An yi garkuwa da babban jami'in gwamnatin Nassarawa

@

Asalin hoton, Getty Images

'Yan bindiga sun yi garkuwa da babban sakataren gwamantin jihar Nassarawa da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Maharan sun yi ta harbe-harbe a iska kafin su shiga gidan Jibrin Giza da ke Lafiya babban birnin jihar Nassawara da ke Arewacin Najeriya da misalin karfe 12:30 na dare.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Bola Longe ne ya tabbatar da faruwar hakan kuma ba su kai ga gano inda 'yan bindigar suka tafi da shi ba.

Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito kwamishinan 'yan sandan jihar na cewa jami'an rundunar sun kaddamar da bincike domin kamo wadanda suka yi garkuwa dababban jami'in gwamantin.

Jihar Nassarawa da ke yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya na cikin jihohin da ke da iyaka da birnin tarayyar kasar, Abuja kuma ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya.

Yawaitan ayyukan masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a jihohin da ke makwabtaka da Abuja na yawan jefa mazauna musamman matafiya cikin damuwa.

Sai dai ya zuwa wannan lokaci babu labarin ko an tuntunbi iyalan jami'in da kuma bayani game da inda yake.