Muna goyon bayan Gantz ne domin korar Netanyahu - Falasdinawa

Asalin hoton, Reuters
Larabawa 'yan majalisar kasar Isra'ila sun mara wa tsohon shugaban sojojin kasar Benny Gantz a kokarin da yake yi na kafa gwamnati.
Wannan na zuwa ne bayan da aka gudanar da zabe a makon jiya da bai samar da wanda ya lashe zaben kai tsaye ba.
Wannan ne karon farko tun shekarar 1992 da jam'iyyun siyasa na Larabawa ke mara wa wani dan takara wajen nemar kujerara Firai ministan kasar baya.
Shugabansu Ayman Odeh ya ce suna fatan ture Firai Minista Benjamin Netanyahu ne daga mukaminsa.
Wannan muhimmin mataki ne da Larabawan Isra'ila suka dauka a siyasance.
Shugaban kasar, Reuven Rivlin na tattauna wa da shugabannin dukkan jam'iyun siyasa kan mutumin da ya dace ya kira domin ya kafa gwamnati.

Asalin hoton, EPA
Jam'iyyun siyasa na Falasdinawa sun taka muhimmiyar rawa a zaben da aka gudanar.
A halin yanzu jam'iyun siyasa na Falasdinu sun kasance sune na uku a karfin iko a majalisar Isra'ila, kuma duk da cewa goyon bayan da za su bai wa Benny Gantz ba zai ba shi gagarumin rinjaye a majalisa ba, amma zai samu karfin gwiwa sosai.
Shugaban hadakar jam'iyyun siyasa na Larabawa, Ayman Odeh ya kuma bayyana cewa ba suna goyon bayan dukkan manufofin Mista Gantz ba ne, amma suna neman hana Mista Netanyahu sake darewa karagar mulkin kasar ne.
Ya kuma ce wannan matakin nasu zai sanar da kowa cewa dole ne wanda zai mulki kasar Isra'ila ya tabbatar da ana adalci ga 'yan kasar wadanda Larabawa 'yan Falasdinu ne.











