Jam'iyyar Republican ta sake kwace iko da Majalisar Wakilan Amurka

Ginin Majalisar Dokokin Amurka

Asalin hoton, ZACH GIBSON

Bayanan hoto, 'Yan Republican sun samu nasara da dan karamin rinjaye ne

Jam’iyyar Republican ta samu kujeru 218 da ake bukata ta samu rinjayen jagorantar majalisar wakilan Amurka, kamar yadda kafar yada labarai ta kasar mai alaka da BBC, CBS ta nuna.

 

Duk da cewa rinjayen da jam’iyyar ta samu a majalisar dan kadan ne, to amma ya isa ta rika taka birki ga manufofi da tsare-tsaren Shugaban kasar Joe Biden na jam’iyyar Democrat a ragowar shekara biyu ta wannan wa’adin mulkin nasa na farko.

 

Sakamakon ya sake dawo da gwamnatin da kanta ya rabu, inda har yanzu jam’iyyar Democrat ke rike da Majalisar Dattawa.

 

Tsohon shugaban kasar Donald Trump tuni ya sanar da aniyarsa ta sake neman takarar shugabancin kasar.

 

An samu rabuwar iko da gwamnatin ne a sakamakon zaben rabin wa’adi da aka yi a makon da ya gabata, inda ‘yan jam’iyyar Republican da suka sa ran sake karbe iko da majalisun dokokin kasar biyu, suka kasa taka rawar da aka yi tsammani a zaben.

 

Kafar yada labaran ta CBS ta yi hasashen cewa yanzu jam’iyyar ta Republican za ta ci tsakanin kujeru 218-223 a majalisar wakilan mai kujeru 435.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An dora alhakin rashin tabuka abin da aka yi tsammani ga jam’iyyar yawanci a kan jagororin jam’iyyar biyu : Donald Trump da shugaban marassa rinjaye na majalisar dattawa Mitch McConnell.

 

A ranar Talata tsohon shugaban ya sanar da aniyarsa ta sake neman kujerar shugabancin kasar a 2024 a gidansa na shakatawa da ke Mar-a-Lago a Florida.

 

A lokacin kaddamarwar ya ce, ‘’har yanzu masu zabe ba su fahimci irin tsananin wahalar da kasarmu ke ciki ba,’’ amma ya ce za su sauya shawara nan da shekara biyu kamar yadda ya yi hasashen cewa abubuwa za su kara tabarbarewa.

 

A ranar Laraba ne kuma a Washington aka sake zaben Mr McConnell a matsayin shugaban marassa rinjaye na Majalisar Dattawa, wanda hakan ya kawo karshen kalubalen mukamin daga Rick Scott shi ma dan Republican daga Florida.

 

Wannan ne karon farko da aka kalubalanci jagorancinsa na tsawon lokaci a shekara 15, yayin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida a kan wanda za a zarga da laifin gazawar jam’iyyar wajen sake samun rinjaye a Majalisar Dattawan.

 

Mutanen biyu sun rika gwara kansu a kai-a kai a daidai lokacin da ake tunkarar zaben rabin wa’adin, kuma Mr Scott ya ce shi bai gamsu da matsayin da ake ba.

 

Kwana daya kafin sannan an zabi dan majalisar wakilai daga California Kevin McCarthy na Republican a matsayin wanda zai maye gurbin shugabar majalisar Nancy Pelosi ‘yar Democrat.

 

 

To amma kafin a zabi mutum ya zama Shugaban Majalisar Wakilan, dole ne sai shugaban marassa rinjaye na Republican ya yi aiki a yanzu domin ya samu goyon baya mai rinjaye daga mambobi 435 na gaba dayan majalisar.

 

Shugaba Biden ya ce, "kamar yadda na fada a makon da ya gabata, yanayin da ake fuskanta na tattare da alherin da ba za a sake dambarwar siyasa ta dabaibaye shi ba.’’

 

‘’Al’ummar Amurka na son mu yi musu aiki. Sona son mu mayar da hankali kan abubuwan da suke da muhimmanci garesu da kuma inganta rayuwarsu,‘‘ in ji shi.

 

Ya kara da cewa, ‘’zan yi aiki da kowa dan REpublican ne ko kuma dan Democrat ne, wanda ke sony in aiki da ni domin bunkasa rayuwarsu.’’

 

A ranar 3 ga watan Janairu na 2023 ne za a kaddamar da sabbin majalisun dokokin biyu.