Garkuwan Yahaya ya kashe Shagon Bahagon Ƴansanda

Garkuwan Yahayan Tarasa ya buge Shagon Bahagon Ƴansanda a damben safiyar Lahadi a Marabar Nƴanya jihar Nasarawa, Najeriya.
Tun farko Wazirin Labaran ɗan Gwamba ne ya hada wasa tsakanin Autan na Aisha da Shagon Bahagon Ƴansanda, ammna Autan na Aisha ya ki yin damben.
Daga nan aka hada tsakanin Garkuwan Yahayan Tarasa Guramaɗa da Shagon Bahagon Ƴansanda daga Jamus.
Nan da nan Alkalin wasa, Anas Ɗandume ya ɗaga hannayen ƴan damben da nufin cewar sune a kan layi.
Daga nan suka sa zare, inda a turmin farko Garkuwan Yahaya ya yi kokarin ɗan damben Jamus ya tsokane masa ido, hakan ya sa aka bashi lokaci ya goge fuskarsa.
Daga nan aka umarce su da su ci gaba da damben, inda ba a dauki wani dogon lokaci ba, Garkuwan Yahaya ya buge Shagon Bahagon Ƴansanda.
Ɗan wasan Jamus din ya ji haushin kisan da aka yi masa, domin ya dade a tsugeni kafin ya mike tsaye, daga baya ya ɗauki kaddarara.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga:
Damben Garkuyan Yahayan Tarasa da Shagon BahagonƳansanda shi ne na karshe da aka taka a Marabar Nƴanya gidan wasa na Idris Bambarewa.
Kafin shi an yi wasanni da yawa da aka yi kashe-kashe da wadanda aka yi canjaras
Wasannin da aka yi kisa:
- Bahagon Ushu ya buge Bahagon Ali Yaro
- Shagon Shamsu ya yi nasara a kan Shagon Jimama
- Aljanin Nokiya ya shimfidar da Jan Idon Guramaɗa
- Shagon Shamsu ya doke Shagon Terminator.
- Jan Idon Guramaɗa ya yi nasara a kan Shagon Jirgi
- Da wanda Shagon Zalama ya buge Shagon Terminator
Wasannin da aka yi canjaras:
- Ɗan Aliyu da Ilele Shagon Garkuwan Mai Caji
- Bokan Sama'ila da Bahagon Ƴansanda
- Bahagon Ushu da Bahagon Yahaya
- Mabilu da Garkuwan Ɗan Aliyu
- Garkuwan Isa da Boloƙo
- Ɗan Yalon Dijango da Shagon Jimama











