BBC Hausa ta zama madogarar samun labarai a duniyar Hausawa
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Shugaban sashen Hausa na BBC Aliyu Tanko ya ce BBC Hausa ta zama madogarar samun labarai a duniyar Hausawa.
Ya fadi hakan ne albarkacin bikin cikar sashen shekara 65 da kafuwa.
An kafa sashen Hausa na BBC ne ranar 13 ga watan Maris din 1957.
Aliyu Tanko ya ce duk da dai ba za a yi wani gagarumin biki a yanzu ba, amma nan da watan Mayu za a hada bikin shekara 65 din da na bude sabon ofishin BBc Hausa a Abuja.
Ana sa ran shugaban Najeriya da na Nijar za su halarci bikin a lokacin.