Bakanon da ke koya wa yara tseren keke a Afirka Ta Kudu
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wannan mutumin ɗan asalin jihar Kano ne da ke Najeriya, kuma matuƙin jirgin sama ne a ƙasar Afirka Ta Kudu, amma ya kan ware lokaci domin koya wa mutane tsere keke.
Tuni dai ya yi fice a wannan harka. Kuma a wannan bidiyo za ku ji yadda ya fara ta da yadda take ci gaba.