Za a maka Najeriya a kotu kan yanke wa Nijar lantarki

Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Mukhtar Adamu Bawa, A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Sai da safenku

    Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Muna nan tafe da wasu sababbin rahotannin daga sassan duniya gobe da safe.

    Kafin goben, ku duba ƙasa domin karanta waɗanda muka kawo a yau Juma'a.

    Umar Mikail ne ke cewa mu zama lafiya.

  2. Kotu a Turkiyya ta ɗaure ɗan crypto shekara 11,196 a gidan yari

    Faruk Fatih Ozer

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotu a Turkiyya ta kama wani matashi da laifin zambatar masu zuba jari a kamfaninsa na kuɗin intanet da aka fi sani da cryptocurrency.

    Kotun ta yanke wa Faruk Fatih Ozer tare da mutum biyu hukuncin ɗaurin shekara 11,196 a gidan yari.

    Tun da farko masu shigar da ƙara sun nemi a yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 40,562, kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.

    Faruk mai shekara 29 ya gudu Albaniya a 2021 da kadarorin masu zuba jarin bayan dandalin canjin kuɗin da ya kafa na Thodex ya daina aiki bagatatan.

    An mayar da shi Turkiyya a watan Yuni kuma aka kama shi da laifin halasta kuɗin haram, da zamba, da kuma aikata shiryayyun laifuka.

    Ozer ya faɗa wa kotun cewa ba "zai aikata irin wannan yarintar ba" da a ce yana da niyyar cutar mutane tun da farko, a cewar kafar yaɗa labaran Turkiyya.

    Kazalika, kotun ta kama yar uwarsa Serap da ɗan uwansa Guven da aikata irin laifukan.

  3. Kotu ta bai wa Abubakar Kusada kujerar majalisar wakilai a Katsina

    Abubakar Kusada

    Asalin hoton, Facebook/Abubakar Kusada

    Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen 'yan majalisar tarayya a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta soke zaɓen Dalha Ismail Kusada a matsayin ɗan majalisar wakilai.

    A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a O. Ogunfowora ta ce Abubakar Yahaya Kusada na APC ne ya lashe zaɓen na watan Fabrairu.

    Haka nan, alƙalan sun ayyana Abubakar a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓun Kankia/Ingawa/Kusada.

    Kazalika, kotun ta umarci Dalha da hukumar zaɓe ta Inec - waɗanda ake ƙara - su biya Abubakar kuɗi naira 200,000.

    Da ma Abubakar ne ke riƙe da kujerar kafin Inec ta sanar da kayen da ya sha jim kaɗan kammala zaɓen, kuma tsohon kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina.

    Sai dai har yanzu Dalha Kusada na da damar ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.

  4. Kotu ta bai wa tsohon Gwamnan Binuwai Suswan nasarar zaɓen sanata

    Gabriel Suswan

    Asalin hoton, Twitter

    Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen majalisar tarayya a jihar Binuwai ta ayyana Gabriel Suswan na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanata a mazaɓar Binuwai ta Arewa.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta yanke hukuncin ne bayan zama na awa uku, inda ta ƙwace nasarar da Emmanuel Udende na APC ya yi a zaɓen na watan Fabrairu.

    Mista Suswan, wanda tsohon gwamnan jihar ta Binuwai ne, ya garzaya kotun yana ƙorafin cewa Udende bai ci ƙuri'u mafiya yawa da aka kaɗa a zaɓen ba.

    Tawagar alƙalai uku ƙarƙashin Mai Shari'a Ory Zik-Ikeorha ta amince da ƙorafin na Suswan da PDP bayan sauraron shaidu da kuma kariya daga APC.

  5. Wace ƙungiya ce G20 kuma me ya sa take da muhimmanci?

  6. An sake kai wa sojojin Mali hari bayan kashe mutum 60

    Mali

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojan Mali ta sake fuskantar hare-hare a sansanoninta kwana ɗaya bayan masu iƙirarin jihadi sun kashe fiye da mutum 60.

    Rundunar ta ce an kai wa wani ɓangare na filin jirgin saman soja hari, amma ba ta bayar da ƙarin bayani ba.

