Me ke janyo yawan saɓani tsakanin gwamnan Kano da rundunar ƴansanda?

..

Asalin hoton, BBC COLLAGE

Bayanan hoto, Ba wannan ne karon farko ba da gwamnan Kano ke samun saɓani da kwamishinan ƴansanda ba.
Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Laraba 1 ga watan Oktoban 2025 ne Gwamnan jihar Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya cire kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Bakori daga mukaminsa.

Yayin da yake jawabi a bikin ranar cikar Najeriya shekara 65 da samun ƴancin kai, da aka gudanar a filin wasa na Kofar Mata, gwamnan ya nuna ɓacin ransa kan abin da ya kira ''halin rashin kishin ƙasa da kwamishinan ke nunawa a jihar''.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ɓangarorin biyu ke samun sartse a alaƙarsu, al'amarin da masana ke ganin ka iya jjanyo ƙamarin matsalolin tsaro a jihar.

Hakan ne ya sa BBC ta yi duba dangane da abubuwan da ke haddasa rashin jituwar da illar hakan da kuma hanyoyin da ya kamata a bi domin warware rikicin.

Abin da ya faru

..

Asalin hoton, ABBA KABIR/X

Gwamna Abba Kabir Yusuf dai ya zargi kwamishinan da janye jami'an ƴansanda daga filin taron a daidai lokacin da ake dab da farawa.

''A yau kowane ɗan Najeriya na murna da zagayowar ranar samun ƴancin kan ƙasarmu,... amma a matsayinsa na kwamishinan ƴansanda ya yi abin da ya kunyata mutanen Kano'', in ji Gwamnan.

''Sai da aka kusa fara wannan biki, kawai ya janye duka jami'an ƴansandan da ke wannan wuri, inda ba don sauran jami'an tsaro da muke da su ba da wannan taron ba zai samu armashi ba'', in ji shi.

"A matsayina na jagoran gwamnatin Kano da mutanen Kano suka zaɓa, mun yi Allah wadai da wannan hali na rashin nuna kishin ƙasa da wannan kwamishinan ke nuna mana, wannan ya saɓa ƙa'idar aiki, sannan cin aiki ne''.

''Don haka ina kira da babbar murya ga shugaban ƙasa Bola Tinubu tare da girmamawa ya cire mana wannan kwamishinan daga jiharmu'', in ji gwamnan na jihar Kano.

Haka kuma gwamnan ya ƙara da cewa zai rubuta ƙorafi a madadin gwamnati da al'ummar Kano zuwa ga shugaban ƙasa ta hanyar ofishin bai ba shi shawara kan harkokin tsaro.

Me ya janyo saɓanin?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da alama batun janye ƴansanda daga faretin ranar ƴancin kai ba shi ne dalili ɗaya tilo da har ya sa gwamnan neman a sauya masa gwamnan, kamar yadda masana suke gani.

"Daga jin maganganun za ka fahimci cewa ba daga jiya ba kuma ko da daga jiya ta fara to ba lallai ta ƙare a iya jiyan ba, duk da dai ni ma idan ka tambaye ni zan ce maka kamata gwamna ya rubuta ƙorafi a hukumance ba faɗa a bainar jama'a ba. Lallai wasu abubuwan sun faru kafin yanzu." In ji Barista Abba Hikima.

Masana da dama musamman masu lura da al'amuran siyasa suna ganin akwai siyasa a saɓanin kasancewar ba wannan ne kwamishinan ƴansanda na farko da ke samun saɓani da gwamnan ba.

Ko a baya-bayan nan sai da aka samu sa-in-sa da kwamishinan ƴansandan jihar da ɓangaren gwamnati kan taron Mauludi da aka yi a Kano, inda ƴansandan suka ce ba za a yi ba saboda matsalar tsaro amma gwamna ya ce sai an yi.

Kafin nan ma an samu irin wannan karo tsakanin ɓangarorin biyu tun bayan cire Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da maye gurbinsa da Sarkin Kano na 14 Muhammad Sanusi II da gwamnatin Abba Kabir ta yi.

Hakan ya janyo kin bin umarnin gwamnan a lokuta da dama tare da aiwatar da abubuwan da rundunar ta samu umarnin aiwatarwa daga gwamnatin tarayya.

Har kawo yanzu dai rundunar ta ƴansanda ta jihar Kano ba ta ce uffan ba dangane da kalaman da gwamnan na Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi.

Wace illa saɓanin ke yi kan Kano?

Abu ne a fili cewa rikici da rashin fahimta tsakanin gwamnan jiha da rundunar ƴansandan jihar kasancewar shi gwamna shi ne shugaban tsaro na jihar,inda shi kuma kwamishinan ƴansanda shi ne shugaban masu ɗamara da ke samar da tsaro a jihar, a lokaci guda.

Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya masu fama da matsalar tsaro da na zamantakewa kamar ayyukan dabanci da shaye-shaye da ƙwacen waya sakamakon rashin ayyukan yi da sauran su.

"Akwai buƙatar samun zaman lafiya tsakanin gwamnati da ƴansanda domin tsamun dangantaka da ke tsakaninsu ba zai haifar wa Kano masalaha ba. Ka da ka manta jihar Kano na fama da matsalar dabanci da shaye-shaye."

"To idan gwamna da kwamishinan ƴansanda ba sa jituwa ta yaya za a yi aiki tare wajen warware waɗannan matsaloli. Dole ne a samu shirya. Dole ne su samu jituwa," in ji Barista Abba Hikima.

Mafita

Barista Abba Hikima ya ce dole ne a samun zamantakewa shiri tsakanin gwamnan Kano da kwamishinan ƴansandan jihar domin warware matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

"Idan ka duba tsarin mulkin Najeriya sashi na 212 zuwa da 16 duk ya yi waɗannan bayanan, inda ƴansanda musamman kwmaishinan yana da nauyi a kansa na karɓar umarni daga gwamnan garinsa, duk da cewa idan umarnin gwamna ya ci karo da na Sifeto Janar to yanzu kuma kwamishina umarnin IG zai bi. Shi kuma Sifeto Janar yana karɓar umarni kai tsaye daga shugaban ƙasa."

"To idan shiryawa ba za ta yiwuwa ba to sai a sauya kwamishinan na ƴansanda a kai shi wani wurin sai a kawo wani da za su zauna lafiya. Shi kwamishina za a iya sauya shi amma gwamna ba zai sauyu ba tunda shi ne gwamna har sai idan wa'adinsa ya ƙare." In ji Abba Hikima.