Ɗabi'u takwas da tsofaffi masu shekara sama da 100 ke da su

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Fernanda Paúl
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Margarita Flores na tashi da sanyin safiya kullum, ta karya kumallo sannan ta yi tattaki idan ta dawo kuma ta yi karatu.
Ta ce tana son yin wasu ƙarin abubuwan, kamar zuwa wajen motsa jiki. To amma a shekara 107, kafafunta ba za su iya jurewa ba.
“Da son samu ne zan sa su aiki fiye da yadda suke yi a yanzu don su saba,” cikin raha ta gaya wa Fernanda Paúl ta BBC daga gidanta da ke birnin Santiago na kasar Chile.

Asalin hoton, Flores family
A lokacin tattaunawata da tsohuwar mai sama da shekara 100, tana magana tar-tar kuma a tsanake. Tana da ƙawaye da kuma wata 'yarta da take zama tare da ita a kullum.
“A shekarun nan nawa, har yanzu ina son yin wasu abubuwan da dama,” ta ce cikin nishaɗi.
Margarita na zaman kyakkyawan misali na ɗabi'un da ƙwararru ke cewa mutane da yawa da suka zarta shekara100, waɗanda har yanzu suke da lafiya yawanci suke da su: karsashi, da juriya da kuma son hira ko mu'amulla da wasu.

Asalin hoton, Getty Images
Margarita na zaman misali na abubuwan da ke ci gaba da faruwa.
Hukumar kula da yawan jama'a ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a yanzu ana kara samun tsofaffi da suke iya hure kyandir fiye da 100 a lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsu.
A shekarar 1990, mutum 92,000 ne kawai ke iya haka, to amma zuwa shekara ta 2021 yawan ya ninka zuwa 621,000.
Kodayake yanayi na halittar mutum da kuma irin salon rayuwarsa na da tasiri a kan hakan, kwararru da dama na cewa akwai yanayi na tunani da halayyar mutum da ke taka muhimmiyar rawa wajen samun hakan.
María Dolores Merino, kwararriya a ilimin halayyar jama'a kuma malama a jami'ar Complutense University da ke Madrid, a Sifaniya na ɗaya daga cikinsu. Tsawon shekaru tana gudanar da bincike na nazari a kan tsofaffin da suka wuce shekara 100.
A ɗaya daga cikin takardun da ta rubuta na baya-bayan nan da aka wallafa a mujallar,Journal of Happiness Studies, ta gano cewa wannan rukunin mutanen suna da wasu ɗabi'u 19 na bai ɗaya.
Ta karkasa su zuwa gida takwas, inda muka jero su a nan ƙasa.

Asalin hoton, Getty Images
1. Karsashi
Karsashi na ɗaya daga cikin ɗabi'u ko halayyar da aka gano tsofaffin da suka wuce shekara 100 suna da - duk da yawan sheakrunsu za ka ga suna cike da burin zama a raye, ga lura da kuma kazar-kazar.
“Abin mamaki ne sosai: tsofaffi masu shekara sama da 100 da muka tattauna da su suna cike da burin ci gaba da rayuwa,” María Dolores Merino ta yi wa BBC bayani.
Ta ƙara da cewa, “Idan kana magana da su ba za ka taɓa cewa wannan mutumin ya wuce shekara 100 ba. A gabaɗaya za ka ga yawanci idan kuna mu'amulla da su, ba sa nuna alamun mutumin da ya kai waɗannan shekaru.”

Asalin hoton, Getty Images
Daga cikin mutanen da Merino ta gudanar da bincike a kansu akwai mata da maza da suka ci gaba da aiki har sai da suka kai shekara 98 da haihuwa.
Sannan kuma sun kasance suna yin wasu abubuwa na motsa jiki da kuma motsa kwakwalwa, kamar hawa bene kullum da wasan karta da makamantansu.
Stacy Andersen na daya daga cikin darektocin cibiyar nazari kan tsofaffi masu sama da shekara 100 da ke Boston a Amurka ( New England Centenarian Study).
Ta yarda cewa karsashi shi ne babban abin da ke zama jagora a wannan nazari.
“Yawanci suna cewa suna jin daɗin rayuwa, wanda ni a wajena, wannan abin mamaki ne,” kamar yadda ta gaya wa BBC.

