Lafiya Zinariya: Yadda ake kare kai da yara daga cutar kyandar biri

Bayanan sautiLafiya Zinariya: Yadda ake kare kai da yara daga cutar kyandar biri

Danna hoton da ke sama don sauraron shirin:

A Najeriya yayin da aka samu bullar cutar kyandar biri, masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana wasu hanyoyi na kaucewa kamuwa daga cutar, musamman a tsakanin kananan yara.

Cutar wadda asalinta ana kamuwa da ita ne daga dabbobin daji, amma tana bazuwa a tsakanin mutane, kuma tafi tsanani a tsakanin yara.

Sai dai kamar sauran cutar virus, ita cutar kyandar biri bata da magani.

Wasu daga cikin hanyoyin kaucewa cutar sun hada da kaucewa mu'amala da dabbobin daji wadanda ke dauke da cutar.

Haka kuma tsaftar jiki, musamman wanke hannu da killace wanda ya kamu da cutar su ma hanyoyi ne na kare kai da kuma kananan yara.

Alamomin cutar sun hada da zazzabi mai zafi da mura da ciwon kai da gajiya da fesowar kuraje.

Sannan akwai ciwon jiki da ciwon baya da kuma matukar gajiya.

Ana iya daukar cutar ta hanyar duk wani ruwa dake fita daga jikin dabba mai dauke da kwayar cutar, ko mutumin da ya kamu da cutar ta kyandar biri.

A cewar hukumar lafiya ta duniya, WHO cutar kala biyu ce ake da ita a duniya, kuma sun samo asali daga yammaci da tsakiyar Afrika.

Ta tsakiyar Afrika ta fi muni, inda ake samun yiwuwar mutuwa kashi goma cikin dari na wadanda suka kamu da ita.

Yayin da kuma ta yammacin Afrika kashi ya ne cikin dari.