Abin da majalisar dattawan Najeriya ta ce kan harin jirgin ƙasa a Kaduna

Bayanan bidiyo, Abin da majalisar dattawan Najeriya ta ce kan harin jirgin ƙasa a Kaduna

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci sojojin kasar su yi amfani da kayan fadan da gwamnati ta samar musu wajen yin luguden-wuta a kan maharan da ke addabar al`umma a shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Ƴan majalisar sun yi Allah wadai da harin da `yan bindiga suka kai kan jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, suna cewa ya kamata jami`an tsaro su gaggauta daukar matakin murkushe maharan.

Senata Uba Sani shi ne ya gabatar da kudurin, ga kuma karin bayanin da ya yi wa Ibrahim Isa: