Yadda limaman coci ke cusa tsoro ga mabiya kan zaben Brazil

Asalin hoton, EVARISTO SA/AFP/Getty Images
Ana tana cikin cocin evangelical a garinsu da ke yankin Arewa maso gabashin Brazil lokacin da limamin cocin ya fara wa'azi.
Sakon limamin ya mayar da hankali ne a kan wata aya daya sananniya: " Sai dai da farko, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinSa, za a kuwa ba ku dukkan waɗannan abubuwa.'' (Mattiyu 6:33)
To amma kuma fassararsa a nan ta bambanta, inda yake cewa.
"Ya ce dole ne mu kare daular Ubangiji ta hanyar zaben dan takarar da ba zai rufe dukkanin majami'u a kasar ba'', in ji Ana.
A ranar Lahadin nan 30 ga watan Oktoba 2022 'yan Brazil za su zabi sabon shugaban kasarsu.
Zabin da suke da shi tsakanin shugaba mai-ci ne Jair Bolsonaro da kuma tsohon shugaban kasar Luiz Inácio Lula da Silva.
Ba wani daga cikin 'yan takarar da ya furta cewa zai rufe coci-coci, to amma Bolsonaro ya yi zargin cewa Lula zai rufe majami'un idan aka zabe shi. Kuma magoya bayan shugaban mai-ci na ta yada labarin na karya.
Sakon da ake ta yadawa a cikin cocin na Ana a bayyane yake, wanda shi ne : A zabi Bolsonaro.
A cikin alhini take cewa , ''Ina cike da damuwa da fargaba. Ina son in tashi na tafi. Na yanke shawarar komawa ne kawai bayan zabe.''
Mun sauya sunanta saboda ba ta son a gane ta domin kada a tuhume ta a cocin.

Asalin hoton, Buda Mendes/Getty Images
Irin bayanan da Ana ta bayar kusan irin su ne ke faruwa a gaba dayan cocin darikar Ibanjilika a kasar ta Brazil, inda ake zargin limaman cocin da yada bayanan karya da nufin canja musu ra'ayinsu na siyasa a kan zaben.
Mabiya darikar Ibanjilika
Yawancin 'yan Brazil mabiya darikar Katolika ne to amma tun shekarun 1950 mabiya darikar Ibanjilika sun samu shiga inda ake samun mabiya cocin musamman a tsakanin bakaken fata da mata da kuma talakawa.
Da wannan a yanzu kusan daya bisa uku na yawan al'ummar kasar mabiya darikar Ibanjilika ne.
Ana daukarsu a matsayin wadanda suka fi mu'amulla da al'ummominsu kuma suna kara samun tasiri a siyasa, inda bincike ya nuna cewa kashi 20 cikin dari na 'yan majalisar wakilan kasar mabiya darikar ne kuma sun yi wani gungu mai tasiri sosai a majalisar.
Dukkanin 'yan takarar shugaban kasar biyu wadanda 'yan Katolika ne, suna ta kokarin zawarcin 'yan Ibanjilikar sosai.
ganin sun samu kuri'un sun karkata ga yada bayanan karya na batanci ga juna a yakin neman zaben nasu.
Wulakanta addini
Cocin darikar Ibanjilika da dama suna da manyan allunan talabijin da suke nuna ayoyin bebul idan suna wa'azi.
Yanzu kuma ana amfanin da wadannan alluna wajen nuna hotunan bidiyo na labaran karya na farfagandar siyasa.
A irin wannan salon ne aka sanya wani hoton bidiyo a cocin da Patricia ke zuwa, a jihar Minas Gerais da ke kudu maso gabashin Brazil, wanda a cikinsa ake ikirarin Lula na cewa shedan ya karbe iko da shi.
Hoton bidiyon wanda na bogi ne da kuma aka yada shi ta shafukan intanet an harhada shi ne aka tashi maganar.

