Masanin kimiyyar Habasha da ke neman ruwa a duniyar wata

..

Asalin hoton, Berhanu Bulcha

Mai binciken kimiyya na ƙasar Amurka da Habasha, Injiniya Berhanu Bulcha na neman mafita ta yadda za a samu ruwa a duniyar wata domin bil adama su kafa sansani na din-din-din a can.

Idan babu ruwa a can, babu wanda zai rayu ko da kuwa bil'adama na nan duniya ko kuma wata duniyar ta daban dole sai da ruwa.

An harba kumbo na sama jannati samfurin Artemis 1 a bana, a wannan makon - wanda hakan duk wani yunƙuri ne na gudanar da wani gagarumin bincike da nufin mayar da bil'adama duniyar ta wata ko kuma can gaba.

Tattaunawa kan batun yadda za a samu ruwa abu ne mai muhimmanci.

Za a iya ɗaukar ruwa a kai shi duniyar ta wata amma hakan zai zamo abu ne mai matuƙar tsada kuma ba zai isa ba.

Haka kuma ruwan da ke duniyar watan za a iya amfani da shi domin samar da man da za a rinƙa zuba wa kumbo, wanda hakan zai bayar da dama ga duniyar watar ta zama wurin da za a rinƙa zirga-zirga.

Tambaya ta miliyoyin daloli

Dakta Berhanu da abokan aikinsa na haɗa wata na'ura ta musamman wadda za ta iya gano ko akwai ruwa a duniyar ta wata.

"Wannan wata tambaya ce ta miliyoyin daloli," kamar yadda ya shaida wa BBC ta waya daga ɗaya daga cikin ofisoshin hukumar NASA ta Amurka.

Tun bayan da ya kammala jami'a a Virginia, shekara 12 da suka gabata, Dakta Berhanu ya yi ta mayar da hankali ne kan abubuwan da za su kawo ci gaba ga NASA, haka kuma batun neman ruwa a duniyar wata shi ne babbar matsalar da NASA ke neman ta magance.

Tuni dai aka tabbatar da cewa akwai ruwa a duniyar ta wata.

Amma babbar matsalar ita ce hanyoyin da ake bi domin gano ruwan ba su iya tantance ruwan da ke da akwai ko suna ɗauke da sinadarin hydrogen da Oxygen da hydroxyl ne.

.

Asalin hoton, Nasa/Michael Guinto

Na'urar da Dakta Berhanu ke aiki a kai na fitar da wuta-wuta domin neman ruwa.

Abokan aikinsa na aiki domin samar da abin da ake kira 'quantum cascade lasers'.

Dakta Berhanu na alaƙanta wannan ci gaban kimiyyar da zai ba ƴan sama jannati dama su yi amfani da na'urar hannu su gano wurin da ruwa yake da adadinsa - wanda wannan wani abu ne da ba a taɓa yi ba.

Haka kuma za a iya girke ƴar ƙaramar na'urar a wata ƙaramar mota da ke amfani da remote.

..

Asalin hoton, Reuters

Kamar yadda NASA ta tabbatar, Dakta Berhanu a kwanan nan ya karɓi dala miliyan 2.5 domin ci gaba da bincikensa da samar da na'urar.

Za a iya ɗaukar shekara biyu kafin a kammala binciken amma Dakta Berhanu ya ce yana da yaƙinin cewa za su cimma burinsu.

Matashin mai shekara 38 ya girma a Addis Ababa, babban birnin Habasha, amma daga baya ya koma Amurka bayan ya kammala sakandire domin ya koyi ilimin Physics da Injiniya a Jami'ar Virginia Commonwealth University.

Ya bayyana cewa wani mataki ne ya ɗauka na hatsari idan ya bar Habasha amma damar da ya samu ya yi aiki kan kimiyya da fasaha ba zai iya bari ta wuce shi ba.

Ya ce ya taso ne kan turbar Addinin Kirista kuma ya bayyana cewa fara karatun Littafin Bible ya sa ya fara yin tambayoyi kan duniyar da kuma yadda abubuwa suke.