Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/10/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/10/2025.

Rahoto kai-tsaye

Daga Habiba Adamu da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo karshen wannan shafin na labaran kai-tsaye.

    Da fata kun ji dadin kasancewa tare da mu.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

  2. Kotun ICC ta kama jagoran Janjaweed da laifin yaƙi

    ICC

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    An samu wani shugaban 'yan tawayen Sudan da laifin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a yankin Darfur sama da shekaru 20 da suka gabata.

    Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, na daya daga cikin jagororin kungiyar Janjaweed, da ke samun goyon bayan gwamnati.

    Ƙungiyar tana cikin ƙungiyoyin da ake zargi tana kana gaba wajen addabar yankin Darfur, inda ta kashe daruruwan mutane.

    Kushayb shi ne mutun na farko da ya fuskanci tuhuma a kotun ta ICC kan ta'asar da aka yi a Darfur.

    Yaƙin wanda ya auku a tsakanin 2003 zuwa 2020 na cikin yaƙoƙin duniya da suka jefa mutane da dama cikin bala'i, inda har aka yi zargin ɓangarorin yaƙin da kisan ƙare dangi.

    Sai dai har yanzu ƙasar ta Sudan na cikin yaƙi saboda yaƙin da ake gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF.

  3. Yaushe Wike zai sakar wa Fubara mara?

    Siminalayi Fubara da Wike

    Asalin hoton, Siminalayi Fubara

    Tun bayan komawar Siminalayi Fubara ofis a matsayin gwamnan jihar Rivers a ranar 18 ga watan Satumba, bayan kwashe watanni shida a dakace sakamakon dokar ta-ɓaci da shugaba Bola Tinubu ya ƙaƙaba wa jihar sakamakon rikice-rikicen siyasa, ake ta ganin Wike da Fubara inda a ƙarshen makon ma mutanen biyu suka yi wata ganawar sirri.

    Ana dai ganin cewa ganawar ta sirri ba za ta rasa nasaba da rushe kwamishinoni da sauran ma'aikatan gwamnatin da Fubara ya yi ba, a ranar bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ƴancin kai.

    Masu fashin baƙin na ganin ganawar da mutum biyun suka yi na da alaƙa da koƙarin sasantawa ta hanyar raba muƙaman kwamishinonin da za a naɗa a nan gaba, wani abu da ake ganin na ɗaya daga batutuwan da aka cimma da gwamnan - wato raba mukamai tsakaninsa da Wike.

  4. Jam'iyyar hamayya ta kasa takaɓus a zaɓen majalisar Syria

    Syria

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakamakon farko-farko na zaben 'yan majalisa da aka gudanar a karon farko a Syria, tun bayan hambarar da mulkin shugaba Bashar al-Assad ya nuna cewa babu wakilcin mata sosai, domin ba a zabi mace ko daya ba a birnin Damascus.

    Zaben na jiya Lahadi ya bayyana karara babu wani tagomashi da sabuwar jam'iyar People's Assembly, wanda ita ake ganin za ta taka rawa lokacin mika mulki.

    A maimakon haka kwamitin zabe ne ya zabi kusan kashi biyu bisa uku na kujerun 'yan majalisun.

    Sauran kuma shugaban riko Ahmad al-Sharaa ne zai nada su. Sai dai masu suka na cewa rashin hakan zai janyo rashin cikakkiyar dimokuradiyyar da ake fatan kafuwarta a kasar ta Syria.

  5. Jam'iyyar hamayya a Tanzania ta zargi ƴansanda da jikkata mambobinta 16

    Tanzania

    Asalin hoton, AFP

    Babbar jam'iyyar adawa ta Chadema a Tanzania, ta zargi 'yansanda da jikkata mambobin ta 16 da ke wajen kotun da ake yi wa jagoransu Tundu Lissu shari'a kan cin amanar kasa.

    Jam'iyyar hamayya ta Chdema ta ce da karfin tuwo 'yan sanda suka fitar da su daga harabar kotun, lamarin da ya jikkata da dama daga cikinsu.

    Jam'iyyar ta ce abin da ya farun cin zarafi ne ga mabiyanta, kuma tuni an kai su asibiti domin kula da lafiyarsu.

    Kawo yanzu 'yansandan ba su ce uffan kan abin da ya faru a wajen ginin kotun da ke Dar-es-Salaam ba, inda magoya bayan Chadema suka taru domin ganin yadda za ta kaya.

