Fashewar na'urori ta biyu a Lebanon ta hallaka mutum 20 da jikkata 450

Asalin hoton, OTHERS
Akalla mutum 20 ne suka mutu, wasu sama da 450 suka ji rauni a wasu fashe-fashe karo na biyu da abubuwan sadarwa da suka hada da wayoyin hannu na oba-oba da suka yi a Lebanon in ji ma’aikatar lafiya ta kasar.
Wayoyin hannu da kananan kwamfutoci na tafi-da-gidanka da kungiyar Hezbollah ke amfani da su ne suka rika fashewa a yankin kudancin Beirut, da kwarin Bekaa da sauran yankunan da ake ganin Hezbollah na da karfi sosai a kasar.
Wannan fashewar ta biyu da ta auku ta kasance ne a lokacin jana’izar wasu daga cikin mutum 12, da ma’aikatar lafiya ta kasar ta Lebanon ta ce sun mutu lokacin da kananan na’urorin sadarwa da mambobin Hezbollah ke amfani da su suka fashe, fashewar da Hezbollah ta dora alhaki a kan Isra’ila, wadda ita kuma ba ta ce komai ba.
Harin ya kasance ne a lokacin da ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant, ya sanar da cewa sun shiga wani sabon babi na yakin, inda suka karkata ga yankin arewa.
Babban Sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya yi gargadin barkewar fadan, inda ya yi kira ga dukkanin bangarorin rikicin da su kai zuciya nesa.
Ya ce, ba shakka dukkanin wannan fashewar kananan na’urorin da ake gani ba wani abu ba ne illa sharar fage ne na wani babban aikin soji, kamar yadda ya gaya wa manema labarai.
Tuni daman ana cikin fargabar barkewar gagarumin rikici bayan wata 11 na fadan kan iyaka da yakin Isra’ila da Hamas a Gaza ya haddasa.
Sa’o’i bayan fashe-fashen ranar Laraba, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya lashi takobin mayar da dubban ‘yan Isra’ila da aka kwashe daga arewacin kasar saboda hare-haren Hezbollah.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumomin sojin Isra’ila sun tabbatar da tura wata runduna da a da take yaki a Gaza zuwa yankin arewacin.
Hezbollah ta ce tana yin abin da take yi ne domin mara baya ga Hamas - wadda Iran ma ke mara wa baya – kungiyar da Isra’ila da kasashen yamma da dama suka ayyana a matsayin ta ta’addanci.
Kuma Hezbollah ta ce za ta daina kai harin na kan iyaka ne kawai idan aka dakatar da yakin Gaza.
Za a ga alamun abin da kungiyar kila za ta yi na martani a ranar Alhamis, a lokacin da jagoranta, mai karfin fadi a ji, Hassan Nasrallah, zai yi jawabi.
Fashe-fashen na ranar Laraba wani abin kunya ne ga kungiyar ta Hezbollah, da ake gani kamar Isra’ila ta yi nasarar satar shiga harkokin sadarwar kungiyar.
‘Yan Lebanon da dama, har yanzu na cike da mamaki da kuma bakin ciki kan abin da ya faru a ranar Talata, a lokacin da dubban kananan na’urorin sadarwa suka rika fashewa a lokaci daya, bayan jama’a sun sami wani sako da suke ganin daga kungiyar ta Hezbollah ne.
Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce, mutum 12 da suka hada da wata karamar yarinya mai shekara 8 da wani yaro mai shekara 11 na daga cikin wadanda suka mutu da kuma mutum 2,800 da suka ji rauni a fashewar.
Wani ayarin ma’aikatan BBC da ya halarci jana’izar hudu daga cikin mutanen da fashewar ta hallaka a kudancin wajen Beirut na Dahiya a ranar Laraba, ya ce sun ji wata fashewa mai karfi a lokacin.
Sai kuma rudani da hatsaniya suka biyo baya a tsakanin masu jana’izar, inda daga nan kuma rahotanni ke ta zuwa cewa an samu fashewa a saurann sassan kasar ta Lebanon ma.
An ga wani hoton bidiyo da ba a tabbatar da sahihancinsa ba a shafukan sada zumunta da muhawara, da ke nuna wani mutum ya fadi bayan wata fashewa a lokacin wani taron jama’a na Hezbollah.
Kungiyar agaji ta Red Cross a Lebanon ta ce sama da motocin daukar marassa lafiya 30 ne suka rika kai dauki a fashe-fashen a wajen kudancin babban birnin, Beirut da sauran wasu sassan birnin.
Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce an hari na’urorin oba-oba ne da mambobin Hezbollah ke amfani da su.
Kungiyar ta ce, na’urar da aka hara ita ce samfurin ICOM-V82, wadda yanzu sun dakatar da amfani da ita.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce, wata majiya ta bangaren tsaron Lebanon ta danganta na’urar ta oba-oba da cewa Hezbollah ta saye ta ne kusan a lokaci daya - wata biyar baya da waccan karamar na’urar sadarwar da ta fara fashewa.
Shafin yada labarai ta intanet na Anxios, ya ruwaito cewa jami'an leken asiri na Isra'ila sun yi nasarar kutse a harkar samar da na'urorin ga Hezbollah, inda suka dasa abubuwan fashewa a dubban wadannan na'urorin kafin a bai wa 'yan Hezbollah.
BBC ta tuntubi reshen kamfanin na ICOM da ke Birtaniya dangane da zargin, to amma ya mika wannan bukata ga hedikwatarsa da ke Japan.











