Amurka ta gargaɗi ƴan ƙasarta mazauna Najeriya saboda zanga-zanga kashe Khamenei
Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya gargaɗi Amurkawa mazauna Najeriya da su yi taka-tsantsan wajen gudanar da harkokinsu, musamman a babban birnin tarayya Abuja saboda fargabar da ofishin yake ciki na yiwuwar ƙazancewar zanga-zanga.
Ofishin ya ce akwai yiwuwar rikiɗewar zanga-zangar nuna rashin jin daɗi kan kashe Ayatollahi Ali Khamenei a yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran.
Ofishin ya fitar da gargaɗin ne bayan mabiya Shi'a a ƙarƙashin ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) sun gudanar da zanga-zanga a jihohin Najeriya.
Ofishin ya buƙaci ƴan Amurka mazauna Najeriya da su kasance a cikin gida, "domin akwai yiwuwar zanga-zangar za ta ƙazance ta rikiɗe zuwa tarzoma a Abuja a ranar 4 ga watan Maris."