Matsanancin zafi na ci gaba da gallabar kasashen Turai

Ma'aikatan kashe gobra na ci gaba da kokarin shawo kan wutar da ke kamari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ma'aikatan kashe gobra na ci gaba da kokarin shawo kan wutar da ke kamari

Yammacin Turai na ci gaba da fuskantar yanayi mai matukar zafi ranar Talata a yayin da matsalar tsananin zafi ta doshi arewacin nahiyar.

A Faransa da Birtaniya an gargadi mutane kan matsanancin zafin da za su yi fama da shi yayin da arewacin Sifaniya ya fuskanci zafin da ya kai maki 43 a ma'aunin selshiyos ranar Litinin.

Wutar daji mai matukar hadari ta watsu a kasashen Faransa, Portugal, Sifaniya da Girka, lamarin da ya tilasta wa dubban mutane tserewa daga gidajensu.

Ana sa ran a yau Birtaniya za ta yi fama da tsananin zafin da ba ta taba fuskanta ba kuma masana sun ce Faransa za ta fuskanci "tsananin zafi babu kakkautawa".

Wutar daji ta kashe mutum biyu a lardin Zamora da ke arewa maso yammacin Sifaniya sannan an dakatar da jigilar jiragen kasa a yankin saboda wutar ta kusanci layukan dogo.

Wata mata da mijnta da suka manyanta sun mutu yayin da suke kokarin tserewa daga inda wutar take ci a arewacin Portugal.

Yankuna da dama a Faransa sun yi fama da zafin da ba su taba fuskanta ta inda a birnin Nantes da ke yammacin kasar yanayin zafi ya kai maki 42 a ma'aunin selshiyos, kamar yadda ofishin da ke lura da yanayi na kasar ya bayyana.

Mahaukaciyar gobara da ta yi kamari a kwanakin baya bayan nan ta tilasta wa fiye da mutum 30,000 tserewa daga gidajensu, inda aka kafa gidajen wucin-gadi ga mutanen.

An kwashe dabbobin da ke wani gidan namun daji da ke da dabbobi 1,000.

Wannan yanki na Dune du Pilat na cikin wuraren da wutar dajin ta lalata a kusa da La Teste-de-Buch

Asalin hoton, Sira Thierij/BBC

Bayanan hoto, Wannan yanki na Dune du Pilat na cikin wuraren da wutar dajin ta lalata a kusa da La Teste-de-Buch