'Yan bindiga sun kashe matafiya 11 a Nijar

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Jama'armu ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafin na labarai kai-tsaye.

    Mu haɗu da ku gobe da safe do kawo muku wasu sababbi.

    Kafin lokacin, Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  2. Matashin da yajin aikin ASUU ya sa ya fara sana'ar zane-zanen Larabci

    Bayanan bidiyo, Danna hoton sama ku kalli bidiyo

    Matashi Dahiru Abubakar Sajo ya faɗa wa BBC Hausa cewa ya fara sana'ar zane-zane cikin harshen Larabci bayan fara yajin aiki da malaman jami'a suka yi a Najeriya.

    Dahiru ɗalibi ne a aji na biyar a Jami'ar Modibbo Adama da ke Jihar Adamawa. Ya ce ya samu lambar yabo a shekarar 2020 sakamakon zane-zanen da yake yi.

    Akwai nasarori sosai kuma ina fatan wannan sana'a za ta kai ni wurare da dama, ba Najeriya kaɗai ba har ma ƙasashen ƙetare," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa yana fuskantar matsaloli masu yawa a aikin.

  3. 'Yan bindiga sun kashe matafiya 11 a Nijar

    Wani mutum riƙe da bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Nijar na cewa 'yan bindiga sun kai hari kan wasu matafiya inda suka kashe mutum 11 a yankin Tillaberi.

    Garin Tillaberi na iyaka da kasar Mali ta ɓangaren yammacin Nijar.

    Bayan kashe mutanen da suka hada da fasinjoji da drebobin motoci, sun kona motoci biyu tare da yin awon gaba da ɗaya.

    Rahotanni sun ce an kai harin a tsakanin Cizgoro da na Banibangu da misalin ƙarfe huɗu na yammacin Asabar.

    'Yan bindiga masu iƙirarin jihadi sun zamar wa yankin na Tilaberi ƙarfen ƙafa duk da ƙoƙarin da jami'an tsaro ke cewa suna yi.

  4. Arsenal ta barar da maki biyu a gidan Southampton

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Southampton da Arsenal sun tashi 1-1 a wasan mako na 13 a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a filin wasa na St Mary.

    Arsenal wadda ke jan ragamar teburin Premier ta fara cin kwallo ta hannun Granit Xhaka a minti na 11 da fara wasa.

    Sai dai Southampton ta farke ta hannun Stuart Armstrong bayan da aka koma zagaye na biyu.

    Wannan shi ne karon farko da Gunners ta buga 1-1 a Premier League a kakar bana a karawa 11, bayan da ta yi nasara a tara, Manchester United ta doke ta 3-2.

  5. NDLEA ta kama mutum huɗu da zargin safarar miyagun ƙwayoyi

    Ƙwayoyi

    Asalin hoton, NDLEA

    Jami'an hukumar NDLEA mai yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta ce ta kama mutum huɗu da ake zargi da hannu wajen safarar haramtattun ƙwayoyi masu nauyin 16,000kg a Jihar Legas.

    Ana zargin mutanen - maza biyu da mata biyu - da safarar ƙwayoyi daga ƙasar Netherlands, a cewar kakakin NDLEA, Femi Babafemi.

    A cewarsa, jami'an NDLEA sun shafe makonni suna bin sawun Aro Aderinde mai shekara 48, inda suka kama shi da zargin shigar da ganyen wiwi mai nauyin 3,149kg ta hanyar ɓoye shi a cikin ganyen kwakwa wanda aka zuba a kwantena mai lamba MSKU 1820587.

    A gefe guda kuma, an kama mata biyu - Hauwawu Bashiru and Basirat Adebisi Yahaya - da zargin yunƙurin fitar da ƙwayar methamphetamine mai nauyin 90kg bisa haɗin gwiwa da wani fasto mai suna Anietie Okon Effiong mazaunin Jihar Akwa Ibom kuma aka kai su Uyo don fuskantar shari'a.

    Haka nan, an kama wani da ake zargi da dillancin ƙwaya mai suna Monday Michael mai shekara 45 lokacin da yake ɗauke da ganyen wiwi mai nauyin 365kg cikin mota biyu a Legas.

  6. Masu zanga-zanga a Sudan na neman a kawo ƙarshen rikicin ƙabilanci

    Masu zanga -zanga sun yi dandazo a birnin Damazin na Sudan inda suke neman a kawo karshen rikicin kbilanci da ya hallaka akalla mutum 200.

    Rahotanni daga birnin na kudancin kasar sun ce dubban jama'a ne suka yi wa hedikwatar sojoji tsinke suna neman lalle hukuma ta kawo karshen tashin hankalin.

