Larurar da ke sa mutane aikata mummunan abu cikin barci

.

Asalin hoton, Getty Images

A ilimin kula da lafiya, larurar da ake kira 'Parasomnia' da Ingilishi wani nau'i ne na matsalar barci da mutum yake tsintar kansa a yanayin aikata wasu abubuwa saɓanin na hankali a lokacin da yake barci.

Larurar na iya sa mutum ya rika tafiya ko maganganu ko fitsarin kwance ko mugun mafarki ko ƙiƙƙifta ido ko yi wa kansa lahani, da dai sauran abubuwa na daban a lokacin da yake barcin.

A lokacin da mutum yake cikin wannan hali wasu da ke tare da shi ko kusa da shi za su ga kamar ba barci yake ba yana farke ne, to amma yana cikin yanayi ne na barci bai san abin da yake yi ba.

Mutanen da ke cikin wannan yanayi ba ma sa iya tuna abin da ya faru da su ko abin da suka aikata a lokacin da suke cikin halin.

Bincike ya nuna cewa abin da mutum kan yi a wannan lokacin kamar yana aikata abin da mafarkinsa ya kunsa ne a zahiri.

Kuma wannan larura na iya faruwa kafin ko kuma yayin barci.

Bayanai sun nuna yadda wani mutum ya yanke marenansa a cikin barci, yayin da wani kuma ya ji targade a dukkan yatsunsa na kafa yayin da ya yi mafarkin cewa yana buga fenareti na wasan kwallon kafa.

Wasu labarai da za ku so ku karanta:

.

Asalin hoton, Getty Images

A cewar Dakta Dayyiba Shu'aibu, wata likita mai kula da masu matsalar ƙwaƙwalwa da barci a Abuja, larurar 'parasomnia' ɗaya ce daga cikin matsalolin barci sai dai duk mai fama da wannan matsala na shiga wani yanayi na aikata abu cikin barci.

Shi kuwa Dakta Aminu Ibrahim da ke aiki a sashen kula da lafiyar ƙwaƙwalwa a asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke birnin Kano a Najeriya, ya bayyana parasomnia a matsayin "ciwon magagin barci.''

Ya ce larurar na iya zama ciwo idan ta kasance tana faruwa kullum kuma idan ta takura wa mutum "don wadansu abin na faruwa da su daga lokaci zuwa lokaci amma abin da ya sa ba a ganewa ciwo ne, saboda ana alaƙanta shi da mutanen ɓoye, musamman a ƙasashe masu tasowa."

Ya ba da misali da matsalar dannau inda mutum cikin barci zai ji kamar an ɗora masa dutse a ƙirji. "Dannau ba lalle ba ne ya zama ciwo saboda abu ne da zai iya faruwa da kowa, idan ya kasance kullum mutum yana samu, to ciwo ne."

Abin da ke janyo matsalar 'Parasomnia'

Dakta Dayyiba ta ce akwai abubuwa da dama da suke haifar da wannan matsala sai dai ta ce ana iya gadon larurar.

"Akwai waɗanda suke faruwa saboda magunguna da mutum ke sha ko kuma wasu cututtuka ko shaye-shaye,” in ji Dr Dayyiba.

Alamomin larurar

Likitar ta bayyana cewa larurar ta bambanta daga mutum zuwa mutum saboda "su waɗanda suke da matsalar, ba sa sanin abin da suke yi, waɗanda suke kwana tare ne suke faɗa musu - ko a ce suna yawan magana a cikin barci, ko su tashi suna yawo a cikin barci, ko su ci abinci a cikin barci, wasu ma sai ka ji an ce suna aikata abubuwa kamar suna jima'i a cikin barci idan sun tashi daga baya aka faɗa musu ba za su tuna cewa sun aikata waɗan nan abubuwa ba".

Sai dai Dr Aminu Ibrahim ya bayyana cewa "barci gaba ɗaya daga ƙwaƙwalwar bil adama yake, farkawa da barci na mutum ne - ya danganta da ƙwaƙwalwar.

Ya ƙara da cewa babbar alamar wannan larura ita ce yin wani abu da bai kamata ka yi shi ba lolacin da kake barci.

Su wa larurar ta fi shafa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar Dr Ibrahim, ciwon yana shafar kowa sai dai an fi ganinsa a ƙananan yara.

"Mutane da dama sun san cewa idan an tashi yara daga barci, ya kan tashi yana magagi, zai tashi kamar bai san abin da yake ba - idan ka yi masa magana ba zai amsa ba. Idan kuma ya tashi yana iya tafiya ya zazzaga har ya fita daga gida, tafiya suke yi ba su san inda suke tafiya ba saboda barci suke, bayan lokacin da suka dawo, ba za su san me suka yi ba." in ji shi.

Akwai kuma masu yin maganganu mara ma'ana lokacin da yake barci.

Likitan ya ce mutum ya kan iya tashi a firgice, a gigice, yana kuma iya zabura a guje ya fita ya yi wani wajen ko kuma ya zauna ya yi ta ihu, kuma idan ka yi masa magana bai san halin da yake ciki ba, bayan wannan yana iya komawa ya ci gaba da barcinsa.

A ɓangaren Dr Dayyiba, ta ce ciwon na samun kowa - mata, maza, yara, manya. A cewarta, babu alƙaluma da suka nuna rukunin mutanen da suka fi fama da ciwon.

Ta ce Parasomnia ba lalle tana faruwa ba ne kan abubuwan da mutum ya yi a lokacin da idonsa biyu inda ta ce "ba lalle abin da suka yi tunani kafin su yi barci, shi za su gani a cikin barci ba."

Ko ciwon na da magani?

Likitar ta ce da farko ana duba tarihin cutar domin a gano abin da yake haifar da ita. "Idan wani ciwon ne daban, sai an yi maganin wannan ciwon, idan wasu magunguna ne da suke haifar da wannan sai an canja waɗan nan magunguna, idan na wanda ba a samu ko me ke jawo shi ba, shawarar da ake badawa ita ce mutum ya tsayar da lokacin kwantawa barci da lokacin da zai tashi.

Dakta Dayyiba ta ce ciwon ba ya warkewa saboda "ciwon na katse barci ne."

Dakta Ibrahim ya bayyana cewa cutar tana da magani sai dai kafin a kai ga magani, a cewarsa, akwai canjin ɗabi'a da mutum zai yi a rayuwarsa kafin a kai ga shan magani.

Ya ce akwai dangantaka tsakanin wannan matsala da kuma wasu abubuwa da ke takura wa mutum a harkokinsa na rayuwa, akwai kuma rashin samun barci sosai.