Asalin hoton, Ricardo Stuckert
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun a 1996 Patricia take aikin sa-kai a cocin amma ta bari a mako biyun da ya gabat saboda abin da take gani ana yi dangane da zaben.
Ita ma a nan an sauya sunanta ne domin kare ta.
Ta ce limaman cocin suna ta yada hoton bidiyon ta shafukan WhatsApp, inda masu aikin sa-kai da masu wa'azi ke tsara ayyukansu.
''Sun gaya mana cewa mu yada bidiyon ta yadda zai karade ko'ina ko kuma mu dauka cewa ba ma tare da Ubangiji'' in ji ta.
Wasu sakonnin na karya da ake yadawa kuma su ne cewa gwamnatin masu ra'ayin kawo sauyi (ta Lula) za ta bayar da damar zubar da ciki, abin da yanzu yana da tsauri a kasar.
Da cewa gwamnatin za a samar da ban-daki na yara maza da mata tare sannan kuma za ta bayar da dama ga masu neman jinsi daya wato 'yan luwadi da madigo a kasar.
Dukkanin wadannan batutuwa ana nuna cewa sun shafi mabiya darikar Ibanjilika.
Patricia ta ce, ''Abin yana ba ni takaici sosai. Limaman coci na yada tsoro daga kan mumbari. Suna muzanta addini.''
Masu bincike na kiran halin da ake ciki ''tsunamin labaran karya ta intanet da kuma ta haka, in ji masaniya a kan harkokin siyasa, Ana Carolina Evangelista, ta Cibiyar Nazarin Addini ta Brazil.
Yawancin labaran da ake yadawa sun ta'allaka ne kan sanya tsoro na rasa 'yancin addini da kuma bata tarbiyya.
A da Mario Henrique de Souza soja ne, amma yanzu lauya ne a kudancin Brazil: "Tun ina shekara 18 yana dan darikar Ibanjilika. A duk lokacin zabe ana irin wannan farfaganda, amma ba ta yi wannan muni ba."
Yanzu kuma, ya ce a coci ya ji ana cewa idan su Lula suka ci zabe za su kwace gidaje kuma a makaranta za a koya wa kananan yara 'yan shekara shida yadda ake jima'i.
Evangelista, ta ce karerayin da ake yadawa a coci-coci da ke sanya fargaba wani lokacin na gaske ne.
"Rayuwa ta yi tsanani a Brazil, wanda ta haka abu ne mai sauki a cusa tsoro a zukatan jama'a.
Har yanzu 'yan darikar Ibanjilika tsiraru ne a kasar, kuma ko da su ne suka fi yawa a cikin marassa rinjaye, da suka yi amanna a baya ana danne musu hakkin addini.

Asalin hoton, Personal archive
Masaniyar ta yi amanna cewa shigar da yakin neman zabe a coci ya yi tasiri sosai wajen sauya wa mutane ra'ayi.
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa lamarin wanda ya samo asali daga mabiya darikar Ibanjilika ya raba kan mabiya cocin, inda a watan Mayu bincike ya nuna cewwa kashi 47 cikin dari na mabiyan za su zabi Bolsonaro, yayin da kashi 45 cikin dari za su zabi Lula.
Bayan wata biyar kuma a tsakiyar watan Oktoba sai binciken ya nuna cewa kashi 65 cikin dari na mabiya darikar Ibanjilikar sun nuna cewa za su zabi Bolsonaro yayin da kashi 31 cikin dari kuma sun karkata ne ga Lula.
'Kungiyar asiri'
Bayan zagayen farko na zaben masu yakin neman zaben Lula sun mayar da martani ta shafukan intanet karkashin jagorancin wani dan majalisar dokokin kasar mabiyin darikar Ibanjilika mai suna André Janones.
Ya bukaci mabiya Lula da su rama wa kura aniyarta, su sa Bolsonaro ya girbi abin da ya shuka.
Wasu sun yi kamar yadda aka ce su yi.
Daga nan aka ga wani hoton bidiyo ya bayyana a shafukan intanet, wanda a ciki Bolsonaro yake magana a wani wurin bauta na mabiya kungiyar asiri ta Freemason a 2017, abin da ke nuna shi a matsayin mai alaka da kungiyar.
Kiristoci da dama suna ganin kungiyar asirin ta Freemason ta saba da akidunsu na addini.
Hoton bidiyon ya yadu kamar wutar-daji.
Bolsonaro ya tabbatar cewa ya je wannan wuri na 'yan kungiyar amma ya ce ya yi hakan ne saboda shi shugaban kasa ne na kowa.
Daga nan sai wannan dan majalsai jigon yakin neman zabe na farfaganda na Lula ya hada wani bidiyo a gaban wani babban taro na mabiya darikar Ibanjilika a São Paulo, inda a ciki yake ankarar da jama'a cewa Bolsonaro ya kulla yarjejeniya da 'yan kungiyar Freemason domin ya ci zabe.