Asalin hoton, Getty Images
2. Son hira ko mu'amulla
Binciken María Dolores Merino, ya nuna cewa mutanen da suka wuce shekara 100 suna matuƙar son hira ko mu'amulla da sauran jama'a.
“Suan da kyakyawar alaka da iyalai da abokansu. Suna taimaka wa wasu idan har za su iya , kuma suna jin ana kaunarsu, wanda wannan abu ne mai muhimmanci,” in ji ƙwararriyar.
Stacy Andersen ta ce bincikenta ya gano cewa tsofaffi masu sama da shekara 100 mutane ne masu son magana da kuma kaunar haduwa da sababbin mutane.”
“Sai dai abin takaicin shi ne ɗaya daga cikin matsalolin kaiwa shekara 100 shi ne za ka rasa yawancin abokanai da danginka. Saboda haka abu ne mai muhimmanci da amfani a wajensu su yi sabbin abokanai da kawaye,” in ji ta.

Asalin hoton, Flores family
Margarita Flores ta ce abu ne mai amfani sosai ya zamanto kana da abokanai da kawaye”.
“Saboda ta haka ba za ka yi kewa ba,” in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
3. Jajircewa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani abin da bincike ya gano kuma shi ne irin waɗannan tsofaffi suna da jajircewa a kan abu.
“Mutane ne da suke da aniya da kuduri da kuma jajircewa a kan duk abin da suka sanya a gaba. Suna da burin cimma duk abin da suka sanya a gaba,” in ji María Dolores Merino.
Cibiyar da Stacy Andersen ke bincike (The New England Centenarian Study) ta jima tana nazari a kan halayyar 'ya'yan tsofaffi masu waɗannan shekaru, lokaci da dama. Ta ce saboda, "galibi suna bin sahun iyayensu ne.
“Kuma mun lura cewa hatta shekara 20 baya, tsawon rayuwa na da alaka da jajircewa da samun buri a rayuwa. Suna da burin da suke son su cimma. Wannan na zama jigo a gare su ga rayuwa a kullum,” in ji ta.
“Ɗaya daga cikin rukunan tsofaffin da aka gudanar da binciken a kansu sosai a Japan. Suna da wannan taken da suke kira 'Ikigai', wadda ke nufin tashi kullum safiya da wuri domin yin wani abu - wanda hakan ke da kamanceceniya da sanya wani buri a rayuwa.
"Ina ganin wannan na taka muhimmiyar rawa wajen kaiwa shekara 100," in ji Andersen.

Asalin hoton, Getty Images
4. Juriya
Juriya na ɗaya daga cikin muhimman halayen tsofaffin da suka kai shekara 100 ko fi kamar yadda bincike da dama ya nuna.
Juriya na da alaƙa kai tsaye da samun tsawon rayuwa.
Merino ta ce, “ɗabi'a ce mai karfin gaske , saboda tana sa ka iya ganin bayan duk wata damuwa ko matsala da ke gabanka, ba tare da ka bari wannan matsala ta yi maka illa ba.
“Samun tsawon rayuwa irin wannan abu ne da za ka ga lalle mutum ya sha kwaramniya da juriya ta shiga matsaloli da damuwa da dama, kama daga yaki ko annoba zuwa da rasuwar 'yan uwa ko iyalai.” Stacy Andersen ta nuna haka.
“Ba shakka suna damuwa a kan abubuwan da ke samun su na bacin rai, to amma suna jurewa su manta da su kamar ba su faru ba, su ci gaba da rayuwarsu kamar kullum,” ta ce.

