Abin da ya sa kotu ta tsare Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi a kurkuku

Bauchi Police

Asalin hoton, FACEBOOK/DUTSEN TANSHI MASJID BAUCHI

Wata kotun Majistare a Bauchi ta ba da umarnin tsare wani fitaccen malamin addinin Musulunci na jihar, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi a gidan yari.

Rundunar 'yan sandan jihar ce ta gurfanar da malamin mai janyo ka-ce-na-ce a gaban kotu ranar Litinin, bayan ta gayyace shi game da wani ƙorafi da aka shigar gabanta.

Matakin na zuwa ne sama da wata ɗaya bayan Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Bauchi ta ɗage wani zaman tattaunawa da ta shirya da Sheikh Idris Abdul’aziz, wanda aka yi zargin ya furta wasu miyagun kalamai a kan Annabi Muhammadu.

Sai dai malamin da wasu masu goyon bayansa sun musanta zargin, suna cewa kalaman Sheikh Idris Dutsen Tanshi, ba munana lafazi ba ne ga Fiyayyen Halitta.

Lamarin ya janyo muhawara mai zafi da ka-ce-na-ce har a tsakanin malaman addinin Musulunci da ke arewacin Najeriya, inda wasu suka fara kiraye-kirayen lallai hukumomi su ɗauki mataki.

Lauyan malamin Barista Umar Hassan ya tabbatar da cewa an tsare Sheikh Idris Abdul'aziz, bayan sun nemi a bayar da belin sa, kuma kotu ta sanya Talata a matsayin ranar da za ta ba da hukunci a kan wannan buƙata.

Lauyan malamin ya ce ƙungiyar Fityanul Islam ce ta shigar da ƙorafi a gaban 'yan sanda, abin da ya sa suka gayyace shi zuwa ofishinsu.

Ya ce ƙungiyar ta zargi Sheikh Idris Abdul'aziz da munana lafazi ga Annabi Muhammadu, kuma suka buƙaci a ɗauki mataki a kan sa.

Lauyan ya nanata wa BBC cewa malamin ya sha musanta wannan zargi da ake yi masa.

A cewarsa tun makon jiya ne ya kamata malamin ya amsa gayyata, amma sai ya aika wa 'yan sanda cewa wani uzuri, ba zai ba shi damar zuwa a lokacin ba.

Shi kuma, Sheikh Ya'u Idris, na'ibin Sheikh Idris Abdul'aziz ya shaida wa BBC cewa tun ƙarfe 10 na safe suka isa ofishin 'yan sanda don amsa gayyatar da aka yi wa malamin.

Kuma daga nan sai aka karanta wa Sheikh Idris Dutsen Tanshi ƙorafin da aka kawo gabansu game da shi, zargin da malamin ya musanta, kamar yadda Sheikh Ya'u Idris ya ce.

A cewarsa, "Don yadda su suke cewa, wai zagi. Mallam ya ce ba zagi ba ne. Sai ya musu bayani."

Daga nan kuma sai 'yan sanda suka ce za a tafi kotu kai tsaye, "Sai aka gama shirye-shiryen zuwa kotu, sannan suka ɗauke mu a motarsu zuwa kotu".

Wace tuhuma aka yi wa Sheikh Dutsen Tanshi?

Na'ibin Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi ya ce da aka je kotu an tuhumi malamin ne da laifin tada tarzoma, kamar yadda shi ma lauyansa ya tabbatar.

A cewarsa mai shigar ƙara na 'yan sanda ne ya gabatar da tuhumar, inda kuma aka bai wa Sheikh Dutsen Tanshi dama, shi kuma ya tashi, ya musanta zargin da aka yi masa.

Barista Umar Hassan ya ce bayan an karanto wa malamin wannan tuhuma kotu ta tambaye shi, ko yana da dalilin da zai hana a hukunta shi?

"Sai ya ce, eh yana da dalilin da zai hana a hukunta shi. Wannan maganar da aka faɗa cewa ya tada hankalin al'umma, ba gaskiya ba ne".

Ya faɗi haka a gaban alƙali, in ji Bar Umar.