Ba zan sake takarar ɗanmajalisa ba don ba matasa dama - Hon Dasuki

Danmajalisar da ke wakiltar Kebbe  da Tambuwal a majalisar wakilan Najeriya Abdussamad Dasuki

Asalin hoton, @abdussamadd

Lokacin karatu: Minti 2

Daya daga cikin ƴanmajalisar tarayya Abdussamad Dasuƙi ya ce ba zai sake tsayawa neman takarar danmajalisa ba kasancewar shekarunsa sun haura 40.

Danmajalisar da ke wakiltar Kebbe da Tambuwal a majalisar wakilan Najeriya ya shaida wa BBC cewa ya yi wannan sadaukarwar ne domin matasa da kuma zama abin koyi ga fafutikar da suka a gaba ta samar wa matasa gurbi a shugabanci a zaben 2027.

Honarabul Dasuƙi shi ne jagoran wata gwagwarmaya ta tabbatar da an ba matasa damar shiga a dama da su a harakokin mulki musamman kashi 75 a majalisun jihohi da na tarayyaya, mai taken "The Future is now" wato yanzu ne lokacin.

Ya ce matakinsa zai tamaka wajen ƙara futo da mahimmacin ba matasa damar a dama da su a harkokin mulki, a kowanne mataki ganin irin rawar da suke takawa a siyasance a Najeriya.

Ya ce sun ƙayyade shekarun matashi daga shekara 40 zuwa ƙasa - kuma a cewarsa, matasa ne fiye da kashi 75 a Najeriya.

"An ɗora min wannan jagoranci, ni kuma na ga cewa na wuce shekara 40 don haka nake ganin bai kamata na tafi ina yi wa matasa yaƙi ba bayan na haura waɗannan shekarun."

"Kafin ma wani ya fito ya ce kai wane mataki ka ɗauka na sadaukarwa saboda ci gaban matasa, don haka na ga cewa ba zan sake neman takara ba a majalisar tarayya a zaɓen 2027," in ji Hon Dasuki.

Ya ƙara da cewa duk wani ci gaba da ake nema a Najeriya dole sai an yi sadaukarwa, kuma ya yanke wannan shawarar ne bayan tuntubar abokan tafiyarsa da iyalinsa da kuma mutanen da yake wakilta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abdussamad Dasuki ya ce ba wai ya ɗauki wannan matakin ba ne saboda wata fargaba ko kuma tsoro illa neman cimma nasarar abin da suka sa a gaba a yanzu.

A 2011 aka fara zaɓensa a matsayin ɗanmajalisar jihar Sokoto, kuma Hon Abdussamad ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan kuɗi kafin zaɓensa a matsayin ɗanmajalisar tarayya a jihar Sokoto.

A watan Oktoban wannan shekarar ne ya jagoranci ƙaddamar da gwagwarmayar tabbatar da ba matasa dama a harakokin mulki a Najeriya.

Manufar gwagwarmayar ita ce samar wa matasa yan ƙasa da shekara 40 kashi 70 na kujerun majalisar wakilai a zaɓen 2027.

Da yake karin haske kan matakinsa, ɗanmajalisar ya ce matakin da ya ɗauka shi ne tabbatar da nuna daidaito ga manufarsa ta shigar da matasa a dama da su.

Ya kuma ce manufar ta shafi yin jagoranci ga matasan ta hanyar ɗora su a hanya da ba su horon da ya dace.

Matasa a Najeriya sun sha gudanar da zanga-zanga domin neman a ba su damar takara a muƙaman siyasa a ƙasar, ƙarƙashin wani gangami mai taken "Not too Young To run."

Fafutikar matasan ta yi tasiri inda aka amince da dokar da taƙaita shekarun muƙaman siyasa shekarar 2018 zamanin mulkin marigayi shugaba Buhari.

Dokar ta rage yawan shekarun wanda ke son takarar shugaban ƙasa daga 40 zuwa shekara 30. Haka ma na gwamna daga 35 zuwa 30. Ƴanmajalisar wakilai na tarayya da na jihohi daga shekara 30 zuwa 25.