  6. Brazil ta buƙaci Trump ya rage mata harajin kayayyaki

    Brazil

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva ya gana da Shugaba Amurka Donald Trump ta bidiyo, wanda shi ne karo na farko da shugabannin suka gana tun bayan da Amurka ta ƙaƙa ba ƙasar Brazil harajin kayayyakin.

    A ganawar ta waya, Brazil ta buƙaci Trump ya rage harajin da ya ƙaƙaba kan kayayyakin ƙasarta da ake shigarwa Amurka.

    Trump ya bayyana wayar da "abu mai kyau" wadda ya ce an fi tattaunawa ne kan abubuwan da suka shafi tattalin arziki da kasuwanci.

    Ya buƙaci sakataren harkokin wajensa da ya ci gaba da tattaunawa da Brazil kan batun, duk da ya karɓa lambar shugaban na Brazil domin su ci gaba da ganawa kai-tsaye.

  7. Tinubu ya buƙaci NAHCON ta rage kuɗin Hajjin bana

    Tinubu

    Asalin hoton, PRESIDENCY NG

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu.

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin.

    Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana.

    Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na bana, ciki har da tattaunawa game da kuɗin kujera.

    "Saboda yadda farashin naira ya haɓaka da kuma sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin Najeiya da aka fara gani, shi ne mataimakin shugaban ƙasa ya ce yana ganin idan har maniyyata sun biya tsakanin naira miliyan 8.5 zuwa miliyan 8.6 a bara, yanzu da darajar naira ta ɗaga, ya kamata a ga canjin da aka samu a kuɗin Hajjin bana."

    A nasa ɓangare, sakataren hukumar alhazan, Dr Mustapha Mohammad ya ce wannan matakin zai taimaka wajen ƙara yawan mahajjatan bana.

  8. Aƙalla mutum miliyan 100 ne suka jarabtu da shan sigarin zamani - WHO

    Vape

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce aƙalla mutum miliyan 100, ciki har da ƙananan yara miliyan 15 ne suka yi tsananin sabo da shan taba sigari ta zamani da ake kira da vape.

    Darakta a hukumar, Dokta Etienne Krug ya ce zuƙar tabar ta zamani na da matsala, "saboda ana tallata su ne da cewa ba su da illa sosai, amma a zahiri, suna jefa matasa da ƙananan yara cikin ta'ammali da sinadarin nicotine da ke cikin sigari ne."

    WHO ta ce wannan sabon salo zai ɓata ƙoƙarin da aka yi gomman shekaru ana yi wajen yaƙi da shan sinadarin nicotine.

    Darakta-janar na WHO, Dr Tedros ya zargi kamfanonin sigari da yunƙurin jefa ƙananan yara cikin shan sigari ta hanyar zamanantar da abun.

    "Yunƙurin da ake yi na yaƙi da shan sigari ya yi amfani matuƙa, inda miliyoyin mutane suka rage shan sigarin a ƙasashen duniya a baya," in ji shi.

  9. Ukraine ta kai hari a kamfanin haɗa makaman Rasha

    Putin

    Asalin hoton, EPA

    Sojojin Ukraine sun ce sun kai hari daya daga cikin masana'antun da Rasha ke hada ababen fashewa da albarusai da dama.

    Sojojin sun bada rahoton fashewar abubuwa a cibiyar makamashi ta Sverdlov da ke tsakiyar yankin Volga na Rasha.

    Ko da tsakar dare, Ukraine ta kai hari depo din mai da ke yankin Crimea da Rasha ta mamaye.

    Yayin da fatan da ake da shi na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kawo karshen yakin Rasha a Ukraine ke kara dakushewa, a bangare guda kuma sojojin sun zafafa kai hare-hare cikin Rasha musamman depo-depo din mai.

  10. Wakilan Hamas za su sa labule da Masar da Qatar kafin ganawa da Isra'ila

    Gaza

    Asalin hoton, AFP

    A yau ne masu shiga tsakani na bangaren Hamas za su gana da takwarorinsu na Masar da Qatar a birnin Alkhahira, gabannin tattaunawar keke-da-keke da wakilan Isra'ila a birnin Sharm El-Sheikh.

    Wakilin BBC ya ce babbar tawagar ta Hamas tun bayan fara yakin da ta kunshi mambobi 11 ciki har da wanda ke wakiltar Falasdinawan da ake tsare da su a gidajen kason Isra'ila.

