BBCHausa@65: Rayuwa a lokaci da bayan aiki da BBC Hausa - Nasir Zahraddeen

Bayanan bidiyo, BBCHausa@65: Rayuwa a lokacin da bayan aiki da BBC Hausa - Nasir Zahraddeen

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A yayin da BBC Hausa ke cika shekara 65 da kafuwa ranar 13 ga watan Maris, sashen zai dinga kawo muku hirarraki da tsofaffin ma'aikatansa.

Za a fara wallafa jerin hirarrakin ranar Talata 1 ga watan Maris na shekarar 2022.

Tsofafin ma'aikatan sun yi bayanai ne a kan yadda suka samu aikin BBC da yadda ya kasance musu, da rayuwa bayan sun bar aikin da dai wasu abubuwan da suka shafe su.

A yau za mu gabatar muku da hira ne da tsohon ma'aikacinmu Nasir Zahraddeen, wanda tsohon mai taimakawa na musamman ne ga shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.