Sabon bincike ya fito da sabbin bayanai kan wurin da korona ta samo asali

Asalin hoton, Reuters
Masana kimiyya sun ce akwai hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa wata kasuwar sayar da naman dabbobin ruwa da na dawa da ke birnin Wuhan na China ce ta haddasa ɓarkewar cutar korona, ba kamar yadda a baya aka yi ta yamaɗiɗi kan cewa cutar ta fito daga wani ɗakin gwaji.
Bincike iri biyu da aka gudanar, duka sun sake bitar bayanan da aka tattara tun daga ɓarkewar annobar korona.
Wasu alƙaluman da aka tattara sun nuna cewa rukunin farko na mutanen da aka kai asibiti adreshin gidajensu ya nuna ba su da tazara sosai daga kasuwar ta sayar da naman dabbobin ruwa da na dawa.
Dakta Michael Worobey, wanda malami ne a Jami'ar Arizona, na daga cikin waɗanda suka jagoranci wannan bincike. "Mun ga alama kan cewa duka mutanen suna kusa-kusa da kasuwar Huanan kamar yadda ƙididdiga ta nuna a taswirance.
A bayyane take kan cewa duka waɗanda suka kamu da cutar a wuri guda suke, sa'annan suka warwatsu cikin al'ummomi tun da farko."
Wani bincike na biyu da aka gudanar kan cutar ya nuna cewa ba lallai ne a ce cutar ta soma yaɗuwa tsakanin bil adama ba kafin Nuwambar 2019.
Binciken ya ce muhawarar da ake yi kan cewa cutar ta sulalo ne daga wani ɗakin gwaji duk soki burutsu ne don kawar da hankalin jama'a.
Haka kuma binciken ya ce akwai yiwuwar an yaɗa farfagandar farko ne domin ƙoƙarin daƙile haɗin kan masana kimiyya na ƙasar China wajen duƙufa don su gano asalin wurin da cutar ta fara ɓulla.











