Abu biyar da suka kamata wanda ya rasa iyayensa ya yi

Wata uwa da 'ya'yanta

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Rashin iyaye ba ƙaramin al'amari ba ne ga iyalan mamata, musamman ma ƴaƴansu, waɗanda suke buƙatarsu domin shawarwari da ma nuna musu ƙauna ta hanyar kula da su a lokacin da tsufa ya riske su.

A duk da lokacin da ƴaƴa suka yi rashin iyayensu, suka shiga wani hali na damuwa da kaɗaici da ƙunci na wani lokacin - wasu ma sukan faɗa cikin ƙuncin da yake taɓa musu rayuwa na dindindin.

A daidai lokacin da mutum ke cikin wannan yanayi akan ba shi shawarwarin yadda zai tafiyar da rayuwarsu ta hanyar amincewa da ikon Allah.

Wannan ya sa BBC ta tattauna da fitaccen malamin Addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa domin jin wasu muhimman abubuwan da ya kamata wanda ya rasa iyayensa ya yi.

Abubuwan da suka kamata ya yi

Sheikh Daurawa

Asalin hoton, FACEBOOK/MAL.AMINU IBRAHIM DAURAWA

Da yake yi wa BBC ƙarin haske kan matakan da suka kamata a ɗauka bayan rasa iyayen, ko wani daga cikinsu, Sheikh Daurawa ya lissafo su kamar haka:

  • Addu'a: Kamar yadda Alqur'ani ya bayyana mutum zai riƙa musu addu'ar, 'Allah Ka musu rahama kamar yadda suka raine ni ina ƙarami." Haka kuma annabawa da dama sun yi addu'o'in samun rahama ga iyayensu da ma muminai.
  • Sadaka mai gudana: Shehin malamin ya ce haƙƙi na biyu shi ne mutum ya yi wata sadaka kamar gina Masallaci ko makaranta ko haƙa rijiya ko dasa bishiya ko wani abu da jama'a za su riƙa amfani da shi, domin a riƙa kai musu lada.
  • Sada zumunta: Sheikh Daurawa ya ce haƙƙi na uku shi ne a sadar musu da zumunta ta hanyar ziyartar ƴan'uwansu da sauran abokansu na arziki, saboda a duk lokacin da suka ganka, za su tuna da su, su yi musu addu'a, ko kuma idan ka musu wani abun arziki za su ji daɗi sannan su yi musu addu'a.
  • Biyan bashi: Malam ya ƙara da cewa akwai kuma sauke musu nauyin bashin da ake binsu. "Idan ana binsu bashi ko akwai wani nauyi na jama'a a kansu na jama'a ka yi ƙoƙari ka sauke musu ta hanyar biya musu bashin, ko idan akwai wata rigima ka nemi a yafe musu idan ka tabbatar su ne ba su da gaskiya, sai ka nemi mai haƙƙi ya yafe musu.
  • Ziyartarsu: Wani abu da malamin ya ƙara shi ne ƙoƙarin ziyartar inda suke. "Lokaci bayan lokaci idan ka san inda ƙabarinsu yake ka riƙa zuwa kana musu addu'a, kana musu ziyara da neman Allah ya yafe musu. Sannan duk abin za ka yi na kirki wanda za a ce Allah ya saka wa iyayenka a cigaba da yi.

Sheikh Daurawa ya ce bin iyaye "tamkar bin bashi ne da ibada. An ce za ka biya bashi, ka ci bashi, ka yi ajiya.

''Ka biya bashi shi ne ka kyautata wa iyayenka, ka ci bashi shi ne ka kyautatawa ƴanuwan da dangi da iyalanka."