Fitattun marubutan finafinan Kannywood da suka yi tashe a 2024

Yakubu

Asalin hoton, Yakubu M. Kumo/Facebook

Lokacin karatu: Minti 2

A harkar finafinan Hausa na Kannywood, an fi mayar da hankali kan 'yan fim ɗin da suke fitowa, musamman ma waɗanda suka jagorantar finafinan, inda a kan manta da waɗanda suke bayan fage.

A harkar, akwai masu ruwa da tsaki da dama da suke bayar da gudunmuwa wajen ɗaukar fim, tun daga marubuta da masu fitilla da masu sauti da masu ɗaukar bidiyo da tsara dandali da zirga-zirga da sauransu.

A cikin waɗanda suke aiki a bayan fage, an fi sani furodusa da darakta, amma ba a cika ambaton sunan marubuta ba, waɗanda kuma alƙaliminsu ne yake saita fim, sannan idan ya samu aiki mai kyau, masu kallo su yaba.

Wannan ya sa a bana BBC ta rairayo wasu marubuta da alƙalumansu ta rubuta finafinai waɗanda suka yi shuhura a bana, duk da cewa akwai zaratan marubuta da a bana ba su yi wani aiki babba ba.

Yakubu M. Kumo

Yakubu M. Kumo, marubuci ne wanda a yanzu alƙaminsa ke tashe a rubuce-rubucen finafinan Kannywood.

Daga cikin fitattun finafinan da ya rubuta akwai Labarina da Manyan Mata da Jamilun Jiddan da Gidan Sarauta da sauransu.

Ya daɗe yana rubuta finafinai masu inganci waɗanda mutane suka yabawa.

Fauziyya D. Suleiman

Fauziyya marubuciya ce da ta daɗe tana rubuta fitattun finafinai masu ƙayatarwa, tun daga ƙananan har zuwa masu dogon zango.

Daga cikin fitattun finafinan da ta rubuta akwai Daɗin Kowa da take cikin marubutan fim ɗin, wanda zuwa yanzu an kai shekara 10 ana yi.

A cikin finafinan da suke tashe bana, ita ce ta rubuta fim ɗin da yake tashe a yanzu wato Garwashi, kuma tana cikin masu shiryawa.

Mujahid Koguna

Mujahid Koguna da Yakubu Mohammad ne suka haɗu wajen rubuta fim ɗin Allura cikin ruwa na 2Effects kuma ya rubuta fim ɗin Fansa.

Sauran fitattun marubutan da ake ji da su a Kannywood

Akwai zaratan marubuta irin su Abdulkarim Papalaje da rubuta fina-finai da dama; akwai irinsu Adamsy da Madubin Dubawa duka na Ali Nuhu da Ni da Matata da Oga Abuja da sauransu.

Nazir Adam Salihi da ya rubuta Gidan Badamasi da Jamil Nafseen da Nabila Rabi'u Zango da ya rubuta fim ɗin Umarni na furodusa Nazir Ɗanhajiya, waɗanda ana yabawa da su, amma wasu daga cikinsu a shekarar 2024 ba su yi rubutu ba.