    Wasu ma sun so su yi kutse cikin ginin kafin banka wa ofishin mulki na karamar hukuma wuta.

    Rikici tsakanin Hausawa da sauran kabilu a kan gonaki ya haddasa mummunar musayar wuta a makon da ya gabata, inda jama'a suka ce an kona gidaje da shaguna.

    Hukumomin Sudan sun sanya dokar ta-baci a yankin.

  7. Labarai da dumi-dumi, Mayaƙan Al-Shabab na kai wa otel hare-hare a Somaliya

    Rahotanni daga Somaliya na cewa mayaƙan ƙungiyar Al-Shabab mai iƙirarin jihadi na kai wa wani otel hare-hare a birnin Kismayu mai tashar jirgin ruwa.

    Wata mota maƙare a bama-bamai ta afka wa otel ɗin Tawakai da ke tsakiyar birnin, inda shaidu suka ce har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton suna jin ƙarar harbe-harbe.

    Haka nan sun ce sun ji fashewa mai ƙarar gaske. Hukumomin gwamnatin yankin sun tabbatar wa kafar talabijin ɗin ƙasar cewa suna yaƙar mayaƙan na Al-Shabab.

    Zuwa yanzu babu bayani kan mutanen da lamarin ya ritsa da su.

    Garin ya ɗan samu zaman lafiya tun bayan korar ƙungiyar daga Kismayu a 2012.

    Hare-haren na zuwa yayin da gwamnatin Somaliya ke cewa ta kashe gwamman mayaƙan a yankin Shabelle da ke kudancin ƙasar.

  8. An yi bikin bude gida 804 da gwamnatin jihar Borno da hukumar UNDP suka gina

    zulum

    Asalin hoton, Twitter/GOVBORNO

    Bayanan hoto, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya kaddamar da bude gine-ginen

    Gwamantin jihar Borno tare da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, sun kaddamar da bude gidaje 804 wadanda suka sake ginawa domin tsugunar da al'umomin Ngarannam a jihar.

    Shugaban ma'aikatar fadar shugaban Najeriya Farfesa Ibrahim Gambari ne ya kaddamar da bude gine-ginen.

    Gwamna Zulum ya mika wa al'umomin gine-gine 360 da suka hadar da shaguna, da makarantu, da gidaje ga malaman makaranta, da jami'an tsaro tare da ginin ofishin 'yan sanda daya.

    Gidaje

    Asalin hoton, @EUINNIGERIA

    Gwamnan jihar ya fada a cikin wata sanarwa cewa daga cikin gidajen 804, a yanzu an kammala 564.

    Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta gina gida 304, a yayin da hukumar ta UNDP za ta gina gida 500.

    Borno

    Asalin hoton, Twitter/GOVBORNO

    A wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na Tuwita ya ce Farfesa Gambari ya bude gidaje 804 da hukumar UNDP da gwamnan jihar suka gina.

    Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa sun bayar da kyautar shanu 2,674, da tufafi da abinci da kyautar kudi naira 100,000 ga duk magidanci.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. 'Yan bindiga sun kashe fasinjoji biyu tare da sace mutum uku a Katsina

    'Yan bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari magamar Jibiya da ke yankin kan iyaka a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya inda suka kashe fasinjoji biyu tare da sace wasu mutum uku.

    Gidan Talbijin na Channels TV a Najeriya ya ambato wani shaida na shaida masa cewa 'yan bindigar sun kaddamar da harin ne da misalin karfe 9:15 na daren ranar Asabar.

    Ya ce ''maharan sun tsayar da motoci guda biyu da ke kan babbar hanya inda suka kshe fasinjoji biyu tare da sace uku, kafin jami'an tsaro su samu nasarar fatattakarsu''.

  10. Jirgin yakin Rasha ya fado kan wani gida a birnin Irkutsk

    Rasha

    Asalin hoton, TELEGRAM

    Hukumomi a kasar Rasha sun ce wani jirgin yakin sojin kasar ya rikito a wata unguwa da ke kudancin Irkutsk

    Jirgin yakin mai suna Sukhoi Su-30, ya fado kan wani gida mai hawa biyu a birnin Irkutsk, kamar yadda gwamnan yankin Igor Kobzev ya wallafa a shafinsa na Telegram.

    Gwamnan ya ce yana wajen da lamarin ya faru, kuma duka matukan jirgin sun mutu, amma babu wanda ya ji ciwo a cikin gidan.

    Ma'aikatar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta ce jirgin ya rikito ne a yayin da ake kan gwajinsa.

    Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda gine-gine da dama suka kama da wuta.

    Wannan dai shi ne karo na biyu da jirgi ke faduwa a kasar cikin kwanaki shida.

    A ranar Litinin din da ta gabata ma wani jirgin soji ya fadi kan wani gini a kudancin birnin Yeysk, da ke kusa da kan iyaka da Ukraine, tare da kashe akalla mutum 15.

  11. Amsoshin Takardunku

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin

    Shin mene ne tarihin kyautar Ballon d'Or da ake bai wa gwarzon dan ƙwallon kafa a duk shekara?

    Kunna wannan shirin domin samun amsar wannan tambaya da ma wasu tambayoyin da suka jibanci wannan kyauta.

  12. Najeriya ta kwaso 'yan kasar 542 da suka makale a Dubai

    An kwaso 'yan Najeriya

    Asalin hoton, Twitter/GEOFFREYONYEAMA

    Bayanan hoto, An kwaso 'yan Najeriya daga Dubai

    Gwamnatin Najeriya ta kwashe 'yan kasar kimanin 542 da suka makale a kasar hadaddiyar Daular Larabawa.

    A wani sako ta Hukumar da ke kula da lamurran 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce da misalin karfe 4:29 na asubahin yau ne jirgin da ya kwaso mutanen ya sauka a filin jirgin saman Abuja babban birnin kasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da hukumar shige da fice ta kasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta bayyana dakatar da bai wa 'yan Najeriya biza, saboda wasu matsaloli da suka shafi diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

    Rahotonni sun ambato gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na cewa duka wadanda suka cika takardun neman biza za a mayar musu da takardunsu ba tare da samun amincewa ba.

    Ta kuma ce ''kin amincewar ya shafi kowanne dan Najeriya, dan haka babu wanda za a ba shi biza a halin yanzu''.

    A baya-bayan nan dai dangantaka na kara yin tsami tsakanin kasashen biyu, inda a watan da ya gabata kasar ta UAE ta daina bayar da bizar yawon bude ido ga 'yan kasa da shekara 40, lamarin da ya shafi 'yan Najeriya da na wasu kasashen.

    Haka kuma a shekarar 2021 ma ƙasashen biyu sun shafe watanni masu yawa suna ce-ce-ku-ce game da harkar sufurin jiragen sama

  13. Buhari ya tafi Koriya ta Kudu

    Shugaba Buhari

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Shugaba Buhari yayin da ya hau jirgi

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi kasar Koriya ta Kudu don halartar taro kan harkokin lafiya na duniya da aka yi wa laƙabi da World Bio Summit, 2022.

    Taron mai taken 'Makomar Rigakafi da Lafiyar Rai' wanda gwamnatin Koriya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka shirya, za a gudanar da shi cikin kwanaki biyu wato ranakun Talata da Laraba.

    Buhari

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Buhari tare da wasu gwamnonin kasar da ke cikin tawagarsa

    A cewar sanarwar da Fadar Shugaban Najeriya ta fitar ranar Asabar, an gayyaci Najeriya ne tare da wasu ƙasashen Afirka biyar game da ba da horo kan yadda za a dinga samar da rigakafin cutuka bisa fasahar MRNA a Afirka.

    Buhari

    Asalin hoton, State House

    Mutane da dama ne dai suka yi wa Buhari rakiya zuwa taron, waɗanda suka haɗa da wasu gwamnoni da ministoci da shugabannin ma'aikatu da sauran manyan jami'an gwamnati.

    Buhari

    Asalin hoton, state House

    Bayanan hoto, Ana sa ran Buhari zai koma gida bayan kammala taron, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
  14. 'Yan sanda sun kuɓutar da mutum 17 a Zamfara

    'Yan sanda

    Asalin hoton, Nig Police

    Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kubutar da mutum 17 da aka yi garkuwa da su a dazukan Gando, da Bagega da kuma dajin Sunke a karamar hukumar Anka da ke jihar

    A wata sanarwa da mai magana da rundunar 'yan sandan jihar Mohammed Shehu ya sanya wa hannu, ya ce an sace mutanen ne a kauyukan Akawa da Gwashi da Tungar Rogo da kuma Anka, inda aka kai su sansanin 'yan ta'adda da ke cikin dazukan.

