Liverpool za ta iya asarar Fam miliyan 120 idan ta rasa gurbin Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin ɗin Liverpool Virgil van Dijk ya ce shi da abokan wasansa suna cikin jimami bayan da Wolves ta doke su da ci 2-1 a gasar Premier ranar Talata.
Rashin nasarar da ta yi a Molineux ya bar Liverpool a matsayi na biyar, a halin da ake ciki zai iya ba ta damara samun gurbi a gasar zakarun Turai ta baɗi.
Amma teburin gasar Premier ta bana a matse ya ke.
Tawagar ta Anfield ta tserewa Chelsea da maki uku ne kacal wadda za ta kara da Aston Villa da ke matsayi na huɗu a wasan da za su fafata a ranar Laraba a filin wasan Villa park.
"Idan ka na takawa Liverpool leda, kodayaushe kana iya samun kanka a wannan matsayi. Ya rage gare mu, tare da magoya bayanmu, mu yi yunƙurin samun sakamakon da muke buƙata don shiga gasar zakarun Turai." in ji Van Dijk
Masana harkar hada hadar kuɗi a fannin wasanni sun bayyan cewa rashin samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta kaka mai zuwa zai iya janyowa Liverpool asarar da ta kai fam miliyan 120.











