Simeone ya bukaci Atletico ta mayar da hankali kan wasa da Real

Diego Simeone

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Diego Simeone ya yi kira ga ƴan wasan Atletico su mayar da hankali kan wasan da za su je Real Madrid a Champions League, maimakon murnar zama na ɗaya a teburi.

Ranar Talata Real za ta karɓi bakuncin Atletico a wasan farko zagayen ƴan 16 a gasar zakarun Turai, wasan hamayya na ƴan birnin Madrid.

Ranar Asabar Atletico Madrid ta haye kan teburin La Liga, bayan da ta yi nasara a kan Athletic Bilbao 1-0 wasan mako na 26.

Hakan ya sa Atletico ta haɗa maki 56 a matakin farko a teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakani da Barcelona da kuma Real Madrid.

Ranar Asabar Real ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Real Betis a babbar gasar tamaula ta Sifanya.

Sai dai Barcelona za ta iya komawa ta farko a kan teburin La Liga da zarar ta doke Real Sociedad ranar Lahadi.

''Muna da babban wasa a Champions League yanzu haka, ya kamata mu mayar da hankali kan karawar, mu kuma samu hutu a wannan kwana ukun da muke da shi,'' in ji Simeone.

''Yanzu abin da ya kamata shi ne mu haɗa karfi waje ɗaya, domin fuskantar kalubalen da ke gaban mu.''

Wasa shida da yake gaban Atletico Madrid:

Champions League Ranar Talata 4 ga watan Maris

  • Real Madrid da Atl Madrid

Spanish Liga Ranar Lahadi 9 ga watan Maris

  • Getafe da Atl Madrid

Champions League Ranar Laraba 12 ga watan Maris

  • Atl Madrid da Real Madrid

Spanish Liga Ranar Lahadi 16 ga watan Maris

  • Atl Madrid da Barcelona

Spanish Liga Ranar Lahadi 30 ga watan Maris

  • Espanyol da Atl Madrid

Copa del Rey Ranar Laraba 2 ga watan Afirilu

  • Atl Madrid da Barcelona