NNPCL zai karɓi rancen dala biliyan uku cikin gaggawa
Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida, Abdullahi Bello Diginza and Badamasi Abdulkadir Mukhtar
Rufewa
Masu bibiyar mu a wannan shafi, ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kenan.
Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta don ci gaba da tafka muhawara a kan labaran da muka wallafa.
Badamasi Abdulkadir Mukhtar ke fatan mu zama lafiya
Me sojojin mulkin Nijar ke nema daga ƙawayensu?
Cire tallafin fetir: Zulum ya bayar da tallafi ga gidaje 2,000
Asalin hoton, BORNO STATE GOVT
Gwamnan jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya raba tallafin abinci da sauran kayan buƙata ga mutum 2,000 a unguwar Feezan ta garin Maiduguri.
Rabon kayan da ya gudana a kwalejin Mohammed Goni, wata hanya ce ta rage wa jama'ar jihar raɗaɗin janye tallafin man fetir da gwamnatin tarayya ta yi.
A cikin watan Yuli gwamna Zulum ya ƙaddamar da shirin bayar da tallafin da nufin taimakawa iyalai dubu 300.
Asalin hoton, BORNO STATE GOVT
A ƙarƙashin shirin mazauna unguwar Feezan sun samu tallafin kayan abinci da sauran kayan buƙata, bayan tantance su domin tabbatar da cancantar su.
Kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautun jihar Borno, Sugun Mai Mele, ya ce unguwanni 15 ne za su amfana da wannan tallafi a cikin Maiduguri, kuma kowacce unguwa za ta samu buhun shinkafa 2,000 da kuma buhun wake 2,000.
Asalin hoton, BORNO STATE GOVERNMENT
Ana zargin sojoji da kisan fararen hula a Habasha
Asalin hoton, AFP
Mazauna gari da ƙungiyoyin adawa sun zargi dakarun Habasha da kisan fararen hula da dama a yankin Oromia, yayin da suke ci gaba da faɗa da ƙungiyoyin ƴan bindiga a Amhara.
Wasu iyalai da abin ya shafa a Yammacin Shoa sun shaidawa BBC cewa dakarun gwamnati sun kashe fararen hula aƙalla 10, ciki harda ƴan gida ɗaya guda huɗu.
Ƙoƙarin BBC na jin ta bakin gwamnatin dai bai cimma nasara ba.
Wani mazaunin yankin, Ararsa Yadesa, ya ce a lokaci guda sojoji suka kashe ƴan uwansa huɗu kuma ƴan gida ɗaya.
Haka nan kuma, jam'iyyar Oromo Liberation Front (OLF) da takwararta ta Oromo Federalist Congress (OFC) sun zargin gwamnati da kisan fararen hula da tsare wasu ba bisa ƙaida ba da kuma keta yancin ɗan adam a yammacin Shoa.
Sun ce mutanen da aka kashen sun kai 11.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun gwamnati ke faɗa da ƙungiyoyin mayaƙa a yankin Amhara.
Man City za ta sayar da Laporte ga Al-Nassr ta Saudi Arabia
Tottenham za ta sayar da Lloris ga Roma
Mutum bakwai sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kongo
Mutane aƙalla bakwai sun mutu bayan wani kwale-kwale ɗauke da kimanin mutum 300 ya nutse a yankin Mai-Ndombe da ke yammacin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Hukumomi sun ce suna ci gaba da ƙoƙarin zaƙulo mutanen da lamarin ya ritsa da su.
Shaidu sun bayyana yadda kwale-kwalen ya rabe biyu sannan ya nutse.
Mafi yawan mutanen da ke cikin kwale-kwalen ma'aikatan gwamnati ne a kan hanyarsu ta zuwa wani gari da ke maƙwabtaka da su.
Ƙwararru na alaƙanta irin wannan hatsari da ɗaukar kayan da suka zarce ƙima cikin kwale-kwalen da kuma rashin kula da inji yadda ya kamata.
A 2019 ma an samu irin wannan hatsari inda aka zaƙulo gawar mutum 30 bayan wani kwale-kwale ɗauke da mutum 400 ya nutse.
