Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An saukaka wa Chelsea haramcin sayen 'yan wasa
Chelsea ta samu damar sayen 'yan wasa a watan Janairu mai zuwa bayan kotun sauraron kararrakin wasanni ta rage tsawon haramcin da aka yi mata sakamakon daukaka karar da ta yi.
Fifa ta haramta wa kungiyar sayen 'yan wasa ne na tsawon kakar wasa biyu a watan Fabarairu sakamakon saba doka game da sayen matasan 'yan wasa.
Kotun ta sassauta haramcin zuwa kakar wasa guda daya, wadda kuma tuni Chelsea ta shafe ta a baya.
Kazalika, ta rage yawan tarar kudin da aka ci kulob din daga 600,000 zuwa 300,000 (kudin kasar Switzerland), kimanin sama da naira miliyan 100.
An kakaba wa Chelsea wannan takunkumi ne sakamakon kama ta da laifi 150 game da sayen 'yan wasa 69 na karamar kungiyarta a lokuta daban-daban, kamar yadda Fifa ta wallafa.