Asalin hoton, Getty Images
5. Iko
Masu bincike sun nuna cewa tsofaffi masu sama da shekara 100, yawanci suna da halayya ta yanke shawara ta kan kansu ba wai wani ya sa su bi tunaninsa ba, in ji Merino.
"Haka kuma sun san yadda za su samu wata dama, da kuma yanke shawara kan abin da ya fi dacewa su yi ko wace dama ya kamata su bi."

Asalin hoton, Getty Images
6. Neman ilimi
Nazarin María Dolores Merino na baya-bayan nan ya nuna cewa tsofaffin da suka zarta shekara 100 yawanci, suna da halayya ta ƙwaƙwar neman sanin abu, da neman ilimi da kuma son su koyi abu da kansu.
Tsofaffin da aka tattauna da su wajen gudanar da wannan bincike sun nuna sha'awar sanin abin da ke wakana a duniya da kuma son koyon abu da kansu.
“Yawanci mutane ne da suke karanta littattafai sosai, inda suke da tarin littattafai na ban mamaki, ko da kuwa talakawa ne ko masu hali,” in ji Merino.
Margarita Flores na ɗaya daga cikinsu. A yanzu tana karanta littafin tarihin rayuwar Fafaroma Francis.
"To amma ina da wasu abubuwan da yawa da nake karantawa don gujewa zama haka - kama daga mujallun tufafin ado zuwa littattafan soyayya," ta fada cikin alfahari.

Asalin hoton, Getty Images
7. Kyakkyawan fata a rayuwa
“tabbas yawancin mutanen da suka wuce shekara100 za ka ga suna da kyakkyawan fata a rayuwa,” in ji Stacy Andersen.
"Ba kasafai za ka ji tsoho mai shekara sama da 100 ba, yana cewa, 'dama a ce ba na raye.' To amma idan ka tambayi mutum mai shekara 40, kana son ka kai shekara 100 a raye, yawanci za su ce maka 'a'a bana so'.''
Margarita Flores ta ce kodayaushe tana cike da kyakkyawan fata a rayuwarta.
"Kowa ce min yake ina cikin koshin lafiya... to eh, na yarda kodayaushe ina cikin kwanciyar hankali," in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
8. Basira
A ƙarshe, basira na daga cikin ɗabi'a ko halayya ta tsofaffin da suka zarta shekara 100 ( kuma basira na daga abubuwan da ke shafar sauran halayya)
Merino ta ce, waɗannan mutanen galibinsu suna da basira ta tunani da magance matsala cikin sauƙi da kuma koyon abu da sauri.
“Yawancin halaye da ɗabi'un irin waɗannan tsofaffi suna da alaka da basira.
"Misali suna da kyakkyawan sakamako na takardun makaranta da kuma na aiki, sannan da kansu suke koyon abu.
Suna yanke shawara da kansu kuma suna tunkarar ƙalubale ko da kuwa ba su da cikakkiyar ƙwarewa a wannan fanni sannan kuma su samu nasara.
''Suna da shauƙi ƙwakƙwafin sanin abu sannan kuma tattaunawarsu na da armashi da sauri baya ga rashin mantuwa da suke da,'' in ji rahoton nata.

Asalin hoton, Getty Images
-"Margarita, mene ne sirrin kaiwa shekara 107 a raye?" Na tambaye ta ta waya.
-"Ban sani ba. Ni dai kodayaushe ina jin daɗi. Kodayaushe ina da abin yi, saƙa ko wasu abubuwan. Ta haka, nake motsa ƙwaƙwalwata ta zama cikin aiki kodayaushe. Kuma ina ganin wannan ne ya sa nake ci gaba da rayuwa," ta ce.
Matar ita ce ta fi kowa shekaru a garinsu da ke Santiago, "La Reina".
Kuma duk da cewa ita kanta tana jin ta gaji, wato shekaru sun yi nisa, hukumomin garinsu sun yi alƙawarin shirya mata wata gagarumar liyafa idan ta kai shekara 110.
“Za mu gwangwaje da liyafa. Saboda haka ba lokacin huta,” ta faɗa cikin nishaɗi.

Asalin hoton, Getty Images











