A magance ɗumamar yanayi ko a fuskanci bala'i - MDD

yaro a kan ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi mummunar ambaliya a Pakistan a bana wadda masana ke dangantawa da sauyin yanayi

Dole ne ƙasashe su sake mayar da hankali tare da bayar da fifiko ga neman magance matsalar ɗumamar yanayi  ko kuma duniya ta fuskanci mummunan bala’i - in ji Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya a tattaunawarsa da BBC.

António Guterres na magana ne a New York yayin da ake shirin gudanar da babban taro kan yanayi a Masar.

Ya ce, ‘’Akwai alamar da ke nuna cewa za a mayar da batun sauyin yanayi baya, to lalle kuwa idan har aka yi haka to za mu samu kanmu cikin bala’i.’’

Taron wanda ake wa laƙabi da COP27, zai haɗa kan ƙasashe ne da za su tattauna kan yadda za a fuskanci matsalar sauyin yanayi.

Mista Guterres ya ce matsalolin da duniya ke ciki a yanzu  kamar hauhawar farashi  da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine da tashin farashin makamashi da abinci sun ɗauke hankalin duniya a yanzu.

A don haka ne ya ja hankalin duniya kan ta dawo da batun matsalar ɗumamar yanayi a gaba.

Babban Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya  ya ce bai kamata duniya ta kawar da kai daga muhimman abubuwan da ya kamata ta mayar da hankali a kai ba.

Abubuwan da suka haɗa da tabbatar da ƙaruwar yanayin zafi na duniya zuwa lamba 1.5 a ma’aunin selshiyas, domin kauce wa bala’in sauyin yanayi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce zai so ya ga Sarki Charles III da sabon Firaministan Birtaniya Rishi Sunak sun halarci babban taron na yanayi, yana mai cewa Sarki Charles, mutum ne da a kodayaushe yake magana kan matsalar sauyin yanayi.

Haka kuma ya yi kira ga Amurka da China da su haɗa kai su yi aiki tare a taron, yana mai cewa duniya ta dogara ga shugabancinsu.

A watan Agusta China ta ce za ta kawo ƙarshen haɗin kanta da Amurka a kan sauyin yanayi bayan da shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ziyarci Taiwan.

Ya yi gargaɗin cewa, "Wannan ita ce babbar matsala ta lokacinmu , ba wanda yake da ikon saryar da matakin da duniya za ta ɗauka a kan sauyin yanayi a kan kowa ne dalili.’’

Ya ƙara da cewa, "Muna buƙatar faɗa wa kanmu gaskiya. Maganar gaskiya ita ce, tuni aka fara ganin tasirin dumamar yanayi  a kan ƙasashe da dama a duniya musamman waɗanda suke tsakiyar abin.’’

Mista Guterres ya jaddada cewa dole ne gwamnatoci su  bayar da dala biliyan 100 da suka yi wa ƙasashe masu tasowa da ke fuskantar tsananin matsalar ɗumamar yanayi alkawari.

Wata mata dauke da kare yayin da wutar daji ke ci a bayanta a Girka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata dauke da kare yayin da gobarar daji ke ci a Girka

Babban Sakataren na Mjalisar Ɗinkin Duniya ya nuna cewa za a iya samun ragowar kuɗin daga tarin kuɗin harajin da za a samu na sayar da makamashi.

Daga nan kuma ya yi kira ga ƙasashe da kada su zuba jari a harkar bunƙasa makamashi mai ɗumama yanayi, maimakon haka su mayar da hankali kan harkokin bunƙasa makamashin da ba ya ɗumama yanayi.

Ya ce, ‘’babban abin sakarci shi ne, nuna tababa a kana bin da ya kai mu ga wannan bala’i.’’

Da aka tambaye shi ko shi da kansa zai halarci zanga-zanga kan yanayi, sai Mista Guterres ya ce ya shirya zanga-zanga a lokacin da yake matashi to amma yanzu aikinsa shi ne ba wai ya je daga wannan shinge zuwa wancan shinge na zanga-zanga ba, maimakon haka ya ce aikinsa shi ne ya matsa wa gwamnatoci lamba domin a samu sauyi.

Jagoran na Majalisar Dinkin Duniya ya ce za a yi maraba da kasancewar matashiyar mai fafutuka kan sauyin yanayi Greta Thunberg a taron na Masar, duk da cewa ta ce ba za ta halarci taron ba.

Haka kuma ya yaba da jagorancin da matasa ke yi a duniya inda suke kira da a mayar da hankali kan batun sauyin yanayi.

Hirar tasa da BBC ta zo daidai da lokacin da aka fitar da wani rahoto da ke gargaɗi cewa a 2021 an samu ɗumamar yanayi fiye da yadda aka taɓa samu a baya.

Hukumar kula da yanayi ta duniya wadda ta bayyana haka ta ce an samu gagarumar ƙaruwa ta  iskar methane yadda ba a taɓa gani ba a cikin shekara 40, abin da ya ba masana matukar mamaki.

A babban taron sauyin yanayin da za a yi a Sharm el-Sheikh a Masar daga ranar 6-18 na watan Nuwamba za a duba irin ci-gaban da aka samu a wannan fanni.

A bara, a wurin taron na yanayi ( COP26) a Glasgow, gwamnatoci sun yi alƙawarin ragewa ko ma daina amfani da makamashi mai ɗumama yanayi da kawo ƙarshen sare dazuka, su kuma samar da kuɗi  ga ƙasashe masu tasowa da ke fuskantar tsananin matsalar sauyin yanayi.

Taron na wannan shekara zai mayar da hankali ne a kan irin ci-gaban da aka samu da aiwatar da alƙawuran da aka yi .