West Ham na zawarcin Trippier, Chelsea ta ƙulla yarjejeniya da Omorodion

Asalin hoton, Getty Images
West Ham na zawarcin ɗan wasan bayan Ingila mai shekara 33, Kieran Trippier, wanda kwangilarsa da Newcastle ke ƙarewa kuma babu wata alamar tsawaita ta. (Telegraph - subscription required)
Da alama Manchester United za ta gabatarwa ɗan wasan tsakiyar Burnley da Norway mai shekara 26, Sander Berge tayin kwangilar £100,000 kowanne mako domin ɗaukar shi zuwa Old Trafford. (Sun)
Chelsea ta amince, za ta biya Atlentico Madrid £35m domin ɗaukar ɗan wasan gaban Sifaniya mai shekara 20, Samu Omorodion. Wata majiya ta ce ɗan wasan ya shirya zuwa a gwada lafiyar sa gabanin ƙulla yarjejeniyar (Fabrizio Romano)
Ana sa ran ɗan wasan tsakiyar Real Sociedad, Martin Zubimendi zai amince da sauya sheƙa zuwa Liverpool amma har yanzu ɗan wasan mai shekara 25 bai ƙulla yarjejeniya ba kawo yanzu. (Athletic - subscription required)
Ɗan wasan gaban Albania mai taka leda a Chelsea, Armando Broja zai gana da kocinsa Enzo Maresca domin cimma matsaya a game da makomarsa. Everton da Wolves na daga cikin masu bibiyar ɗan wasn mai shekara 22 (Mail)
West Ham na neman ɗaukar ɗan wasan bayan Chelsea da Ingila mai shekara 26, Trevoh Chalobah, da kuma ɗan wasan bayan Jamus mai shekara 35, Mats Hummels, wanda kwangilarsa da Borussia Dortmund ta ƙare a bana. (Sky Sports)
Crystal Palace na zawarcin ɗan wasan bayan Chelsea Chalobah, ta na kuma bibiyar ɗan wasan bayan Faransa mai shekara 24, wanda ke leda a Wolfsburg, Maxence Lacroix (Telegraph)
Har yanzu Liverpool na da sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaban Jamus da Hoffenheim, Maximilian Beier, amma ɗan wasan mai shekara 21 ya fi son komawa Borussia Dortmund. (Sky Germany)
Ɗan wasan bayan Aston Villa mai shekara 31, Lucas Digne ya ƙi amincewa da tayin komawa taka leda a Galatasaray. Ana sa ran ɗan wasan Faransan ya ci gaba da zama a Villa. (Athletic - subscription required)
Valencia ta dakatar da tattaunawar sayar da ɗan wasan tsakiyar Sifaniya mai shekara 21 Javi Guerra ga Atletico Madrid. (Athletic - subscription required)














