma sinadaran da ke fita daga fatar jikinsu.

Fatar jikin mutum kan fitar da sinadarai da ke haddasa wari. Daga cikinsu akwai toluene wanda ake samu saboda amfani da man fetur wajen haɗa mayuka. Akan same shi a taba sigari, mutane kan shaƙe shi a wurin aiki ba tare da sun sani ba.

Fatar mutm kan fitar sinadarai a kowane lokaci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fatar mutm kan fitar sinadarai a kowane lokaci

Yanayin ƙyamar jiki na People Allergic To Me (PATM) ɗaya ne daga cikin larurori da ke haifar da wa wasu mutane su ji ba su son jikin sauran mutane, ta yadda za su dinga tari ko ƙwarewa a gaban mutanen.

A 2023, Farfesa Yoshika Sekine a fannin harhaɗa sinadarai na jami'ar Tokai ta Japan, sun yi bincike kan sinadaran da fatar mutum ke fitarwa da mutane ke cewa ba su so. Daga cikin sinadarai 75 da suka bincika, an gano akwai yiwuwar akwai mahaɗin toluene

Mutanen da ke fama da PATM kan fitar da sinadarai ninki 39 na wannan mahadin fiye da waɗanda ba su da matsalar.

Abubuwan da jiki ke fitarwa

Matsalar kan faru kuma saboda abubuwan da ke fita daga jikin mutum.

Wata mace a Birtaniya ta shiga matsalar nimfashi bayan yin jima'i da wani mutum da ya ci gyaɗar Brazil 'yan awanni kafin haka duk da cewa ya wanke bakinsa tsaf.

Saboda haka yawun baki kan haddasa matsalar saboda sumbata idan mutum ya ci wani nau'i na 'ya'yan itaciya, kayan miya, naman ruwa, ko ma madara.

Su ma nau'in abincin da mutum ya ci kan haddasa matsalar idan masu larurar suka haɗu da wani ruwan da ke fita daga jiin mutum. Ɗaya daga cikin abin da ƙwararru ke magana a kai shi ne maniyyi.

Sumbata kan jawo matsalar ƙyamar jiki saboda yawun da ke gaurayuwa da juna

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sumbata kan jawo matsalar ƙyamar jiki saboda yawun da ke gaurayuwa da juna

Akasarin matasa masu shekara 20 zuwa 30 ne suka fi fuskantar larurar ƙin mu'amala da maniyyi, amma ƙasa da mutumu 100 akas sani baki ɗaya na mutanen da ke da matsalar, in ji wani bincike a 2024.

Maganin matsalar

Ɗaya daga cikin hanyoyin magani da aka gwada shi ne saka wa mai larurar maniyyin mutumin da ba shi son alaƙa da shi a kan fatarsa domin rage ƙiyayyar.

Sai dai wannan na da tsada sosai. Masu larura kan kashe kuɗi sosai saboda irin wuya da ake sha wajen yin gwaje-gwaje kafin shirya samfuran da za a yi amfani da su.

Rashin son mu'amala da wani mutum kan haifar wa mutum damuwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rashin son mu'amala da wani mutum kan haifar wa mutum damuwa