Barcelona na tunanin korar Xavi

XAVI

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Barcelona na duba yiwuwar korar kocin tawagarta Xavi.

A cikin watan Junairu ne, dan shekaru 44 din ya bayyana cewa zai sauka daga mukaminsa a karshen kakar wasa ta bana, amma sai shugaban kungiyar Joan Laporta ya lallashe shi, sai ya sauya shawara.

Amma kuma saboda kalamansa a tarukan manema labarai, a yanzu mahukunta kulob din suna fushi da shi kuma suna ganin ya kamata a raba gari da shi.

Kocin tawagar karamar kungiyar Barcelona, Rafael Marquez ne ake tunanin zai maye gurbinsa.

A ranar Alhamis bayan sun doke Almeria, Xavi ya ce akwai matukar wuya su iya gogayya da Real Madrid ta fannin kudi.

"Ina tunanin ya kamata magoya bayan Barcelona su fahimta a kan yanayi mai sarkakiya da ake ciki, ba za su iya goga kafada da Real Madrid a Sifaniya ba da kuma sauran a nahiyar Turai," in ji Xavi.

Real ta lashe gasar La Liga kuma a yanzu tana jiran buga wasan karshe a gasar zakarun Turai sannan kuma za su dauko Kylian Mbappe daga Paris St-Germain.

Xavi ya koma Barca ne daga kungiyar Al Sadd a watan Nuwamban 2021, sannan ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar La Liga a shekarar 2023.