    Sanarwa ta ci gaba da cewa “Rundunar ta kubutar da mutanen ne bayan da jami'an tsaron suka samu bayanan da ke cewa wasu gungun 'yan ta'adda sun kai farmaki wadannan kauyuka tare da sace mutane masu yawa, inda kuma suka tafi da su cikin dazukan Gando, da Bagega da kuma dajin Sunke''

    Mutanen dai sun kwashe kusan mako guda a hannun 'yan fashin dajin kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    A baya-bayan nan dai Jihar Zamfara na fuskantar karuwar hare-haren 'yan fashin daji wadanda ke sace mutane domin neman kudin fansa.

    Ko a makon da yabata ma dai 'yan fashin dajin sun yi harbi kan mai uwa-da-wabi ga mutanen da suka je cin kasuwa a Tashar 'Yar Sahabi cikin yankin Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar , inda suka kashe mutum tara, tare da raunata mutum biyar ciki har da mata da kananan yara.

  15. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin

    Ahmad Abba Abdullahi tare da Auwal Ahmad Janyau ne suka gabatar da shirin na wannan makon.

  16. Dubban Iraniyawa sun gudanar da zanga-zanga a birnin Berlin

    Iran

    Asalin hoton, otthes

    Ƴan sanda a Jamus sun ce kusan Iraniyawa 80,000 ne da magoya bayansu suka shiga wata zanga-zanga a Berlin domin nuna goyon baya ga masu zanga-zanga a ƙasar Iran.

    Wannan zanga-zangar ita ce mafi girma da ƴan Iran suka yi a ƙasashen ƙetare.

    A yayin zanga-zangar, Iraniyawa daga faɗin Turai sun rinƙa ambatar mata da rayuwa da kuma ƴanci tare da kira ga ƙasashen yamma da su ƙara ƙaƙaba wa dakarun juyin juya hali na Iran ɗin takunkumi.

    A Iran ɗin ƙanta, an shiga mako na shida na zanga-zanga wadda ta samo asali tun bayan mutuwar matashiyar nan a hannun jami'an tsaro wadda aka kama kan zargin ƙin rufe kanta yadda ya kamata da ɗankwali. Kuna shan.,,,,

  17. Rasha ta umarci mazauna Kherson da su gaggauta ficewa daga birnin

    Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Kherson ne birnin farko da Rasha ta fara kwacewa a Ukraine

    Jami'an Rasha da ke iko da birnin Kherson na Ukraine sun buƙaci mazauna birnin da su fice daga birnin ba tare da bata lokaci ba, inda jami'an suka ce yakin da sojojin ke yi ya yi tsanani a birnin.

    A daidai lokacin da dakarun Ukraine ke ƙara matsawa gaba ta gaɓar yamma da kogin Dnipro, akwai dubbai da ke tsallakawa ta ɗaya ɓangaren.

    Mutumin da Rasha ta naɗa a matsayin wanda ke jagorantar gudanar da lamura a birnin na Kherson ya ce gwamnatinsa tana da shirin kwasar aƙalla mazauna birnin 10,000 a duk rana domin kare su daga harin ramuwar gayya daga Ukraine.

    Kherson ne dai birni na farko da Rasha ta soma ƙwacewa bayan kutsen da ta yi a Ukraine.

    Ana kallon idan Ukraine ta sake ƙwace birnin wani babban ci gaba ne a gare ta a wannan yaƙi.

  18. Shugaban China ya yi tazarce zuwa wa'adin mulki na uku

    Xi Jinping

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban China Xi Jinping ya kafa tarihi a matsayin Shugaban China bayan ya samu damar yin tazarce zuwa wa'adi na uku a mulkinsa.

    Hakan na nufin Mista Xi ya zama shugaba mafi karfin fada-a-ji tun da Mao Zedong ya mulki kasar.

    A halin yanzu dai Jam'iyyar Kwaminisanci ta ƙasar ta tabbatar da shi a matsayin babban sakataren jam'iyyar wanda hakan ke nufin a watan Maris mai zuwa yana da tabbacin ɗorawa a kan mulkin ƙasar na wasu shekaru biyar.

    Kafin a kawo wannan matakin, tuni manyan kusoshin jam'iyyar suka bayyana goyon bayansu ga tsawaita wa'adin mulkin Mista Xi, baya ga amincewa da suka yi ga wasu sauye-sauye masu yawa da suka tilasta wa wasu manyan jami'ai ajiye mukamansu

  19. Assalamu Alaikum

    AB Diginza

    Asalin hoton, Mo Sani

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da sake saduwa a wannan rana ta Lahadi, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai ku ci gaba da kasancewa da mu a wannan lokaci na hutun karshen mako, domin sanin halin da duniya ke ciki.

    Haka kuma kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafa.

    Suna na Abdullahi Bello Diginza kuma ni zan ja ragamar shafin a daidai wannan lokaci.