Yahudawa masu mamaya na korar Falasɗinawa daga gidajensu akai-akai

- Marubuci, Jake Tacchi, Ziad Al-Qattan, Emir Nader & Matthew Cassel
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
- Lokacin karatu: Minti 6
A watan Oktoban da ya gabata, dattijuwa Bafalasɗiniya Ayesha Shtayyeh ta ce wani mutum ya nuna ta da bindiga kuma ya umarce ta da fita daga gidan da take zaune tsawon shekara 50.
Ta faɗa wa BBC cewa barazanar da ake yi musu na ƙara zama wata hanyar muzgunawa da tilastawa tun daga 2021, bayan kafa wani sansanin ƴan mamaya a kusa da gidanta da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Adadin matsugunan sun ƙaru sosai a ƴan shekarun nan, kamar yadda binciken BBC ya gano. Yanzu akwai irin waɗannan matsugunai aƙalla 196 a Gaɓar Yamman, kuma 29 daga cikinsu an yi su ne cikin shekarar da ta gabata - fiye da kowace shekara.
Matsugunan da suka ƙunshi gonaki, da gidaje - da yawa ba su da iyaka a hukumance kuma sun saɓa wa dokokin Isra'ila kanta da kuma ƙasashen duniya.
Sai dai sashen ƙasashen ƙetare na BBC ya ga wasu takardu da ke nuna wasu ƙungiyoyi da ke ƙawance da gwamnatin Isra'ila suna ba da kuɗi da filaye domin gina haramtattun matsugunan.
BBC ta kuma nazarci wasu majiyoyi na fili domin tantance ƙaruwar gina su, sannan ta binciki ɗan mamayar da Ayesha Shtayyeh ta ce ya yi mata barazana.

Asalin hoton, Matthew Cassel / BBC
Babu wani adadi na sansanonin a hukumance. Amma sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Eye ya nazarci jerin su da kuma inda suke wanda wata ƙungiyar yaƙi da masu mamaya a Isra'ila ta tattara mai suna Peace Now da kuma Kerem Navot - har ma Hukumar Falasɗinawa da ke iko da wani ɓangare na Gaɓar Yamman.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mun duba hotunan tauraron ɗan'adam domin fayyace wurare da kuma lokutan da aka gina sansanonin. Haka nan, mun duba shafukan zumunta, da takardun gwamnati, da kafofin yaɗa labarai.
Bincikenmu ya gano kusan rabi (89) daga cikin 196 da muka tabbatar an gina su ne tun daga 2019.
A farkon shekarar nan gwamnatin Birtaniya ta saka wa wasu ƴan mamaya takunkumi saboda tunzirawa da kuma haddasa tashin hankali a kan Falasɗinawa. Aƙalla shida daga cikinsu na zaune ko kuma su suka kafa wasu haramtattun sansanoni.
Wani tsohon kwamanda a rundunar sojin Isra'ila, Avi Mizrahi, ya ce akasarin mazauna sansanonin masu bin doka ne amma kuma ya amince cewa kasancewarsu a wurin na ƙara barazanar tashin hankali.
"Duk lokacin da ka ƙirƙiri haramtaccen sansani a wurin, yana jawo tashin hankali ga Falasɗinawa...da ke zaune a yankin," a cewarsa.
Ɗaya daga cikin masu tsattsauran ra'ayi da Birtaniya ta saka wa takunkumi shi ne Moshe Sharvit - mutumin da Ayesha ta ce ya yi barazanar harbinta. Shi da sansanin da ya kafa Amurka ta ƙaƙaba wa takunkumi a watan Maris da ya gabata.
"Ya ƙuntata wa rayuwarmu," in ji Ayesha, wadda yanzu dole take zaune tare da ɗanta a wani gari da ke kusa da Nablus.
Sansanonin ba su da wani tsari ko amincewar gwamnatin Isra'ila - ba kamar matsugunai ba waɗanda gwamnati ke gina wa Yahudawa a Gabar Yamma kuma waɗanda ba su saɓa wa dokar Isra'ilar ba.
Dukkansu sun saɓa wa dokokiin ƙasa da ƙasa, waɗanda suka haramta mayar da fararen hula zuwa wani yanki da aka mamaye. Sai dai Yahudawa da yawa kan ce yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan haƙƙinsu ne.
A watan Yuli, babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce ya kamata Isra'ila ta dakatar da gina duk wani sabon matsuguni kuma ta kwashe masu mamaya daga wuraren da suka mamaye na ƙasar Falasɗinawa.
Isra'ila ta yi watsi da umarnin a matsayin "kuskure" kuma mai nuna ɓangaranci.
Duk da cewa sansanonin sun saɓa wa doka, babu wata hujja da ke nuna gwamnatin Isra'ila na ƙoƙarin hana gina su.
BBC ta ga yadda wasu ƙungiyoyi masu alaƙa da gwamnati suka bayar da filaye da kuɗaɗe domin gina sababbin sansanoni.

