Masu zanga-zanga a Brazil sun far wa gine-ginen gwamnati

.

Shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, ya sha alwashin hukunta magoya bayan tsohon shugaban ƙasar, Jair Bolsonaro bayan da suka afka cikin Kotun Kolin ƙasar.

Magoya bayan tsohon shugaban ƙasar mai tsattsauran ra’ayi sun afka cikin Kotun Koli da kuma yin ƙawanya wa fadar shugaban ƙasa.

Sai dai ‘yan sanda sun sake karɓe iko da wuraren da ke Brasilia babban birnin ƙasar da yammacin ranar Lahadi bayan shafe sa’o’i ana artabu.

Shugaba Lula ya kai ziyara Kotun Kolin ƙasar domin ganin irin ɓarnar da aka yi bayan isar sa birnin.

‘Yan sandan Brazil sun ce an kama mutane 300 kawo yanzu.

Kotun Kolin Brazil ta tsige gwamnan babban birnin ƙasar, Ibaneis Rocha, daga muƙaminsa kwanaki 90 da suka wuce.

Mai shari’a Alexandre de Moraes, ya zargi gwamnan da kin dakatar da tarzomar da aka tayar da kuma kin yin magana lokacin da suka afka wa fadar shugaban ƙasa.

Sai dai mista Rocha ya nemi afuwa kan abubuwan da suka faru a ranar Lahadi.

Shugabanni da kuniyoyi masu ra’ayin riƙau a faɗin Brazil ne ke kiran gangamin neman rajin dimokuraɗiyya.

An ga dubban masu zanga-zanga sanye da riguna masu kore na kungiyar kwallon ƙafar ƙasar na artabu da ‘yan sanda da kuma lalata abubuwa a tsakiyar ƙasar makonni kalilan bayan rantsar da sabon shugaba Lula.

An tursasa wa shugaban mai tsattsauran ra’ayi ayyana dokar ta-ɓaci kafin aikewa da jami’an tsaro zuwa babban birnin ƙasar domin mayar da doka da oda.

Ya kuma umurci a rufe tsakiyar ƙasar – haɗe da wuraren da gine-ginen gwamnati ke da zama na tsawon sa’a 24.

.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ministan shari’a, Flavio Dino ya ce an kwace motocin bas 40 wadanda aka yi amfani da su domin daukar masu zanga-zanga zuwa babban birnin ƙasar, inda ya kira abin da suka yi da ‘yunkurin tursasa zaman masu zanga-zanga da ƙarfin tuwo’’.

Mista Bolsonaro dai ya ki amincewa ya sha kaye a zaɓen da aka gudanar a watan Oktoban bara, inda ya fice ya bar ƙasar a makon da ya gabata maimakon ya tsaya a rantsar da sabon shugaban ƙasa.

Bolsanaro mai shekara 67 wanda ake kyautata zaton cewa yana Florida – ya yi Alla-wadai da harin sannan ya musanta hannu wajen ƙarfafa wa masu bore a wani bayani da aka wallafa a shafin tuwita, sa’o’i shida bayan barkewar tarzomar.

Da yake magana kafin isar sa Brasilia, babban birnin ƙasar, Lula ya ce ‘‘irin wannan tarzomar ba ta taɓa faruwa ba a tarihin Brazil’’ inda ya kira hakan da abin Alla-wadai.

Sannan ya soki jami’an tsaron ƙasar wadanda ya zarga da rashin iya aiki saboda kin dakatar da masu zanga-zanga shiga Kotun Kolin ƙasar.

''Za ka ga a cikin hotunan ‘yan sanda na nuna wa mutane hanyar da za su bi zuwa dandalin Praca dos Tres Powers," in ji Lula.

‘Za mu yi bincike domin gano wadanda suka dauki nauyin masu zanga-zangar da suka je Brasilia sannan za mu hukunt su.''

