Yadda ƙungiyoyin al'umma suke tasiri a lokacin zaɓe

Wasu daga cikin manyan ƙungiyoyin al`umma a Najeriya na ci gaba da fitowa suna karkata ga wasu da ke takarar shugabancin ƙasar.
Ƙungiyoyin suna yin haka ne da nufin jarraba irin nasu tasirin a kan siyasar ƙasar inda wasu ke ganin cewa yadda kungiyoyin ke jiɓantar ƴan takara ka iya rura wutar kabilanci ko ɓangaranci.
Ko a kwanakin baya sai da jagoran ƙungiyar Afenifere mai rajin kare muradun ƙabilar Yarabawa ya fito fili ya sanya wa ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam`iyyar APC, Bola Tinubu albarka, ta hanyar shafa masa kai tare da nuna goyon bayan ƙungiyar ga aniyar Tinubun.
Kazalika, ita ma kungiyar Ohanezi Ndi Igbo, mai kare muradan ƙabilar Igbo ta ce za ta goya wa ɗanta baya, wato ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam`iyyar Labour, Peter Obi.
Kawo yanzu dai, haɗakar kungiyoyin dattawan arewacin Najeriya ce ba ta fito kai-tsaye ta ce ga alƙibla ko inda ta dosa ba.
Su dai waɗannan ƙungiyoyin suna gwara-kwanji ne, inda kowacce ke jin cewa duk ɗan takarar da ta tsaya masa babu shakka zai kai labari.
Sai dai wasu na ganin cewa irin wannan karkata da ƙungiyoyi ke yi ga ƴan takara ka iya sa siyasar Najeriyar ta rikiɗe zuwa ƙabilanci ko ɓangaranci saboda tasirin su.
Amma masana siyasa a ɓangare guda na da ra`ayin cewa ƙungiyoyin suna da amfani a tsari irin na demokuradiyya.
Farfesa Jibrin Ibrahim masanin siyasa ne, kuma ya shaida wa Ibrahim Isa cewa irin waɗannan ƙungiyoyi suna da muhimmanci kuma yana da kyau su fito su gaya wa mutane abin da suke ganin shi ne daidai.
Duk da cewa ƙungiyoyion suna da irin nasu tasirin, Mallam Hassan Gimba da kan yi sharhi a kan siyasa da al`amuran yau da kullum ya ce tasirin bai kai yadda ake kambamawa ba.
A cewarsa, jama’a a ko wane yanki dama tuni sun yanke shawarar wanda za su zaɓa.
Sai dai masanan duka sun yi ittifakin cewa babu wata illa tattare da irin matsayar da ƙungiyoyi suke ɗauka.
A Najeriyar dai wasu ƙungiyoyi da ke sa ido a kan zabe sun yi gargaɗin cewa da yiwuwar ɓangaranci da ƙabalanci da kuma bambancin addini su mamaye babban zaɓen da ke tafe.











