'An kashe duka iyalaina ciki har da 'yan huɗun da matata ta haifa'

Asalin hoton, Handout
- Marubuci, Alex Smith
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, London
- Lokacin karatu: Minti 4
Wani ma'aikacin jinya a Gaza ya shaida wa BBC cewa an kashe matarsa da 'ya'yansa shida, ciki har da 'yan huɗun da ta haifa a wani hari da aka kai tsakiyar birnin Gaza.
"An shafe duka iyalaina a harin", in ji Ashraf El Attar, yana mai cewa "yanzu babu abin da ya rage min".
Ma'aikacin jinyar - wanda ke aiki a asibitin Turawa da ke birnin Gaza - ya ce an kai hari ka gidan suke zaune tare da matarsa a Deir-al-Balah da safiyar ranar Lahadi, inda shi kaɗai ne ya tsira da ƙananan raunuka.
Yayin da yake zantawa da sashen Larabci na BBC, ma'aikacin jinyar ya ce da misalin ƙarfe 6:00 na asubahi ranar yana shirin tafiya wajen aiki, sai kwatsam ya ce na'urar ankararwa na ƙara.
Ya ce nan take ya fita waje da sauri, inda fitarsa ke da wuya aka ruguza gidan nasa gaba-ɗaya.
Isra'ila ba ta yi magana kan wannan hari ba, sai dai ta ce dakarunta na kai hare-hare a birnin. Ta kuma ce tana kai hare-haren ne kan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
Waɗanda suka mutu a harin sun haɗa da matarsa - Hala Khattab, wadda malamar makaranta ce, da 'ya'yansu shida - mai shekara 15 da 'yan huɗun da suka haifa masu shekara goma-goma da ƙanwarsu mai shekara guda.
"Na yi ta kiran sunan matata da 'ya'yana, amma babu wanda ya amsa, saboda gaba-ɗaya sun mutu'', in ji shi.
"'Ya'yana shida, ciki har da 'yan huɗu, da matar tawa duk sun mutu nan take'', in ji Mista El Attar.
Ya ƙara da cewa ba su yi tsammanin harin ba a lokacin. A cikin daren da ya gabaci mutuwarsu, iyalan sun kwashe tsawon lokaci suna hira cikin nishaɗi da walwala, cike da muradin ganin ƙarshen yaƙin da ake yi a Gaza.

Mahaifiyar El Attar - kaka ga 'ya'yan nasa shida - ta ce ba za ita bayanin yadda harin ya aukawa gidan nasu ba.
"Ɗana Ashraf ma'aikacin jinya ne a asibitin Turawa da ke Gaza, inda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ceton rayukan jama'a ta hanyar taimaka wa marasa lafiya.
"Ba mu da alaƙa da kowace ƙungiya," in ji kakar marigayan 'ya'yan.
Shi da matarsa sun "ɗauki lokaci mai tsawo suna shan wahalar renon 'ya'yansu, musamman 'yan huɗun da suka haifa'', in ji ta.
"Jariran sun fuskanci matsananciyar jinya a lokacin da aka haife su''.
"Har sai da muka sayi tukunyar iskar oxygen muka ajiye a gida saboda yadda suke buƙatar iskar oxygen, kuma an taɓa yi wa ɗaya daga cikinsu, mai suna Hammam, tiyata a ciki'', in ji dattijuwar.

Asalin hoton, Handout
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mista El Attar ya ce matarsa - Hala - ta "sadaukar da kanta" don taimaka wa 'yan gudun hijira.
Tana aiki ne da ƙungiyar agaji da Majalisar Dinkin Duniya ta (Unrwa), da ke tallafa wa 'yan gudun hijirar Falasɗinawa, kamar yadda mijin nata ya bayyana.
Ma'aikacin jinyar ya ce wannan iftila'i da ya same shi, ya tilasta masa rayuwar kaɗaici.
"Ina aiki, tuƙuru domin tallafa wa iyalina, kuma nakan ji daɗin ganin 'ya'yana suna tasowa, ina da burin samar musu ingantacciyar rayuwa - in gina babban gida, na sayi babbar mota, kuma saya musu manyan wayoyi ," in ji shi.
Amma yanzu ''duka wannan buri nawa ya daƙushe''.
"Ina buƙatar samun adalci game da kisan iyalina",wani abu da yake fatan samu ta hanyar shigar da ƙara a "kotun duniya".
"Isra'ila ta aikata babban zalunci. An shafe duka iyalaina a lokaci guda, inda aka barni ba tare da komai ba a yanzu."
Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba kan harin, amma ta ce ta kai hare-hare a yanzin Deir al-Balah a ƙarshen mako.
A wata sanarwar da ta fitar ranar Litinin, Rundunar sojin Isra'ilar ta ce ta kai hare-hare a wajen birnin Deir al-Balah "inda ta kashe 'yanta'adda tare da lalata, gine-ginen mayaƙan da ke kan tudu da kuma ƙarƙashin ƙasa".
Ta ce tana kai hare-haren ne kawai kan mambobin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai, sannan ta ɗora alhakin mutuwar fararen hula kan ƙungiyar Hamas - waɗanda ta ce ta girke mayaƙanta, da makamai da rokoki a hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da gidajen yankin.
Ƙungiyar Hamas wadda ta jagoranci wani hari a ranar 7 ga watan Octoban 2023, ta kashe kusan mutum 1,200, tare da yin garkuwa da mutum 251 zuwa Gaza.
Harin ya janyo zazzafan martani daga ɓangaren sojin Isra'ila, waɗanda suka ƙaddamar da hare-hare a Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40,170 a Gaza, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta bayyana.