Hotunan bidiyo da jaridar O Globo ta wallafa, sun nuna wasu jami’ai na dariya da kuma daukar hotuna lokacin da masu boren ke kokarin shiga Kotun Kolin ƙasar.

.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ɓalla tagogi yayin da wasu kuma suka shiga zauren Majalisar dattijai, inda suka yi ta tsalle a kan kujeru.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna masu zanga-zanga na ture wani dan sanda daga kan dokinsa da kuma far masa a wajen ginin majalisar.

Hotuna da kafafen yaɗa labaran ƙasar suka watsa, sun nuna ‘yan sanda na tsare da gomman masu zanga-zanga da ke sanye da korayen riguna a wajen fadar shugaban ƙasa.

An ɗaure hannuwan wasu da ake zargi ta baya – da kuma fitar da su daga ginin.

Masu zanga-zanga sun yi ta taruwa tun sanyin safiya a wajen majalisar dokoki kilomitoci kaɗan da titin Esplanada wanda ke layi ɗaya da wajen da ma’aikatun gwamnati suke da kuma wuraren tarihi.

Sa’o’i kalilan kafin tarzomar, an ga da yawan jami’an tsaro da aka girke sun toshe hanyoyi kusa da majalisar dokoki, inda jami’an tsaro ke rike da makamai a kofar shiga majalisar.

BBC ta ga ‘yan sanda a safiyar Lahadi inda ake hana motoci shiga majalisar, yayin da ake binciken jakukkunan masu shiga da kafa.

.

Sai dai masu zanga-zangar sun mayar da martani kan abin da suka aikata lokacin da manema labarai suka nemi ji daga gare su.

Wata mai suna Lima mai shekara 27 wacce kuma ta kasance injiniya ta ce ‘ya kamata mu dawo da abubuwa yadda suke bayan wannan zaɓe mai cike da maguɗi.’’

''Na zo nan ne don tarihi, domin kuma ‘ya’yana,’’ in ji Lima.

Wasu kuma sun yi Alla-wadai da abubuwan da masu zanga-zangar suka aikata inda suka kwatanta shi da ranar bakin ciki a fadin Brazil.

''Na zaɓi Bolsonaro amma ban amince da abubuwan da suke yi ba,’’ in ji Daniel Lacerda, mai shekara 21.

"Idan baka amince da shugaban ƙasa ba ka fito kawai ka faɗa sannan ka yi harkokin gabanka, ba wai ka fita zanga-zanga ba kamar yadda wasu ke yi.’’

.

Mutane da yawa na kwatanta hakan da irin tarzomar da ta faru na mamayar majalisar dokokin Amurka da ke Capitol a ranar 6 ga watan Janairun 2021, da magoya bayan Donald Trump suka yi, wanda abokin Bolsonaro ne.

Magoya bayan Bolsonaro sun kafa tantuna a fadin biranen Brazil, wasu kuma a wajen sansanonin soji saboda yawancin su suna son sojoji su sa baki da yin zaɓe mai gaskiya.

Sai dai ana ganin kamar bukatarsu ba za ta karɓu ba saboda ganin an rantsar da shugaba Lula – an tarwasa sansanoni da suka kafa a Brasilia kuma babu wata matsala da aka fuskanta ranar da aka rantsar da shi.

Sai dai abubuwan da suka faru a ranar Lahadi sun sake ɗora ayar tambaya.

A cewar Wakilin BBC na Kudancin Amurka, wasu masu zanga-zanga ba wai suna fushi ne kawai don Bolsonaro ya faɗi zaɓe ba – sai dai suna son shugaba Lula ya koma gidan yari.

Ya shafe watanni 18 a ɗaure bayan samun sa da laifin cin hanci da rashawa a 2017 inda daga baya aka soke zargin da kuma hukuncin wanda a farko ya kai ɗaurin shekara sama da 90.

.

Shugabannin duniya da dama ne dai suka mayar da martani na yin Alla-wadai da abin da masu zanga-zangar suka yi.

.