Harin lashe zinare: Afirka na fatan cin lambobin yabo a gasar duniya
An kashe sojojin Nijar a harin kwanton-ɓauna
Ma'aikatar tasron Nijar ta ce wasu mayaƙa sun kashe sojojin ƙasar 17.
An kuma raunata wasu sojin 20 a kwanton-ɓaunar da mayaƙan suka yi wa sojin a yankin Tillabéri da ke kusa da iyakar Nijar da Burkina Faso.
Dakarun sojin Nijar sun ce sun kashe mahara fiye da 100 a yayin da suke neman guduwa daga wajen da suka kai harin.
Sanarwar da gwamnatin ƙasar ta fitar ta ce: "Ɗaukin gaggawa da dakarunmu suka kai ta sama da ta ƙasa ya taimaka wajen yi wa maharan illa da kuma fatattakar su."
Gwamnatin ta miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe.
Wannan ne karo na bakwai da aka kai wa dakarun Nijar hari tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi makon uku da suka wuce.
Sojojin da suka ƙwace mulkin dai sun ce ayyukan ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi na daga cikin dalilansu na kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
NNPCL zai karɓi rancen dala biliyan uku cikin gaggawa
Asalin hoton, NNPC LIMITED/TWITTER
Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da bankin Afreximbank mai hada-hadar kayayyaki a ciki da wajen Afrika don samar da dala biliyan uku ta gaggawa da za a biya bashin ɗanyen mai da su.
Wata sanarwa da NNPCL ya fitar a yau Laraba ta ce an ƙulla yarjejeniyar ne a hedikwatar bankin da ke birnin Alƙahira na ƙasar Masar.
Kamfanin ya ce wannan yarjejeniya za ta taimaka wa shirin gwamnatin Najeriya na samar da daidaito a kasuwar canjin kuɗi da kuma bunƙasa darajar naira.
A makon da ya gabata darajar nairar ta yi faɗuwa mafi muni a tarihi, inda aka canzar da dala ɗaya kan N970 a kasuwar bayan fage - kafin ta ɗan farfaɗo zuwa N790 a ranar Talata.
Lamarin na faruwa ne tun bayan da Shugaba Tinubu ya sauya tsarin canjin kuɗin zuwa na kasuwa ta yi halinta kan darajar naira a watan Yuni.
Timber zai yi jinya mai dan tsawo in ji Arsenal
Lithuania za ta rufe iyakokinta shida da Belarus
Asalin hoton, Reuters
Ƙasar Lithuania za ta rufe iyakokinta shida da Belarus daga ranar Juma'a.
Gwamnatin ƙasar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani martani na sauyin yanayin siyasar yankin.
gwamnatin ta kuma ƙara da cewa ƙasar na fusknatar barazana a fannin tsaronta da kuma ayyukan fatauci da ake yawan yi a iyakokin ƙasashen.
Ƙasashen yankin sun ƙara tsarara tsaron iyakokinsu tun bayan da Belarus ta bai wa mayaƙan Wagner na Rasha masauki.
Kawunan 'yan Kenya sun rabu a kan kiraye-kirayen haramta TikTok
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Korafe-Korafe kan haramta TikTok sun janyo ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan majalisar dokokin Kenya da kuma al'ummar ƙasar.
A ranar Talata ne majalisar dokokin Kenya ta yi muhawara kan buƙatar korafin da wani dan kasar Bob Ndolo ya gabatar kan haramta TikTok .
Mista Ndolo ya buƙaci 'yan majalisar da su haramta TikTok, yana mai nuni da damuwar cewa dandalin na barazana ga al'adun gargajiya da na addinin Kenya.
Mai shigar da ƙarar ya kuma ce rashin tsarin TikTok a Kenya ya haifar da yaɗuwar munanan abubuwa da ba su dace ba a dandalin.
