Na samu matsala da iyayena lokacin da na kai masu Baturiya da nufin aure - Soja boy
Latsa lasifikar da ke sama domin kallon tattaunawar BBC da mawaki Soja boy
Mawakin arewacin Najeriyar nan Usman Umar wanda aka fi sani da soja boy ya ce ya sha gwagwarmaya da 'yan uwansa lokacin da ya kai masu baturiya Lisa gida da nufin aurenta.
Ya ce ya samu rashin fahimta sosai tsakaninsa da 'yan uwa da kuma iyaye. Kuma soyayyarsa da ita kusan ta kasance kaddararriya kuma shi kadai ya san dalilin da ya sa yake sonta.
Mawakin wanda ya yi fice tsakanin matasa a arewacin Najeriya ya ce shi ɗan talaka ne kuma ya sha gwagwarmaya a rayuwa saboda talauci, kafin ya kai matsayin da ya ke a yanzu.
Soja boy kamar yada aka fi saninsa da shi, ya ce tun yana yaro yake son waka kuma bayan kammala sakandarensa ya shiga aikin soja, sai dai son harkar waka da fina-finai ta sa ya ajiye aikin.