Mece ce aƙidar ƙungiyar mayaƙan Mahmuda, wadda ake zargi da hannu a harin Kwara?

Asalin hoton, Getty Images
A ƙauyukan Woro da Nuku da ke ƙaramar hukumar Kaiama har yanzu lamurra ba su koma daidai ba, yayin da al'umma ke cikin kaduwa game da kashe-kashen da aka yi a ranar Talata.
Da almurun ranar Talatar al'ummun ƙauyukan suka gamu da fushin wasu mayaƙa, wadanda suka isa ƙauyukan suka kashe mutane da ƙona wasu ƙurmus.
Alƙaluma na baya-baya da aka samu sun nuna cewa an binne kimanin mutum 78 a yammacin ranar Laraba.
Baya ga haka nan ɗan majalisar jihar Kwara daga yankin Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa maharan ''sun wuce da mata 38,'' daga ƙauyukan da suka kai wa hari.
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce "masu tsattsauran ra'ayin addini ne suka kai harin, ba 'yan bindiga ba".
Bayani daga cibiyar Acled mai nazari kan tsaro ya nuna cewa yankin arewacin Najeriya da ma Sahle na zama wata cibiya ta ayyukan masu iirarin jihadi.
Alaluma kan ayyukan ta'addanci a fadin duniya Global Terrorism Index (GTI) a shekarar 2025 sun nuna cewa Afirka ta zama "cibiyar ta'addanci ta duniya", inda a karon farko "sama da rabi na kashe-kashe masu alaƙa da ta'addanci a duniya ke faruwa a yankin".
A Najeriya tun daga shekarar 2009 ne ƙasar ke fama da matsalar ayyukan ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Boko Haram.
Sai dai daga bisani ƙungiyar ta ɓalle zuwa gida biyu, tare da haifar da wasu ƙungiyoyin waɗanda suka ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula a yankunan ƙasar.
Masana tsaro sun bayyana cewa akwai ƙungiyoyin ƴan bindiga da dama da ke gudanar da ayyukansu a dazukan arewa maso yammacin Najeriya, inda abin ya fi ƙamari a jihohin Neja da Kebbi da Zamfara da Sokoto da kuma Kaduna, sai dai abin ya fara ta'azzara a jihohin Kwara ko Kogi a baya-bayan nan.
Sai dai daga baya irin waɗannan mayaƙa sun ƙara gangarawa zuwa jihohi kamar Kwara da Kogi.
Duk da cewa babu ƙungiyar da ta fito ta ɗauki alhakin harin na ƙauyen Woro, amma an fi alaƙanta shi da ƙungiyoyi masu alaƙa da ƙungiyoyin IS da kuma Alqaeda, kamar ƙungiyar Mahmuda.
BBC ta duba ƙungiyar Mahmuda, wadda ta yi ƙaurin suna a yankin.
Ƙungiyar Mamudawa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An yi amannar cewa Mahmuda ƙungiya ce da ta ɓalle daga Boko Haram, inda ta kafa sansani a kusa da tafkin Kainji da ke yammacin ƙasar a wuraren shekarar 2020.
Ana kallon wa'azin ƙungiyar a matsayin wanda bai kai na ƙungiyar Boko Haram tsauri ba, kuma mambobinta na amfani ne a mafi yawan lokuta da harshen Hausa wajen wa'azi tare da ɗaukin sabbin mabiya.
Ƙungiyar ta ƙaddamar da wasu kashe-kashe, inda takan zaɓi wanda take son ta kashe. Mayaƙanta kan yi amfani da babura wajen kai hari a kasuwanni da kuma gungun ƴan sa-kai masu ƙoƙarin kare ƙauyuka a jihar Kwara.
A watan Afrilu ƙungiyar ta kashe ƴan bijilanti da dama, da kuma kashe makiyaya a wani hari da suka kai a kasuwa.
A baya-bayan nan ƙungiyar ta fi mayar da hankali wajen gudanar da ayyukanta a arewacin jihar Kwara, sai kuma jihohin Neja da Kebbi.
Masani kan harkar tsaro a Sahel, Kabiru Adamu ya ce ƙungiyar a baya tana da alaƙa da ƙungiyar Ansaru.
"A tsakankanin 2012 ne ƙungiyar ta fito. Asali suna da alaƙa ne da Ansaru, ita kuma Ansaru a lokacin tana da alaƙa da ƙungiyar alQaeda."
Ya ce shugabanta na farko shi ne Mahmuda, wanda shi ne Mahmud Alnijeriy.
Ya ƙara da cewa "babu tabbacin ko wane ne shi, ko daga ina ya fito. Amma dai ya je Libya ya samu horo kan sarrafa makamai da haɗa bama-bamai a tsakanin 2013 zuwa 2015 kafin ya koma Najeriya."
Kabiru Adamu ya ce bayan Mahmuda ya koma Najeriya ya shiga gandun dajin Kainji da ke tsakanin Kwara da Neja da Kebbi ya kafa sansaninsa ya ci gaba da wa'azi da kai hare-hare.
Ƙarfin ƙungiyar Mamuda

