Waiwaye: Amince wa Tinubu karɓo bashi da kama jagoran 'yan awaren IPOB

Lokacin karatu: Minti 5

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Simon Ekpa

Asalin hoton, Simon Ekpa/Twitter

A makon da muke bankwana da shi ne hukumomin ƙasar Finland suka kama jagoran ƙungiyar ƴan awaren Biafra ta IPOB, Simon Ekpa, inda suka samu izinin ci gaba da tsare shi har lokacin da za a yi masa shari'a.

Hukumomin sun kama shi ne bisa zargin tunzura mutane su aikata ayyukan ta'addanci.

Hukumomin Najeriya sun ji daɗin hakan tare da nuna sha'awar ganin an miƙa masu shi domin ya fuskanci shari'a a Najeriyar.

Simon Ekpa ya daɗe yana iƙirarin cewa shi shugaban wani ɓangare ne na ƙungiyar IPOB, mai neman ɓallewar yankin Biyafara daga Najeriya.

Har yanzu ba mu ɗauki matsaya kan ƙudurin harajin Tinubu ba - Kakakin Majalisa

Abbas Tajudeen

Asalin hoton, OTHERS

Harwayau a ranar Litinin da ta gabata ne shugaban majalisar wakilan Najeriya, Abbas Tajudeen, ya ce har yanzu majalisar ba ta ɗauki matsaya ba a kan sabon ƙudirin haraji na gwamnatin Tinubu ba.

Ya bayyana hakan ne kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a jawabinsa na buɗe tattauna kan sabon ƙudirin harajin a zauren majalisar da ke Abuja a ranar.

Sai dai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya ce majalisar za ta yi aikin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na tantancewa kan duk tanadin ƙudurin tare da yin gyara inda ya zama wajibi.

Ana kitsa shirin mallake arewacin Najeriya daga Legas - Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso

Asalin hoton, OTHER

A ranar Litinin da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa sabon ƙudurin dokar haraji da gwamnatin tarayya ta gabatar zai daƙile kuɗaɗen da ake samu a jihohi irinsu Kano ta hanyar harajin VAT.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a taron yaye ɗalibai karo na uku da jami’ar skyline University da ke Kano ta gudanar.

Jagoran jam'iyyar NNPP, ya ƙara da cewa ''A yau muna ganin a bayyane yadda ake wani yanƙuri daga ɓangaren Legas na neman ta mamaye yankin arewacin Najeriya, muna ganin yadda wasu 'matasa' daga Legas ke neman su ƙaƙaba mana haraji domin su tattara kuɗaden da muke samu daga harajin VAT da Kano da ɓangaren arewacin ƙasar nan zuwa Legas'.

Kwankwaso ya yi kira ga ƴan majalisar da suka fito daga yankin Arewacin ƙasar da su farka su tabbatar ba a yi wa yankin sakiyar da babu ruwa ba ta kowace hanya.

Ɗangote ya fara fitar da man kamfaninsa zuwa ƙasashen Afirka ta yamma

Aliko Dangote

Asalin hoton, Getty Images

Matatar man Ɗangote ta fara fitar da tacaccen mai zuwa ƙasashen Afirka ta yamma masu maƙwabtaka, a wani sabon yanayin kasuwanci da ka iya sauya kasuwar mai a Afirka, kamar yadda wani rahoto da mujallar Bloomberg ta fitar ranar Talata ta makon da ya kare ya ambato .

Bayanai da aka samu daga Vortexa da Kpler da Priecise Intelligence da ke bin diddigin bayanan jiragen ruwa, ya ce wani jirgin ruwa ɗauke da mai daga kamfanin Ɗangote inda ya nufi ƙasar Togo mai maƙwabtaka.

A watan da ya gabata ne shugaban kamfanin man ƙasar Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ya ce ƙasar tasa na shirin sayen man daga hannun Ɗangote domin taimakon ƙasar rage yawan kuɗaɗen da take kashewa wajen shigar da mai daga nahiyar Turai kimanin dala 400 a kowane wata.