    Ana fatan za su tsaida ranar da tsagaita wutar za ta fara aiki, da tattauna mataki na gaba kan shirin zaman lafiyar.

    An cimma hakan ne bayan amincewar da Hamas ta yi da daftarin yarjejeniyar kawo karshen yakin da shugaba Trump na Amurka ya gabatar.

  11. An kashe ƴansanda uku a harin jamhuriyyar Benin

    ,,,,

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla ƴansanda uku aka kashe a wani harin da ƴanbindiga suka kai shingen bincike jami'an tsaro da ke garin Segbana na yankin Alibori a ƙasar Benin da ke da iyaka da Najeriya.

    Kafar yaɗa labarai ta Faransa, RFI ta ba da labarin cewa, akwai kuma wani ɗansanda guda da ya ɓata, sannan daga ɓangaren ƴanbindigar akwai waɗanda aka kashe.

    Mahukunta sun tura ƙarin jami'an tsaro kan iyakar, tare da kama wasu da ake zargi da hannu a harin, kuma an ƙaddamar da bincike domin ƙara fahimtar musababbin harin.

    Harin na zuwa ne ƙasa da wata guda, bayan harin da aka kai ofishin ƴansanda da ke Kalale a ranar 10 ga watan Satumba.

    Sai dai babu wanda ya mutu a cikin jami'an yansanda. Akwai tazarar kilomita 85 tsakanin Kalale da Segbana.

    Tsakanin 6 zuwa 7 ga watan Satumba, sojoji sun kashe mayaƙa shida da ake zargi da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda, a wani samamen da suka kai dajin Pendjari, wanda ya yi iyaka da Burkina Faso, da kuma wani daji da ya raba Nijar da Burkina faso.

    Tun shekarar 2021 ne jamhuriyyar Benin ke fama da hare-hare da ke janyo asarar rayuka.

    Maharan na kai munanan hare-hare tare da lalata bututan da ake tura mai daga jamhuriyyar Nijar zuwa Benin, wanda yan China suka gina.

  12. Yajin aikin PENGASSAN ya janyo tashin farashin gas a Najeriya

    ,,,

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, Bayo Ojulari ya ce yajin aikin da ƙungiyar manyan ma'aikan kamfanonin mai da na iskar gas, PENGASSAN suka yi ne ya dakatar da rarraba iskar gas na tsawon kwanaki, lamarin da ya janyo tashin farashinsa.

    Shugaban ya kuma zargi wasu daga cikin masu sayar da gas ɗin da yin amfani da yanayin ƙaracin isakar da aka fuskanta na wani ɗan lokaci wurin ƙara farashin.

    Mr. Ojulari wanda ya bayyana wa manema labarai haka a Legas ya bayyana cewa ƙarin farashin ƙirƙirarsa aka yi.....kuma a yayin da komai ya koma kamar a baya, zai ɗauki lokaci kafin rarraba iskar gas ɗin ya kankama.

    “A tunani na yanzu komai ya koma daidai, ya kamata farashin ya sauko kamar yadda yake a baya.” In ji shugaban na NNPCL.

  13. Isra'ila na tisa ƙeyar masu fafutukar flotilla da ta kama

    ,,,

    A ranar Litinin Isra'ila ta tusa ƙeyar mai fafutuka, Greta Thunberg da wasu masu fafutukar 170 ƙasashen waje.

    Waɗanda aka mayar ƴan ƙasashen Girka ne da Italiya da Faransa da Ireland da Sweden da Poland da Jamus da Bulgaria da Lithuania da Austria da Luxembourg da Finland da Denmark da Slovakia da Switzerland da Norway da Burtaniya da Serbia da kuma Amurka.

    Yayin da a ranar Lahadi ta mayar da wasu masu fafutuka 29 Spaniya, cikinsu har da ƴan Portugal da ƴan ƙasar Netherlands.

    A ranar Asabar ɗin da ta wuce kuma Isra'ilar ta mayar da wasu masu fafutuka 137 Turkiyya.

    A cikinsu har da Amurkawa da Italiyawa da ƴan Jordan da Burtaniya da Kuwait da Libya da Algeria da Mauritania da Malaysia da Bahrain da Morocco da Switzerland da Tunisia da Turkawa.

    Sai wasu masu fafatukar ƴan Italiya su huɗu da Isra'ilar ta mayar da su ƙasarsu a ranar Juma'ar da ta gabata.