    Hukumomi sun ɗora wa ƙungiyoyi masu alaƙa da al-Qaeda alhakin harin na ranar Alhamis.

    Mazauna yankin sun faɗa wa BBC cewa kwalekwalen ya bar Gao zuwa Mofti a tsakiyar Mali lokacin da aka kai masa harin a Bamba.

    Wasu daga cikin fasinjoji sun afka ruwa don tsira da rayuwarsu amma kuma suka nitse.

    Kazalika, maharan sun shiga wani sansanin soja, inda suka kashe dakaru 15, amma rundunar sojan ta ce ta kashe 'yan bindigar 50.

  7. Rikici ya raunata Falasɗinawa 20 a Lebanon

    Ain al-Helweh

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon rikici ya ɓarke a sansanin Falasdinawa da ke Lebanon, wurin da aka kashe mutum 13 a wani tashin hankali a watan Yuli.

    Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya rawaito cewa aƙalla mutum 20 ne suka jikkata sakamakon faɗan da aka gwabza tsakanin bangarorin da ke gaba da juna ranar Alhamis a sansanin Ain al-Helweh da ke wajen Sidon.

    Mutane da dama dai sun tsere daga yankin a sansanin da fada ya fi kamari.

  8. Ukraine ta yi watsi da zaɓen da Rasha ta shirya a yankunanta

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    An nemi mazauna yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye da su kaɗa ƙuri'a a zaɓen da mahukunta ke cewa zaɓen ƙanananan hukumomi.

    Ministan harkokin wajen Ukraine ya siffanta zaɓen da "na boge", yana mai cewa ƙuri'ar ba ta da wani matsayi a idon doka.

    Dukkan 'yan takara 'yan Rasha ne ko kuma magoya bayanta, kuma sun haɗa da gwamnonin da Rasha ta tsayar takara.

    Da yawa daga cikin waɗanda suka kaɗa ƙuri'a da wuri sun yi hakan ne a kan idon dakarun Rasha ɗauke da makamai.

    Hukumomin Ukraine na cewa duk ɗan ƙasar da aka kama da hannu wajen shirya zaɓukan za a hukunta su.

    Cibiyar Council of Europe mai kare haƙƙi ta yi watsi da zaɓen a wuraren da "Rasha ta ƙwace da ƙarfi ba bisa doka ba", tana mai cewa ya saɓa da dokokin ƙasa da ƙasa.

  9. 'Shinkafa ta yi tsadar da ba a taɓa gani ba cikin shekara 15 a Indiya'

    Rice

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Abinci da Noma ta Duniya (FAO) ta ce farashin shinkafa a duniya ya kai matsayin da bai taɓa kaiwa ba cikin shekara 15 a watan Agusta.

    Hauhawar farashin ya faru ne bayan Indiya, wadda ta fi kowa fitar da shinkafar a duniya, ta haramta sayar da shinkafar zuwa wasu ƙasashe.

    A yayin da farashin kayan abinci ya sauka a watan Agusta, farashin shinkafa ya ƙaru da kashi 9.8 idan aka kwatanta da watan Yuli.

    FAO ya ce hakan ba ya rasa nasaba da haramta fitar da shinkafar da Indiya ta yi.

    Shinkafa ce babban abincin da aka fi ci a duniya, kuma farashinta ya tashi tun bayan ɓullar annobar Korona da ɓarkewar yaƙin Ukraine.

    A watan Yuli ne Indiya ta sanar da haramta fitar da shinkafar da ba basmati ba, wadda ta kai kusan kashi ɗaya cikin huɗu na adadin shinkafar da ƙasar ke fitarwa

    Ma'aikatar abinci ta ƙasar ta ce an ɗauki matakin ne domin magance ƙarancin shinkafar da saukar da farashinta a cikin ƙasar.

  10. Masu fafutuka za su maka Najeriya a kotu kan yanke wa Nijar wuta

    s

    Asalin hoton, Nigerian Electricity

    Ƙungiyoyin fararen hula a Nijar na CODDAE da ke fafutukar kare hakin jama'a a fanin makamashi sun yi barazanar kai karar Najeriya a gaban kotu kan yadda ta yanke wa ƙasar wuta lantarki.

