Abu huɗu da ake la'akari kafin ƙirƙiro jihohi a Najeriya

A ƙarshen mako ne kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul ya amince da a ƙirƙiro ƙarin jihohi guda shida.
Wannan na cikin matsayar da aka cimma a ƙarshen taron ƙarawa juna sani na kwana biyu, wanda mataimakin majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu suka jagoranta a jihar Legas.
Kwamitin ya tattauna ne kan buƙatu guda 69, ciki har da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da buƙatar a ƙirƙiro ƙarin ƙananan hukumomin 278 kamar yadda rahotanni suka ruwaito.
A game da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi guda shida wato ɗaya kenan daga kowace shiyyar ƙasar guda shida.
Idan majalisa ta amince da ƙirƙirar sababbin jihohi, Najeriya za ta zama tana da jihohi 42 ke nan.
Waɗanne abubuwa ake la'akari da su kafin ƙirƙiro jihohi a Najeriya?
Buƙata
Dakta Bello Maisudan, malami a jami'ar Bayero da ke Kano kuma masanin kimiyyar siyasa ya shaida wa BBC cewa dole ne sai an dubi cewa shin akwai buƙatar samar da jiha a yankin da ake nema.
"Misali akan samu buƙatar kafa jiha idan akwai matsalar rikici tsakanin ƙabilu a yanki ko kuma ƙorafin danniya daga babbar ƙabila. Mun ga yadda aka samar da jihohin Bauchi da Nassarawa da wasu jihohin Neja Delta sakamakon irin wannan ƙorafin."
Yawan al'umma
Dakta Maisudan ya ce abu na biyu da ake yin la'akari da shi kafin a ƙirƙiri jiha a Najeriya shi ne yawan al'umma wanda shi ma wani abun dubawa ne.
"Shin jihar da za a yanki wata jiha daga cikinta tana da yawan jama'a? Sannan ita ma sabuwar jihar da za a samar za ta samu yawan jama'ar da ya dace da jiha? Misali kamar jihar Kano tana da yawan al'umma da yawan ƙananan hukumomi."
Girman ƙasa
Masanin ya ce ɗaya daga cikin abin da ake dubawa shi ne girman ƙasa na jihar da za a yanka da wadda za a ƙirƙira ɗin.
"Dole ne ne a dubawa cewa akwai faɗin ƙasa a jihar da za a yanka sannan jihar da za a samar za ta samu isasshiyar ƙasar da za ta dace da jiha? Domin idan aka duba aka ga ita jihar da za a yanka ɗin ba ta da girman ƙasa sannan ita ma wadda za a samar ba za ta samu isasshiyar ƙasa ba, to ka ga babu dalilin ƙirƙirar jihar." in Dakta Bello Maisudan.
Riƙe kai/ Tattalin arziƙi
Wannan shi ne babban ƙalubalen da ke gaban masu son a ƙirƙirar musu jiha.
"Wannan ma shi ne babban abin tambaya a ƙoƙarin ƙirƙirar sabuwar jiha. Shin ko jihar da za a ƙirƙira za ta iya riƙe kanta dangane da tattalin arziƙi?
"A nan ana duba irin kuɗin shiga da jihar za ta samu a cikin gida ko da babu kuɗin da zai rinƙa zuwa mata daga gwamnatin tarayya. Ba zai yiwu a ƙirƙira jiha ba amma duk wata sai ta jira kuɗi daga gwamnatin tarayya idan ba a turo mata to ba za ta iya biyan ko da albashi ba."
"Abin mamaki yawancin jihohin Najeriya a yanzu haka idan gwamnatin tarayya ba ta aike musu da kuɗin wata-wata ba to ba za su iya yin komai. Shi ya sa nake ganin ya kamata duk jihar da za a ƙirƙiro a nan gaba to wannan ya zama babban ma'uni," in ji Dakta Maisudan.
Matakan tsarin mulki kafin ƙirƙirar sabbin jihohi
Sashe na takwas tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima a 1999, ya gindaya sharuɗɗan da dole a cika su kafin a kai ga ƙirƙirar jihohi ko kuma gyaran iyakoki kamar haka:
- Buƙatar ƙirƙirar jiha ta samu goyon bayan aƙalla kaso biyu bisa uku na ƴan majalisar dattawa da wakilai da suka fito daga yankin da ke neman jihar, haka kuma sai an samu rinjayen kaso biyu bisa uku na majalisar ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashin yankin da ke son jiha.
- Dole ne ƙudirin ya samu goyon bayan al'ummar yankin da ke son jiha ta hanyar samun kaso biyu bisa uku na ƙuri'ar jin ra'ayin al'ummar.
- Sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayin mutane kan ƙudirin ya samu amincewar mafi yawan jihohin ƙasar tare da samun rinjayen majalisun dokokin jihohin ƙasar.
- Ƙudurin ya samu sahhalewar kaso biyu bisa uku na yawan ƴan majalisun dokokin ƙasar na dattawa da tarayya.
Muhimmanci da illolin ƙirƙirar sabbin jihohi
Dakta Bello MaiSudan amince cewa ƙirƙirar sabbin jihohi a Najeriya na da alfanu ga ƴan Najeriya kamar haka:
- Ƙara matso da gwamnati kusa da jama'a ta hanyar bai wa jama'a damar shiga harkokin gwamnati kai tsaye.
- Bunƙasar tattalin arziƙi sakamakon ci gaban da jihar za ta samu tattalin arziƙin al'ummar jihar ka iya samun bunƙasa.
- Ƙirƙirar sabbin jihohi ka iya sanya wasu al'ummu samun sauƙin daga danniyar manyan ƙabilu.
Sai dai kuma masanin ya ce idan aka dubi halin da ake ciki a Najeriya, za a ga kamar illolin da hakan zai haifar sun fi alfanun yawa. Sun zayyana wasu illoli guda da suka ce za su iya yi wa cigaban Najeriyar tarnaƙi:
- Kashe-kashen kuɗaɗen gwamnatin tarayya zai ƙaru musamman duba da yadda a yanzu haka wasu jihohin ƙasar ba sa iya riƙe kansu ba tare da kuɗi daga gwamnatin tsakiya ba. "Ya kamata yanzu a duba a ga irin halin da ƙasar take ciki musamman abin da ya shafi tattalin arziƙi da tsaro. Su ya kamata a magance ba batun ƙirƙirar jihohi ba." In ji dakta Bello MaiSudan.
- Rarrabuwar kai: Za a iya samun yanayin da maimakon a samu sauƙin rikici tsakanin al'ummomin da ke rikici suka nemi a raba su, sai kuma a samu rikici.