"Korafin ya nuna cewa yayin da TikTok ya samu karɓuwa tsakanin matasa a Kenya, abubuwan da ake yaɗawa a shafin ba su dace ba, domin kuwa suna tayar da hankulan jama'a da yaɗa batsa da kalaman ƙiyayya, wanda babbar barazana ce ga ɗabi'un al'adu da addini na Kenya," Moses Wetangula, kakakin majalisar dokokin Kenya, ya fada wa 'yan majalisar.
Mista Ndolo ya kara da cewa haramcin zai kare al'ummar Kenya daga illolin TikTok da suka hada da jarabar son yin Tiktok din da ka iya kawo cikas ga karatu da lafiyar kwakwalwar dalibai.
Mista Ndolo ya kuma nuna damuwarsa kan cewa manhajar na iya zama wajen tattarawa ko raba bayanan mutanen Kenya ba bisa ka'ida ba.
Wasu 'yan majalisar dokoki da 'yan kasar sun goyi bayan korafin, yayin da wasu ke cewa irin wannan matakin zai hana ci gaban fasahar kasar da kuma shafar kudaden shiga ga yawancin matasan Kenya da ke ƙirƙirar abubuwa a kan TikTok.
TikTok zai dauki mataki a kan bidiyon koyar da cin abinci da basu dace ba
Yadda wasu ‘yan Tiktok suka kwana a gidan yari bayan ɓata sunan Gwamna Ganduje
An kori ma'aikatan fasfo a Ghana
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Ministar Harkokin Waje da
cigaban Yankuna ta Ghana, Madam Shirley Ayorkor Botchwey ta kori dukkan jami'an
ofishin fasfo da ke aiki sama da shekara guda daga ofishin.
A cewar ministar hakan
martani ne ga karuwar damuwar da ake samu na zargin su da hannu a haramtattun
ayyuka da ayyukan cin hanci da rashawa da ke bata sunan sabon tsarin bayar da
fasfo ta yanar gizo, wanda aka kaddamar da shi domin dakile ayyukan cin hanci
da rashawa wajen karbar fasfo a kasar ta Ghana.
Tinubu na alhini kan mutuwar sojojin da jirginsu ya faɗo
Ingila ta kai wasan ƙarshe a gasar Kofin Duniya ta mata
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Ingila ta kai wasan ƙarshe a gasar cin Kofin Duniya ta Mata da haɗaƙar ƙasashen Australia da New Zealand ke karɓar baƙunci.
Ingila ta kai matakin ne bayan doke Australia da ci 3-1 a wasan da aka fafata a birnin Sydney na ƙasar Australia
Tawagar matan Ingilar ta kasance tawagar 'yan wasan ƙasar da ta taɓa kai wa wasan ƙarshe a matakin duniya tun shekarar 1966.
Ella Toone ce ta fara jefa ƙwallo a ragar Australia kafin zuwa hutun rabin lokaci
Bayan koma wa hutun rabin lokaci ne 'yar wasan Australia Sam Kerr ta farke ƙwallon bayan da ta zira wata ƙwallo da ta ƙayatar daga tazarar yadi na 25.
Lauren Hemp ta ƙara jefa ƙwallo ta biyu a ragar Australia bayan kuskuren mai tsaron baya, kafin Alessia Russo ta ƙara ƙwallo ta uku.
A yanzu Ingila za ta ƙara da Sifaniya a wasan ƙarshe da za a buga ranar Lahadi
Firaministan Nijar ya ziyarci ƙasar Chadi
Asalin hoton, Chadian presidency
Bayanan hoto, ...
Firaministan Jamhuriyar Nijar da sojoji suka naɗa, Ali Mahaman Lamine Zeine, tare da wasu mambobin majalisar mulkin soja biyu sun ziyarci kasar Chadi domin tattaunawa da shugaban kasar, Janar Mahamat Idriss Deby.
Zeine - wanda ya bayyana a matsayin fuskar diflomasiyya ta gwamnatin soja - ya ce a yanzu ƙasarsa na karkashin gwamnatin mulkin soji, inda ya ce a shirye suke da tattaunawa.
Sai dai ya ce gwamnatin mulkin sojan za ta yi magana ne kawai da "ƙawayensu" wadanda ke mutunta gwamnatin Nijar.