    Ƙungiyoyin sun ce Najeriya ta karya yarjejeniyar da ke tsakaninta da Nijar.

    Alh Mustapha Kadi shi ne shugaban ƙungiyar CODDAE, ya kuma shaida wa Tchima Illa Issoufou cewa dole ne Nijeriya ta biya hakkin 'yan Nijar:

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton:
  11. Gwamnatin Zamfara ta buƙaci jami'an tsaro su fara sintiri a manyan titunan jihar

    n

    Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ɗauki matakin shirya jami'an tsaro da za su riƙa sintiri a kan manyan titunan jihar.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce za a girke jami'an tsaron domin sintiri a kan hanyar Gusau zuwa Funtua da Magami zuwa Dangulbi zuwa Dan Kurmi da wasu tinunan da ake samun barazanar tsaro a jihar.

    A taron majalisar tsaron jihar na baya-bayan nan da gwamnan jihar Dauda Lawan Dare ya koka wa shugabannin jami'an tsaro da ke jihar kan ayyukan 'yan fashi a wasu manyan titunan jihar, ɗaya daga cikin dabarun da gwamnan ya ɗauka domin magance matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.

    Sanarwar ta ƙara da cewa jami'an tsaron da za su yi sintiri a kan titunan sun haɗar da sojojin ƙasa da na sama.

    Haka kuma sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta ce ta kammala shirye-shirye domin fara ɗauka tare da horas da 'yan sa kai a jihar.

  12. 'Najeriya ta samu gagarumar nasara wajen gano masu tarin-fuka'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa ƙasar ta samu gagarumin ci gaba wajen aiwatar da matsayar babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2018 kan yaki da cutar tarin-fuka (TB) a Najeriya.

    Dakta Chukwuma Anyaike, Daraktan kiwon lafiyar jama’a na ma'aikatar ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da masu ruwa da tsaki kan cutar tarin fuka a Abuja.

    Cutar ta TB na ci gaba da zama wani babban kalubale a fannin kiwon lafiyar al’umma a Najeriya, inda kasar ke cikin jerin kasashe 10 na duniya da ke fama da matsalar tarin fuka.

    Dakta Anyaike, wanda Dr. Urhioke Ochuko ya wakilta, ya bayyana cewa adadin waɗanda suka kamu da cutar tarin fuka kuma da aka yi wa magani sun ƙaru a Najeriya.

    “Mun gano karin mutane sama 285,000 da suka kamu da cutar, sannan an cimma kashi 60 cikin 100 na burin da aka sa gaba wajen gano masu dauke da cutar a shekarar ta 2022,” in ji shi.

    Bugu da kari, Najeriya ta yi kokarin karfafa tsarin kiwon lafiyarta, ta hanyar horar da ma'aikatan kiwon lafiya da kafa karin cibiyoyin kula da masu dauke da cutar tarin fuka.

    Ya kara da cewa "Rigakafin cutar tarin fuka ya kuma inganta tun daga 2018."

    Ya ce gwamnati ta nuna himma a siyasance don magance tarin fuka kuma ta kara yawan kudade tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa.

    Duk da haka, Dr. Anyaike ya lissafo ƙalubalen da ake fuskanta da suka haɗa da rashin isassun kuɗi da ƙarancin gano masu cutar tarin fuka cikin yara, da rashin isassun rajistar masu fama da cutar.

    Ya bukaci mahalarta taron da su nemo wata damar da za a kara zuba jari a fannin maganin tarin fuka da sabbin dabarun samar da kudade don bayar da tallafi kan cutar ta tarin fuka.

    • WHO ta yi gargaɗi kan wani maganin tari na Indiya mai illa ga bil'adama
    • Za a samar da maganin HIV mai ɗanɗanon inibi ga yara a Afirka
  13. Amurka ta sauya wa dakarunta matsuguni a Nijar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Gwamnatin Amurka ta dauki matakin sauya wa dakarunta de ke ƙasar Nijar matsuguni bayan juyin mulkin da aka yi a ƙsar.