Asalin hoton, Matthew Cassel / BBC
Ɗaya daga ciki ita ce World Zionist Organization (WZO), wata ƙungiyar ƙasa da ƙasa da aka kafa sama da shekara 100 da suka wuce kuma take da hannu wajen kafa ƙasar Yahudawa. Tana da ofishin kula da yankunan da Isra'ila ta mamaye tun daga 1967.
Takardun da ƙungiyar Peace Now ta samu sun nuna yadda sashen WZO ya ba da filayen da aka gina sansanoni. Takardun sun nuna cewa WZO ta haramta yin gini a filayen tana mai cewa kiwo da noma kawai za a yi - amma hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna an yi gini a huɗu daga cikin filayen.
Mun nemi jin ta bakin WZO game da filayen da ta bayar kuma aka gina gidaje, amma ba ta ce komai ba. Mun kuma nemi ji daga Zvi Bar Yosef, shi ma bai ce komai ba.
BBC ta bankaɗo wasu takardu da ke kwarmata wata ƙungiyar 'yan mamaya mai suna Amana. Ta ba da bashin dubun dubatar kuɗi don a gina sansanonin.
A wani wuri, ƙungiyar ta ba da bashin kuɗin Isra'ila NIS 1,000,000 (dala 270,000) ga wani ɗan mamaya don ya gina gidaje a wani haramtaccen sansani.
An kafa Amana a 1978 kuma ta yi aiki tare da gwamnatin Isra'ila wajen gina mastugunai a faɗin Gabar Yamma.
Sai dai a shekarun nan, akwai hujjoji da ke nuna Amana na taimakawa wajen gina haramtattun sansanoni.
BBC ta nemi bayani daga Amana kan dalilin da ya sa take ba da bashi don gina haramtattun sansanoni. Ba ta ce komai ba.
An ga kuma yadda gwamnatin Isra'ila ta dinga halasta haramtattun sansanoni a baya - inda ake mayar da su matsugunai. A shekarar da ta wuce misali, gwamnati ta fara shirin halasta sansani 10 kuma ta bai wa aƙalla shida daga ciki takardun halasci.

Asalin hoton, Matthew Cassel / BBC
A watan Fabarairu Moshe Sharvit - Bayahude ɗan mamaya da ya kori Ayesha daga gidanta - ya shirya wani fati a sansaninsa kuma aka ɗauka a bidiyo. Ya bayyana yadda za a yi amfani da sansanonin wajen karɓe yankunan Falasɗinawa.
""Babbar matsalar da muke fuskanta ['yan mamaya] ita ce muna maƙalewa a cikin iyakarmu kuma ba za mu iya faɗaɗawa ba," kamar yadda ya faɗa wa mahalarta taron.
"Gonar na da muhimmanci amma babban abin da ya fi shi ne yankunan da ke kewaye da mu."
Ta hanyar hana Falasɗinawa bin wasu hanyoyi, mazauna sansanonin kan jefa manoma mawuyacin hali, a cewar Maayad Shaaban, shugaban hukumar kula da mulkin mallaka ta Hukumar Falasɗinawa.
"Abin ya kai ga Falasɗinawa ba su da komai ma. Ba za su iya cin abinci ba, ba za su iya fita kiwo ba, ba su iya samun ruwa," in ji shi.
Bayan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba a kudancin Isra'ila da kuma hare-haren Isra'ilar a ka Gaza, Moshe ya tsaurara tsangwamar da yake yi wa Falasɗinawa, kamar yadda Ariel Moran da ke tallafa wa Falasɗinawa ya faɗa.
Ofishin OCHA na MDD ya ce cikin wata 10 da suka wuce, ta tattara rahoton sama da hare-hare 1,100 kan Falasɗinawa. Yahudawa masu mamaya sun kashe Falasɗinawa aƙalla 10 kuma sun raunata sama da 230.
An kash aƙalla ƴan mamaya biyar tare da raunata 17 a arangamar da suka yi da Falasɗinawa a Gabar Yamma a wancan tsakanin, in ji OCHA.

Asalin hoton, Matthew Cassel / BBC
A watan Disamban 2023, wata biyu bayan korarsu daga gidansu, mun ɗauki Ayesha da Nabil lokacin da suke komawa gidan domin ɗaukar wasu kayayyakinsu.

Asalin hoton, Matthew Cassel / BBC
Mun sha tuntuɓar Moshe Sharvit don jin ta bakinsa game da zarge-zargen, amma bai taɓa cewa komai ba.
A watan Yulin 2023, BBC ta tunkare shi gaba da gaba a sansaninsa. Ya ce bai san abin da muke magana a kai ba kuma ba shi ne Moshe Sharvit ba.