Shugaban kasar Chadi Deby ya yi kokarin shiga tsakanin sojojin na Nijar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum don shawo kan lamarin.
Kasar Chadi ta kuma ce ba za ta shiga duk wani matakin soji da za a dauka kan jagororin juyin mulkin Nijar ba.
A ranakun Alhamis da Juma'a ne, manyan hafsoshin sojojin kasashen yammacin Afirka (Ecowas) za su gana a birnin Accra na kasar Ghana, domin tattauna halin da ake ciki a Nijar.
Ecowas ta umarci dakarunta su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar
Ƙasashen Yamma za su fara kwashe 'yan ƙasashensu daga Nijar
'Yan ci-rani da dama ne suka mutu, yayin da aka ceto 40 a kusa da Cape Verde
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
An gano gawarwakin wasu bakin haure da dama a yammacin Afirka a cikin wani kwale-kwale da ke bi ta Cape Verde, tare da ceto kusan mutum 40.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka jikkata ba.
Rahotanni sun ce jirgin ya taso ne daga kasar Senegal wata daya da ya gabata ɗauke da mutane kusan 100.
An yi imanin cewa jirgin na kan hanyar zuwa tsibirin Canary na Spain, wata kofar da bakin 'yan ci-rani ke bi zuwa Tarayyar Turai.
Mutane da dama da ke son tsere wa talauci da yaƙi ne ke jefa rayuwarsu cikin hatsari, a ƙoƙarinsu na tsallaka teku zuwa Turai kowace shekara.
Yadda ƴan ci-rani ke jefa rayuwarsu cikin hatsari wajen tsallaka teku
Me ya sa 'yan Pakistan ke yin kasadar zuwa Turai ta Libya?
Farashin dala na ci gaba da sauka a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Farashin dala na faɗuwa a kasuwannin canjin kuɗi a Najeriya daga naira 940 zuwa naira 890 a safiyar Laraba, kamar yadda bayanan da BBC ta samu daga kasuwannin canji a birnin Legas suka nuna.
Bayanan sun ce a safiyar jiya Talata, an sayar da dalar Amurka a kan naira 940, da yamma kuma, ta fadi zuwa naira 927 a kasuwannin canjin na Legas.
Wannan na zuwa ne bayan ganawa da muƙaddashin gwamnan babban bankin kasar, Folashodun Shonubi, ya yi da Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin, kan yadda za a farfaɗo da darajar Naira.
A kasuwannin canji na Abuja kuma, a safiyar Laraba, dalar ta fadi zuwa naira 900, bayan a safiyar Talata, an sayar da ita a kan naira 947, da dare kuma, ta sauka zuwa 910.
Haka ma Kano da ke arewacin ƙasar, bayanai daga kasuwar canji ta Wapa na nuna cewa dalar ta faɗi daga naira 946 a safiyar Talata zuwa naira 900 a safiyar yau Laraba.
A daren jiya, dalar ta fara sauka a kasuwannin canji na Kano inda ta fadi zuwa naira 927.
Wannan lamari na nuna cewa darajar naira ta fara farfadowa, bayan fargabar da aka yi ta nunawa daga makon jiya cewa dalar Amurka na iya kai wa har sama da naira 1,000.
Daga bisani, BBC Hausa ta sake tuntubar masu hada-hada a kasuwannin canji na Abuja, inda suka bayyana mana cewa dalar ta sake faduwa daga naira 900 da aka bude kasuwa da ita da safe zuwa naira 800 da misaln karfe 1:00 na rana a yau Laraba.
A kasuwar canji ta kano kuma, wani dillali ya shaida mana cewa an sayar da dalar a kan naira 890 daga karfe 1:30 na rana, ba kamar yadda aka sayar da ita naira 900 a safiyar yau ba.
Amma kamar a legas, farashin bai sauya ba.
Hakan dai na nuna yanayin saurin sauka da tashi na kasuwar canjin kudaden waje na Najeriya a wannan lokaci da ake ciki.
Me ya sa darajar naira ke daɗa karyewa?
Farashin man fetur zai iya ƙaruwa saboda tashin dala