Najeriya za ta karbi kashi na biyu na rigakafin korona

Jami'an lafiya a Najeriya sun ce su na sa ran karbar kusan rigakafin cutar korona miliyan hudu ta kamfanin AstraZeneca a karshen watan Yuli.
Za dai a karbi allurar ne karkashin shirin COVAX da ke tallafawa kasashe matalauta da ke Afurka samun yi wa al'umarsu kashi na biyu na rigakafin cutar ta korona.
Ana sa ran Najeriyar za ta kammala aikin yin kashi na farko na rigakafi miliyan hudu da aka bata zuwa karshen watan.
Kawo yanzu kashi 1 cikin 100 na al'ummar Najeriya ne aka yi wa kashin farko na rigakafin. Ita ma Najeriya kamar sauran kasashen Afurka da ke fama da matsalar karancin kayan aikin asibiti, za ta yi fadi tashin ganin an yi wa 'yan kasar rigakafin cutar.
A bangare guda gwamnat ta ce ta na shirin yi wa akalla kashi 70 cikin 100 na 'yan Najeriya da ke tsakanin shekara 18 allurar rigakafin korona nan da shekaru biyu masu zuwa.