    Mai magana da yawun ma'aikatar tsaro ta Pentagon Sabrina Singh ta ce a mayar da wasu sojojinta da ke sansani na 101 da ke kusa da babban birnin kasar Yamai zuwa sansaninta na 201 da ke Agadez "a matsayin riga-kafi" makonni shida bayan da sojoji suka karɓi mulkin ƙasar.

    Misis Singh ta ce wata ƙaramar tawagar sojojin za su ci gaba da zama a sansanin Yamai.

    Bayan juyin mulkin da sojoji sukayi a watan Yuli, Amurka ta dakatar da wasu ayyukan agajin da kasashen ketare ke bai wa ƙasar tare da dakatar da horar da sojoji, inda aka killace sojoji a sansanonin.

    A hukumance Amurka ba ta kira mamayar da sojoji suka yi a Nijar a matsayin juyin mulki ba, matakin da zai takaita irin taimakon tsaro da Washington za ta iya bai wa kasar da kayayyakin aiki da za a iya turawa ga sojojin.

    “Tsarin mu a Nijar bai canza ba. Matsayinmu har yanzu shi ne. Muna fatan za a nemi mafita ta hanyar diflomasiyya, amma babu wata barazana ga jami'an Amurka ko tashin hankali a kasa," in ji Ms Singh.

    Amurka na da a kalla dakaru 1,100 a sansanoninta guda biyu a Nijar.

    Sansanin jirage marasa matuka na Agadez mai nisan kilomita 920 daga birnin Yamai.

    Ita ma ƙasar Faransa wadda ta kasance tsohuwar ƙasar Nijar ta mulkin mallaka na da dakaru kusan 1,500 a ƙasar.

    Sai dai ya zuwa yanzu, Paris ta yi watsi da kiraye-kirayen da shugabannin da suka yi juyin mulki suka yi na su fice daga kasar, lamarin da ya haifar da zanga-zanga yayin da jama'a suka yi sansani a kusa da sansanin.

    • Shin Ecowas ta fara ba da kai ga sojojin Nijar ne?
    • Amurka ta gargaɗi Nijar a kan hatsarin aiki da sojojin hayar Rasha
  14. Kim Jong Un ya ƙaddamar da jirgin ƙarƙashin teku da zai iya harba nukiliya

    e

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a halarci bikin ƙaddamar da abin da Pyongyang ta kira da 'Jirgin ƙarƙashin teku na farko' da zai iya harba makaman nukiliya.

    Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce ƙaddamar da jirgin ya ɗaga ƙarfi da matsayin ƙasar, ta fuskar makaman nukuliya.

    An sanya wa jrigin suna 'Hero Kim Kun Ok' sunan sojan ruwan ƙasar da ya zana jirgin.

    Jirgin ƙarƙashin tekun na daga cikin jerin makaman da Koriya ta Arewa ta daɗe tana burin ƙerawa.

    u

    Asalin hoton, Reuters

    Hotunan da kafar yaɗa labaran ƙaar ta wallafa sun nuna Mista Kim na tsaye kusa da jirjin kewaye da manyan jami'an sojin ruwan ƙasar.

    Shugaban ya ce jirgin zai kasance ɗaya daga cikin makaman da sojojin ruwan ƙasar za su riƙa kai hari da shi ta ƙarƙashin teku.

    A baya-baya nan Koriya ta Arewa na ci gaba da gwajin makaman linzami masu nisan zango.

    t

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙaddamar da jirgin na zuwa ne kwanaki kafin bikin cikar ƙasar shekarar 75 da kafuwa.

    Kafar yaɗa labaran ƙasar ta ce ana sa ran China za ta tura tawagar wakilanta zuwa ƙasar domin halartar wani ɓangare na bikin ƙaddamar da jirgin.

    Hakan na zuwa ne bayan da rahotonni suka ce Mista Kim na shirin zuwa Rasha domin ganawa da Vladimir Putin.