ACF ta dakatar da shugabanta kan zaɓen ɗan takara a 2027

'Yan kungiyar ACF

Asalin hoton, OTHERS

A ranar Alhamis ne ƙungiyar tuntuɓa ta dattawan arewa wato Arewa Consultative Forum ta ce ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta, Mamman Mike Osuman dangane da wasu kalamai da aka alaƙanta da shugaban a wani taronta da ta yi ranar Laraba a Kaduna.

A wata sanarwa mai sa hannun Alhaji Bashir Muhammad da Alhaji Murtala Aliyu, ƙungiyar ta musanta wasu bayanai da ke yawo cewa sun bayyana goyon bayan fito da ɗantakarar shugaban ƙasar Najeriya daga yankin arewa a 2027.

Ƙungiyar ta kuma ce yankin na arewa na fama da ƙangin talauci da matsalar tsaro da jahilci, inda ta bayyana cewa gundarin matsalar yankin na hannun ‘yan arewa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa an jirkita bayanan ta wata fuskar da ba ita ce alƙiblar da ta ɗauka ba.

Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya ciyo bashin naira triliyan 1.77

Shugaba Tinubu na rubutu

Asalin hoton, STATE HOUSE

A ranar Alhamis da ta gabata ne Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da buƙatar Shugaban ƙasar Bola Tinubu na ciyo bashin $2.2, wanda ya kai kimanin naira tiriliyan 1.77, domin amfani da kudin wajen cike giɓin kasafin kuɗin bana.

Majalisar ta amince da buƙatar ne bayan kwamitin ciyo bashi daga ciki da wajen ƙasar, ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko mai wakiltar Sokoto ta arewa ya gabatar da rahotonsa.

Daily Trust ta ruwaito cewa idan aka karɓo wannan sabon bashin, bashin da ake bin Najeriya zai kama naira tiriliyan 136 kenan.

Majalisar Wakilai ta yi fatali da ƙudirin wa'adin mulki ɗaya na shekara shida ga shugaban ƙasa da gwamnoni

Majalisar Wakilan Najeriya

Asalin hoton, House of Reps Nigeria/Facebook

A ranar Alhamis da ta gabata, kudurin ɓukatar yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima don mayar da wa'adin mulkin ƙasar zuwa wa'adi ɗaya na shekara shida ga shugaban ƙasa da gwamnoni ya gamu da cikas a majalisar wakilan ƙasar, inda suka yi watsi da shi.

Ƙudirin wanda Ikenga Ugochinyere ya gabatar ya buƙaci a zagaya da matsayin shugabancin ƙasar zuwa yankuna ƙasar shida, tare da bukatar gudanar da duka zaɓukan ƙasar a rana guda.

A lokacin da aka gabatar da kuɗirin domin karatu na biyu a zauren majalisar, sai mafi yawan 'yan majalaisar suka yi fatali da shi.

ACF ta dakatar da shugabanta kan zaɓen ɗan takara a 2027

Mambobin ACF

Asalin hoton, OTHERS

Na yi farin cikin kama Simon Ekpa - CG Musa

Janar Christopher Gwabin Musa

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Alhamis ne Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya ce ya yi fari ciki da kamen da hukumomin Finland suka yi wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware ta IPOB ta Najeriya, Simon Ekpa.

Cikin wani saƙo da kakakin ma'aikata tsaron ƙasar, Manjo Janar Tukur Gusau ya aike wa BBC ya ce babban hafsan tsaron ƙasar ya ce yana fatan kamen ya zama wani mataki na tisa ƙeyar Mista ekpa zuwa Najeriya don ya fuskanci sharia.

Hukumomin Finland sun kama Simon Ekpa tare da aika shi gidan yarin ƙasar, byan gurfanar da shi a kotu, kan zargin tunzura mutane su aikata ayyukan ta'addanci, kotun ta ce ta samu Simon Ekpa ne da laifin yaɗa aƙidu na ƴan aware a kafar sada zumunta, a ranar 23 ga watan Agustan 2021 a birnin Lahti na ƙasar ta Finland.