    A makon jiya ne hukumomin Isra'ilar suka tsare ɗaruruwan masu fafutuka ciki har da mai rajin sauyin yanayi ƴar ƙasar Sweden, Greta Thunberg, bayan dakarun Isra'ilar sun kama jiragen ruwa da ke ɗauke da masu fafutukar da kayan agajin da zasu kai Gaza.

    Dakarun sun kama masu fafutuka 470 da gwamman jiragen ruwa na Global Sumud Flotilla (GSF) kafin su kai Gaza.

  14. Red Cross za ta taimaka wajen shigar da agaji Gaza

    ,,,

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa ta Red Cross (ICRC) ta ce ta shirya don zama mai shiga tsakani wurin musayar waɗanda ake garkuwa da su a Gaza da kuma fursunonin da Isra'ila ke tsare da su.

    "Tsagaita wuta mai ɗorewa na da matuƙar muhimmanci wurin ceton rayuka da kawo ƙarshen kashe-kashe da lalata wurare,” a cewar shugabar ICRC, Mirjana Spoljaric.

    "Kuma a shirye muke mu shigar da kayan agaji cikin Gaza tare da rarraba shi ga fararen hula da ke matuƙar buƙatar su." Inji ta.

    A watan Oktobar 2023 ƙungiyar ta taimaka wurin sakin waɗanda ake garkuwa da su 148 da 1,931 da ake tsare da su, da kuma gawawwaki.

  15. Tanzania ta yi gargaɗi kan kafafen sada zumunta bayan yin kira da a kifar da gwamnati

    ,,,

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an ƴansanda a ƙasar Tanzania sun yi gargaɗi kan amfani da kafafen sada zumunta wurin yaɗa bayanan da ba na gaskiya ba, bayan wani faifai bidiyon da ya karaɗe shafukan da ya nuna wani da ake zargin soji ne yana sukar gwamnatin ƙasar.

    Hakan na zuwa ne makonni uku gabannin babban zaben ƙasar.

    Mutumin wanda ya bayyana kansa a matsayin "kyaftin Tesha" daga rundunar sojin ruwan ƙasar, ya zargi gwamnati da cin hanci da rashawa, take haƙƙin bil'adama da sanya siyasa a cikin al'amuran soji.

    Sai dai rundunar sojin ba ta bayar da amsa ga tambayoyin da BBC ta yi mata ba kan mutumin ko shi wanene, kuma BBC kawo lokacin haɗa wannan labarin ba ta kai ga sanin ko soja ne da ke aiki a yanzu ba.

    Mutumin ya buƙaci hafsan sojin ƙasar, Jacob Mkunda da ya ɗauki mataki, kuma ya tabbatar ya haɗa kan ƙasar tare da kare ƴancin mutanenta.

  16. Najeriya na sa ran haƙo gangan ɗanyen mai miliyan1.8 a kullum

    ,,,,

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana kyakkyawan fatan cewa ƙasar zata dinga haƙo gangan ɗanyen mai miliyan1.8 kafin ƙarshen shekarar 2025.

    Kafar watsa labarai ta Channels TV ta ce shugaban kamfanin ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin da ya ke sanar da shugaba Bola Tinubu kan ayyukan kamfanin a jihar Legas.

    Mista Ojulari ya ce gyare-gyaren da suka yi a watannin Agusta da Satumba zasu taimaka wurin samar da ci gaba a wannan watan.

    Inda ya ƙara da cewa “Muna fatan kafin ƙarshen shekarar nan mu kai ga haƙo aƙalla gangan ɗanyen mai miliyan ɗaya da dubu 800 a kullum. ”

    A halin yanzu dai ƙasar na haƙo ganga miliyan 1.71 a kullum.

    Kuma ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da ke gaba-gaba wurin samar da ɗanyen mai a ƙungiyar OPEC a duniya.

  17. Firaiministan Faransa Sébastien Lecornu ya yi murabus

    ,,,

    Firaiministan Faransa, Sébastien Lecornu ya ajiye muƙaminsa , ƙasa da kwana ɗaya da ƙaddamar da ƴanmajalisar zartarwarsa.

    "Ba a cika sharuɗɗan da suka dace ba da za su bani ikon ci gaba da zama firaiminisa," a cewar Lecornu a ranar Litinin da safe, inda ya soki rashin yardar jam'iyyun siyasa wajen cimma daidaito.