    Ana fargabar cewa Koriya ta Arewa za ta buƙaci ƙarin fasahar makamai daga Moscow.

    j

    Asalin hoton, Reuters

    • Shugaban Koriya Ta Arewa ya bayyana ƴarsa ga duniya a karon farko
    • Hukumar nukiliya ta duniya na fargaba kan tashar Zaporizhzhia ta Ukraine
  15. Mun raba Najeriya da ƴan ta'adda fiye da 800 a wata uku - Sojoji

  16. Hotunan birnin Delhi da aka ƙawata kafin taron G-20

    Sa'o'i kaɗan gabanin fara taron G-20 da za a gudanar a birnin Delhi na ƙasar Indiya, tuni shugabannin ƙasashe da wakilai suka fara sauka a birnin, domin halartar taron da za a gudanar ranar 9 zuwa 10 ga watan Satumba.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An yi ta sanya hoton take taron a wurare daban-daban a birnin Delhi, inda mutane ke tururuwa domin ɗaukar hotuna
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wannan ne karo na farko da Indiya ke karɓar baƙuncin babban taro irin wannan.
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Hukumomin ƙasar sun ɗauki matakan tabbatar da gudanar da taron cikin kwanciyar hankali da lumana.
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ana na gyara titunan birnin domin ƙawata su
    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, An ta gyara wuraren hutu da shaƙatawa da dama a birnin gabanin taron
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugabanin ƙasashen Amurka Joe Biden da firaminitan Birtaniya Rishi Sunak, da na Canada Justin Trudeau, da shugaban Faransa Emmanuel Macron duk za su halarci taron.
    ...

    Asalin hoton, AFP

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jami'an 'yan sanda 40,000 ne za su kula da birnin a lokacin taron.
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    • Mece ce ƙungiyar G20 kuma me shugabanninta ke tattaunawa?
    • Me Najeriya za ta samu a shigarta ƙungiyar G20?
  17. Sarki Charles ya yi juyayin cikar Sarauniya Elizabeth shekara ɗaya da rasuwa

    Queen Elizabeth

    Asalin hoton, PA Media

    Sarkin Birtaniya Charles III ya wallafa saƙo tare da hoton da ya fi so na Sarauniya Elizabeth II domin tunawa da cikar mahaifiyar tasa shekara guda da rasuwa.

    Cikin saƙon, Sarki Charles lll ya ce yana tunawa da irin "jajircewar da ta nuna wajen hidimta wa ƙasar".

    Hoton da sarkin ya zaɓa ya nuna sarauniyar a lokacin da take matashiya mai shekara 42, da aka ɗauka a shekarar 1968.

    Sarauniya Elizabeth ll

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Kafin yanzu ba a taɓa wallafa wannan hoto ba

    Ranar 8 ga watan Satumban 2022 ne Sarauniya Elizabeth II ta rasu a fadarta da ke Balmoral tana da shekara 96 a duniya.

    Mutuwar tata na zuwa ne watanni bayan bikin cikarta shekara 70 a kan gadon sarauta.

    A saƙon alhinin da ya aike, Sarki Charles lll ya gode wa ƙasarsa kan "ƙauna da goyon baya" da suka nuna masa shi da matarsa Sarauniya Camilla a tsawon shekararsa guda ta farko da ya yi a kan gadon sarauta.

    "A yayin da ake cika shekara guda da rasuwar mai martaba sarauniya, da kuma hawanmu karagar mulki, muna iya tuna irin sadaukarwar da ta yi wajen hidimta wa ƙasarmu," in ji sarkin.

    "Haka kuma ina matuƙar godiya bisa soyayya da goyon baya da kuka nuna mini ni da matata a shekararmu ta farko a kan kadon sarauta, a yayin da muke iya bakin ƙokarinmu wajen hidimta muku".

    • Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II ta rasu, a cewar Fadar Buckingham
    • Ta'aziyyar Sarauniya Elizabeth: Tarihin rayuwar Sarauniyar Ingila
  18. Masu haƙar ma'adanai 30 sun mutu bayan ruftawar ƙasa a Abuja

    vc

    Asalin hoton, RVGH PRESS

    Bayanan hoto, Nyesom Wike ministan Abuja

    Masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba 30 ne suka mutu bayan ƙasa ta rufta kansu a ƙaramar hukumar Kuje da ke Abuja babban birnin Najeriya.

