Lukaku ya ƙulla yarjejeniya da Napoli, Aston Villa na neman Beier

Lukaku

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Brighton ta sallamawa Borussia Dortmund ɗan wasan tsakiyarta ɗan asalin ƙasar Jamus mai shekara 33, Pascal Gross a kan kuɗi £5.9m.(Guardian)

Chelsea na tattaunawa da Napoli domin sallama mata ɗan wasan gabanta kuma ɗan ƙasar Belgium mai shekara 31, Romelu Lukaku yayin da aker sa ran ɗan wasan gaban Najeriya mai taka leda a Napolin, Victor Osimhen zai koma Chelsea a matsayin aro.(Athletic - subscription required)

Chelsea da Aston Villa sun shiga zawarcin ɗan wasan gaban Bayer Leverkusen mai shekara 21, kuma ɗan asalin Jamus, Maximilian Beier. (Sky Germany)

Da alama an samu ɓaraka a yunƙurin Monza na ɗaukar mai tsaron ragar Nottingham Forest kuma ɗan Costa Rica, Keylor Navas bayan ɓangarorin biyu sun gaza cimma matsaya wajen tattaunawa. (Fabrizio Romano)

West Ham na shirin janyewa daga zawarcin ɗan wasan gefen Leeds mai shekara 22, Crysencio Summerville. (Talksport)

Ɗan wasan Manchester United da Tunisia, Hannibal Mejbri mai shekara 21 na shirin komawa Rangers da taka leda. Ƙungiyar ta Scotland na fatan ɗaukar shi a matsayin aro amma United ta fi son ciniki ya kaya. (Teamtalk)

Aston Villa na zawarcin dan wasan gaban Faransa mai shekara 27 da ke taka leda a Crystal Palace, Jean-Philippe Mateta. (Express)

Everton na nazarin shiga zawarcin ɗan wasan gaban Ingila mai taka leda a Roma, Tammy Abraham. (Sportitalia)

Manchester United na tattaunawa da ɗan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 29, Adrien Rabiot, bayan kwangilarsa da Juventus ta ƙare a bana. (Caughtoffside)

Liverpool na shirin ɗauko ɗan wasan tsakiya kafin a rufe kasuwar cinikin ƴan wasa a ƙarshen watan Ogusta. (Football Insider)