    Fadar Elysée ce ta bayar da sanarwar murabus ɗin bayan Lecornu ya gana ta tsawon sa'a guda da shugaba, Emmanuel Macron a ranar Litinin.

    Hakan na zuwa ne bayan kwana 26 da naɗa, Lecornu, a matsayin firaiminista, sakamakon rugujewar gwamnatin, François Bayrou da ta shuɗe.

    Baki ɗaya jam'iyyun siyasan da ke majalisar dokokin ƙasar sun yi kakkausar suka ga majalisar ta Lecornu, wadda bata da wani sauyi sosai daga na wanda ya gada Bayrou, inda suka yi barazanar kada ƙuri'ar rashin amincewa da ita.

  18. ICC zata yanke hukunci kan shugaban ƴantawayen Sudan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Litinin za a yanke hukunci a birnin Hague, a shari'ar zargin aikata manyan laifuffukan yaƙi da ake yi wa shugaban ƴantawayen Sudan, Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman.

    Mutumin da aka fi sani da Ali Kushayb, shi ne mutum na farko da zai fuskanci shari'a a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa kan laifukan ta'addanci da aka aikata a yankin Darfur na kasar Sudan.

    Masu gabatar da kara na tuhumar tsohon shugaban na Janjaweed da kitsa kisan kai da fyade da azabtarwa da kuma bautar da jama'a sama da shekaru 20 da suka gabata.

    An gwabza faɗa a yankin Darfur lokacin da ƙabilun da ba na Larabawa ba suka yi zargin cewa ana nuna musu wariya, abun da ya sa suka ɗauki makamai tare da fara yaƙar Larabawan.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa mutane dubu 300 ne suka mutu, sannan sama da miliyan biyu suka rasa matsugunansu, sanadiyar yaƙin.

  19. Bincike ya samu Ministan kimiyya na Najeriya da 'mallakar takardun boge'

    ..

    Asalin hoton, Nnaji/X

    Wani bincike da jaridar Premium Times ta yi ya nuna cewa ana zargin ministan kimiyya da fasaha na Najeriya, Uche Nnaji, da yin takardun kammala karatu na boge, lamarin da ke ci-gaba da janyo cece-kuce a ƙasar.

    Binciken da jaridar ta Premium times ta wallafa ya ce an gano cewa ministan ya miƙa takardun bogin ga majalisar dattawan ƙasar domin tattance shi, bayan shugaban Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunansa cikin waɗanda yake so ya bai wa muƙamin minista a shekarar 2023.

    Jaridar ta yi ikirarin cewa takardun shaidar kammala karatun digiri da na bautar ƙasa na Mr Nnaji duka na boge ne.

    Inda ta ƙara da cewa masu suka sun ce ministan bai kammala karatun digirin ba, haka kuma takardar shaidar bautar ƙasar da ya miƙa wa ofishin sakataran gwamnatin tarayya da hukumar tattara bayanan sirri ta DSS da kuma majalisar dattawan na bogi ne.

    Kuma binciken da ta yi ya tabbatar mata da cewa takardun na boge ne.

    A cewar jaridar a ranar Lahadi ministan ya amince cewa jami'ar Nsukka da ke Najeriyar ba ta taɓa ba shi shaidar kammala karatu na digiri ba.

    Batun zargin takardun bogin na cikin manyan batutuwan da suka fi jan hankali a kafafen sada zumunta na Najeriya a ranar Litinin.

  20. Kotu ta hana Trump kai sojojin kwantar da tarzoma Portland

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani alƙali a Amurka ya hana gwamnatin Trump aika dakarun tarayya daga wasu jihohi zuwa birnin Portland da ke jihar Oregon, don wanzar da zaman lafiya.

    Alkalin ya ce matakin kawo sojoji daga jihohin California da Texas ya saɓawa hukuncin da ya yanke na baya, na hana amfani da jami’an tsaron ƙasar a jihar ta Oregon.

    Gwamnan California, Gavin Newsom wanda ya goyi bayan hukuncin, ya zargi shugaba Trump da amfani da sojoji a matsayin makamin siyasa.

    A halin da ake ciki, Gwamna JB Prit-zker na Illinoi, ya yi tur da shirin tura sojoji daga Texas zuwa jiharsa, abun da ya bayyana a matsayin "mamayar Trump".