Asalin hoton, Getty Images/Emmanuel Arewa
Kabiru Adamu ya ce babu tabbacin yanayi makamai da yawan ƴan ƙungiyar.
"Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta kama shi shugaban ƙungiyar wato Mamuda a watan 8 na shekarar 2025, sai ƙungiyar ta watse. Ba a sake jin ɗuriyaru ba, sai jefi-jefi," in ji shi.
Sai dai ya ƙara da cewa sun kasance suna zuwa wa'azi tsakankin mutum 100 zuwa sama, "musamman a tsakanin jihohin guda uku." in ji shi.
Manyan hare-haren da suka kai
Daga cikin manyan hare-haren da ƴan ƙungiyar suka kai, kamar yadda masanin tsaron ya bayyana, shi ne a ranar 16 ga watan Afrilun 2025, inda mayaƙan ƙungiyar ne suka kai wani hari a wani gari da ake kira Kemaji a jihar Kwara, inda suka kashe ƴan-sa-kai 15.
"Sannan a watan sun ƙara kai wani a kasuwar garin Kaiama, inda suka kashe mutane da dama, sannan a watan Yulin ta koma Kemaji ta kashe mutum 7 ta ƙona gidaje," in ji shi.
Kabiru Adamu ya ce yawancin hare-haren da suka kai wa, suna aikawa da wasiƙun cewa za su je, kafin su shiga.
"Wani bayani mai muhimmanci shi ne yadda take ɗaukar sabbin mayaƙa. Tana amfani amfani dabaru wajen jan matasa ciki har da kuɗi da aura musu mata da wa'azi."
Ya ƙara da cewa ƴan ƙungiyar suna kafa iko da karɓar zakka da sharia' da kuma amfani da ƙarfi wajen saka mutane su musu noma, sannan suna tilast bayar da sadaka da zakka.
"Kuma suna wa'azin bijire wa gwamnati da kuma tilasta amfani da dokokin shari'ar musulunci."
Kama Mamuda

Asalin hoton, ONSA
A watan Agustan shekarar 2025 ne gwamnatin Najeriya ta ce jami'an tsaronta sun samu nasarar kama wasu gawurtattun ƴanbindiga, ƴan tsagin ƙungiyar Ansaru da take zargi da kitsa fasa gidan yarin kuje a shekarar 2022, har wasu fursunoni suka tsare.
Mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya gudana a ofishinsa da ke Abuja a ranar Asabar, inda ya ce ƴanbindigan biyu na cikin waɗanda suke nema ruwa a jallo.
"A yau ina farin ciki sanar da ku cewa mun samu gagaruwamr nasara a yaƙin da muke yi da ta'addanci ta hanyar amfani da bayanan sirri, inda muka kama manyan jagororin ƙungiyar Ansaru masu alaƙa da Al-Qaeda a Najeriya."
Sanarwar ta ƙara da cewa sun samu nasarar ce a wasu samame da suka yi a tsakanin watan Mayu da Yulin bana, inda ya ce "muka kama manyan jagororin ƙungiyar Ansaru waɗanda suka kitsa kai wasu manyan hare-hare a Najeriya a shekarun baya."
Waɗanda aka kama ɗin kamar yadda ya bayyana su ne "Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Bara'a ko Abbas ko Mukhtar, wanda shi ne Amir, da kuma Mahmud al-Nigeri wanda aka fi sani da Mallam Mamuda, wanda shi ne shugaban ma'aikatan Abu Bara'a kuma mataimakinsa."
Ribadu ya ce Mamuda ya samu horo ne a ƙasar Libya a tsakanin 2013 zuwa 2015 a ƙarƙashin wasu ƴanbindiga daga ƙasashen Masar da Tunisia da Aljeriya da suka ƙware wajen amfani makamai da nakiyoyi.
Daga cikin manyan hare-haren da suka kitsa, kamar yadda Nuhu Ribadu ya bayyana akwai harin gidan yarin Kuje da aka yi a shekarar 2022 da hari a wajen haƙar ma'adinin uranium na Nijar da garkuwa da wani Bafaranshe mai suna Francis Collomp a Katsina da sace Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba a shekarar 2019 da sace Sarkin Wawa.
A lokacin har gwamnatin Amurka sai da ta yaba wa Najeriya da kama Mamudan.











