Ku San Malamanku tare da Malam Muhammadu Ɗan-Lami Basakkwace
Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Malam Muhammad Muhammad Basakkwace, wanda aka fi sani da Muhammadu Ɗanlami.
An haifi malamin a unguwar Tudunwada da ke cikin garin Gombe a shekarar 1973.
Ya fara karatunsa na Ƙur'ani a wajen mahaifinsa kafin daga bisani ya kai shi garin Darazo na Jihar Bauchi wajen Malam Muhammadu Sabo, wanda aka fi sani da Yaya Babba.
Daga baya mahaifin malamin ya kai shi garin Kano kuma ya sauka a gidan jagoran Ɗariƙar Ƙadiriyya Sheikh Nasiru Kabara.
An danƙa Muhammadu Ɗanlami a hannun Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara, wanda a hannunsa ya samu ilimin tafisirin Ƙur'ani.
Haka nan, ya yi karatu a wajen Sheikh Musa Ƙasiwini Nasiru Kabara. Yanzu haka shi ne shugaban Ɗariƙar Ƙadiriyya a Gombe.
Malam yana da mata uku ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto. 'Ya'yansa 15 - maza bakwai da mata takwas.