Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Neymar ya karya tahirin Pele na yawan cin kwallo a Brazil
Neymar ya karya tahirin Pele na yawan cin kwallo a Brazil, bayan ɗan wasan ya ci kwallo biyu a wasan da suka yi nasara kan Bolivia.
Dan wasan mai shekara 31 wanda ya je wasan share fagen gasar kofin duniya da kwallo 77 kamar, ya kuma zubar da bugun fenariti gabanin ya ci kwallo biyu a minti 45 na biyu a wasansa na 125 a ƙasar.
"Ban taba kawo wa zan iya haɗa wannan tarihi ba. Ban fi Pele ba ko wani ɗan wasa a tawagar Brazil ba," in ji Neymar.
Mata ta ce kwallo 122 a wasa 189 da ta bugawa tawagar Brazil ta mata.
Pele da ya mutu a watan Disamba a shekara 82 ya ci kwallo 77 a wasa 99 da ya buga tsakanin shekarun 1957 zuwa 1971.
Ana masa kallon ɗaya daga cikin kwallon da ba a taɓa yin irinsu ba a fagen sannan ƙwallon kafa a duniya.
Shafinsa na X ya yaba da wannan nasara da Neymar ya samu.
"Muna taya ka murna Neymar na karya tahirin Sarkin cin kwallo a Brazil. Babu shakka Pele na tafa maka a yau!" a cewar saƙon.
Kocin Brazil Fernando Diniz ya ce: Ya zo ya yi abin da zai iya ne: a yi farin ciki, ya ci kwallo biyu ya karya tarihi."
Neymar ya zama ɗan wasan da ya fi kowanne tsada a duniya lokacin da ya koma PSG daga Barcelona a 2017 inda aka saye shi kan kuɗi fan miliyan 200.
Ya bar ƙungiyar da Faransa a wannan kakar inda ya koma gasar Saudiyya zuwa ƙungiyar Al-Hilal.
"Ai babban ɗan wasa ne da mutane ke son gani," in ji Diniz.