Dabarun yin azumi a lokacin zafi

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar lura da yanayi ta Najeriya - Nimet ta fitar da rahoton gargaɗi kan tsananin zafin rana da za a fuskanta a wasu jihohin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Nimet ta ce za a samu ƙarin yanayin zafi na tsawon kwanaki uku zuwa huɗu, lamarin da zai iya jefa al'ummar jihohin cikin matsi.
Hakan na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmi a ƙasashen duniya ke gudanar da azumin watan Ramadana, inda sukan ƙaurace wa ci da sha daga asuba har zuwa faɗuwar rana.
Wannan na nufin masu azumi ba za su iya shan ruwa ko wani abu da zai taimaka musu wajen kashe ƙishi ko yunwa ba.
To sai dai akwai shawarwari kan dabarun da mai azumi zai iya amfani da su domin rage hatsarin da zai iya faɗawa ciki sanadiyyar zafin yanayi.
Jihohin da yanayin zafin zai fi shafa a Najeriya su ne na arewa ta tsakiya da kuma na kudu maso gabashin ƙasar:
Kebbi, Neja, Kwara, Oyo, Kogi, Nassarawa, Benue, Enugu, Anambra, Abia, Ebonyi, Cross River da Abuja.
Sauran jihohin da ke cikin haɗarin yanayin na zafi kuma su ne:
Taraba, Adamawa, Filato, Kaduna, Zamfara da Sokoto.
Illar yanayin zafi ga lafiya
Bayanin na Hukumar kula da yanayi na Najeriya ya nuna cewa illolin da mutane za su iya fuskanta sanadiyyar yanayin zafin su ne:
- Gajiya/Jiri
- Rashin iya mayar da hankali
- Rashin iya gudanar da aiki yadda ya kamata
Dabarun kare kai
Masana sun bayar da shawarwari kan yadda mutum zai kare kansa daga illolin da zafin rana ke haifarwa.
- Kasancewa cikin sanyi: Amfani da fanka, ko na'urar sanyaya ɗaki ko kuma zama a inuwa
- Sanya kaya marasa nauyi: A sanya kaya waɗanda iska za ta iya shiga ta cikinsu.
- Shan ruwa mai yawa: A sha ruwa sosai idan an yi buɗe-baki da kuma lokacin sahur.
- Zama a ɗaki: A guje wa fita waje lokacin garjin rana, tsakanin ƙarfe 12 na rana zuwa uku na yamma.
- Wanka da ruwan sanyi
- Neman wuri mai sanyi: Zuwa wurare masu sanyi kamar gine-ginen gwamnati ko ɗakunan karatu, da kuma wuraren shaƙatawa masu bishiyoyi da furanni.
- Amfani da kariya: A sanya malafa da baƙin tabarau da kuma amfani da man shafawa mai bayar da kariya daga rana.











