Newscastle na son Guimaraes ya tsawaita kwataraginsa, Arsenal da Liverpool na son Nusa

An samu ci gaba a tattaunawar tsakanin Newcastle da ɗan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 25 kan tsawaita kwantaraginsa, sun kuma gama cimma duk wata yarjejeniya. (Fabrizio Romano)

Kungiyoyin Chelsea da Manchester City su ma sun nuna sha'warsu kan dan wasan na Newcastle Guimaraes, wanda kwantiraginsa da kungiyar za ta kare a 2026. (90 Min)

Rangers na duba yiwuwar dauko tsohon manajan Brighton da Chelsea Graham Potter a matsayin wanda zai maye gurbin manajan kungiyar na yanzu, Michael Beale. (Football Insider)

Arsenal da Liverpool na cikin kungiyoyin da ke zawarcin matashin dan wasan tsakiya na Norway, Antonio Nusa, mai shekara 18, wanda ya yi watsi da tayin Chelsea ana gab da rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa. (90min)

Tsohon ɗan wasan gaban Ingila, Andy Carroll, mai shekara 34, ya ce sai da aka yi masa tayin ci gaba da zama a Ingila amma sai ya yanke shawarar komawa League din Faransa. (Sun)

Dan wasan tsakiya na Chelsea Romeo Lavia, mai shekara 19, ya ji mummunann rauni a a idon sawunsa lokacin atisaye, kuma kungiyar na jiran sakamakon hoton kashi da aka yi masa, domin sanin tsayin jinyar da dan wasan na Belgium zai yi. (Guardian)

Dan wasan tsakiya na Ingila, Jadon Sancho, mai shekara 23, na tsaka mai wuya, domin samun goyon bayan 'yan wasa da manajan kulub din Erik ten Hag, sakamakon matakin da ya dauka lokacin da ya ke cikin fushi kan ajiye shi da aka yi a wasan Arsenal. (ESPN)

Manchester City ta tuntubi Barcelona kan yiwuwar daukar dan wasan baya na gefe Alejandro Balde, mai shekara 19. (Fabrizio Romano, via Sport - in Spanish)

Tsohon ɗan wasan gaban kungiyoyin Sifaniya da Real Madrid, Raul na duba yiwuwar samun mukamin manajan kuniyar Villarreal, bayan korar manaja Quique Setien sakamakon rashin tabuka abin azo a gani a kakar wasan nan. (Marca - in Spanish)