    Shugaban ƙaramar hukumar ne ya bayyana haka ranar Alhamis a lokacin da shugabannin ƙananan hukumomin birnin suka gana da ministan Abuja, Nyesom Wike.

    Haka kuma masu garkuwa da mutane sun sace mutum 19 ranar Alhamis a yankin ƙaramar hukumar Bwari da ke Abuja babban birnin Najeriya.

    Ministan - wanda ya nuna damuwarsa game da waɗannan batutuwa - ya ce zai gayyaci daraktan hukumar tsaron farin kaya da kwamishinan 'yan sanda birnin domin ɗaukar matakan da suka dace don kuɓutar da mutanen.

    Mista Wike ya kuma yi kira ga shugabannin ƙananan hukumomin da su kafa kwamitocin sa ido a ƙananan hukumominsu domin lura da ayyukan masu haƙar ma'adinai.

    Ya kuma ce a nasa ɓangare zai gana da ministan ma'adinai Dele Alake domin kawo ƙarshen ayyukan haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a Abuja.

  19. MDD ta koka kan raguwar ayyukan agaji a Sudan ta Kudu

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce an tilasta wa kungiyoyin jin ƙai rage ayyukansu a Sudan ta Kudu sakamakon matsalolin kuɗi da yadda ayyukan jin ƙan suka tsananta.

    Kimanin mutum miliyan 7.76 ne ke buƙatar tallafi, to sai dai ƙarancin kuɗi ga ƙungiyoyin tallafin ya sa mutum miliyan 3.2 ne kawai da ke cikin tsananin buƙata za su samu tallafin abincin.

    Hakan na nufin wadanda ke gab da mutuwa ne kawai za su samu agaji, har ma ana rage musu abinci.

    "Gaskiyar magana ita ce, babu isassun kayan aiki ga al'ummomin jin kai don biyan bukatu a Sudan ta Kudu," in ji Makena Walker, muƙaddashin darektan Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP).

    "Matsalar karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki na shafar kashi biyu bisa uku na al'ummar kasar, wanda hakan ya sa ta zama mafi muni a cikin matsalar ƙarancin abinci a duniya."

    Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta buƙaci dala biliyan 1.7 don agaji, kashi 46 cikin dari na kudin ne kawai aka samu.

    MDD ta kuma ce ana buƙatar fiye da dala miliyan 300 cikin gaggawa domin taimaka wa mutanen da yaƙin basasar Sudan ya ɗaiɗaita.

    • Abin da janye tallafin jinƙai da Birtaniya ke shirin yi ke nufi ga wani asibitin Sudan ta Kudu
    • Yadda ake samun ƙaruwar mata da ba sa samun abinci su koshi a Najeriya
  20. Hong Kong na fuskantar ambaliya ruwa mafi muni a tarihi

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Yankin Hong Kong da wasu sassan kudancin China na fama da ambaliyar ruwa mai ƙarfin gaske, yayin da yankin ke fuskantar mamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske a tarihi.

    Ruwan ya share tituna da tasoshin jiragen ruwa na ƙarƙashin ƙasa da ke yankin Hong Kong yayin da jami'ai suka rufe makarantu da wuraren aiki.

    Hukumar kula da hasashen yanayi ta yankin ta ce, mamakon ruwan sama da aka fara tun ranar Alhamis, shi ne ruwan sama mafi ƙarfi da yankin ya taɓa fuskanta a cikin kusan shekara 140.

    Hukumomi na aikin ceto domin kuɓutar da mutane, yayin da hotuna ke nuna yadda ruwa ke tafiya da mutane da ababen hawa.

    A ranar Juma'a, hukumomin Hong Kong sun ce aƙalla mutum 83 aka kai asibiti cikin sa'o'i 24 sakamakon isak mai ƙarfi da ruwa da ake tafkawa a yankin, lamarin da ya haifar da zaizayewar ƙasa tare da toshe wasu tituna.

    Wasu bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya mayar da titunan birnin tamkar wasu koguna, yayin da mutane neman tsira da rayukansu.