Liverpool da Barcelona na hamayya kan Leao, Bayern ta rage farashin Coman

Rafael Leao

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, .
Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool na nazarin ɗaukar ɗan wasan Portugal Rafael Leao, mai shekara 25, amma za ta fuskanci hmayya daga Barcelona, wanda ita ma ke zawarcin ɗan wasan gaban na AC Milan. (Teamtalk)

Bayern Munich ta rage farashin ta ƙaƙabawa Kingsley Coman, mai shekara 28, wanda Arsenal ke zawarci yayin da ta ke neman sayar da ɗan wasan na Faransa a bazara. (Bild - in German)

Ɗan wasan gaban Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25, ya shaida wa Liverpool cewa yana son barin ƙungiyar a watan Janairu amma an hana shi komawa kulob ɗin Al-Hilal na gasar Saudi Pro League. (Football Insider)

Tottenham na da yaƙinin cewa tana kan gaba a jerin masu zawarcin ɗan wasan tsakiyar Ingila Tyler Dibling, mai shekara 19, wanda bai yi amanna da sabon kwantiragin da Southampton ta miƙa masa ba. (Talksport)

Manchester City na son daukar ɗan wasan Leicester City Jeremy Monga amma sai an kammala tantace diyyar da za ta biya kan ɗan wasan Ingilan mai shekara 15. (Sun)

Haka kuma ƙungiyar Pep Guardiola na zawarcin ɗan wasan AC Milan da Faransa Theo Hernandez mai shekara 27. (Caught Offside)

Eric Dier, mai shekara 31, zai so ya ci gaba da zama a Bayern Munich bayan ƙarshen kwantiraginsa a bana, amma tsohon ɗan wasan bayan Tottenham da Ingila yana jiran kulob ɗin ya yanke shawara akan makomarsa. (Florian Plettenberg)

Dan wasan bayan Manchester United da Sweden Victor Lindelof, mai shekara 30, yana son barin ƙungiyar a bazarar nan domin ya koma tsohuwar ƙungiyarsa Benfica. (Record)

Ɗan wasan Ingila Jack Grealish, mai shekara 29, zai iya barin Manchester City a bazara mai zuwa. (Mail)

Ana kyautata zaton Milos Kerkez, mai shekara 21, zai bar Bournemouth a bazara yayin da Liverpool ke ci gaba da bibiyar ɗan wasan bayan na Hungary. (Fabrizio Romano)

West Ham na iya ƙalubalantar Newcastle kan zawarcin ɗan wasan gaban Strasbourg ɗan ƙasar Holland Emanuel Emegha mai shekara 22. (GiveMeSport)

Liverpool na harin ɗan wasan Wolfsburg Konstantinos Koulierakis, mai shekara 21, amma za ta iya fuskantar gogayya daga Crystal Palace da Aston Villa kan ɗan wasan bayan na ƙasar Girka. (Caught Offside)

Ɗan wasan baya na Southampton da Ingila Taylor Harwood-Bellis, mai shekara 23, yana son ci gaba da taka leda a matakin Premier League a kakar wasa mai zuwa inda ya ke jan hankalin Crystal Palace da West Ham. (Football Insider)